Aminiya:
2025-11-08@15:41:11 GMT

Yadda kwacen babur da waya ya maye gurbin garkuwa da mutane a Birnin Gwari

Published: 7th, August 2025 GMT

Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo.

A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu.

Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da rikicin da ya mayar da babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari daya daga cikin mafiya hatsari a Najeriya.

Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC

Daga shekara ta 2015, mazauna yankin sun sha fama da hare-hare da garkuwa da su, yayin da matafiya kuma ala tilas suka koma neman rakiyar sojoji kafin su iya wuce hanyar.

Yanzu dai yankin ya fara samun saukin matsalar, yayin da mazauna yankunan suka fara komawa gidajensu manoma kuma suka ci gaba da noma gonakinsu.

To sai dai da alama yanzu a maimakon garkuwa da mutanen, rahotanni na cewa a yanzu ’yan bindigar sun fara yawo a gonaki suna kwace babura, wayoyi, kudade da ma kayan aikin gona daga hannun manoman yankin.

Mazauna kauyen Kuyello da ma wasu kauyukan sun ce yanzu suna zaman dardar.

Wasu daga cikinsu sun kyale gonakin gaba daya, wasu kuma sun ce yanzu sukan bar wayoyinsu a gida saboda tsoron za a iya yi musu fashi.

“Yanzu ’yan bindiga sun daina garkuwa da mutane, amma sun koma yi mana kwace. Yanzu suna yawo a gari hankalinsu kwance ba sa tsoron kowa,“ in ji wani mazaunin garin na Kuyello.

Hakan dai ya sake jefa tsoro a kan ingancin zaman sulhun da aka ce an yi.

Mazauna yankin dai sun yi korafin cewa babu wani yunkuri da ake yi na dakile tubabbun ’yan bindigar daga kwacen da suke yi, lamarin da ya sa suka ce suna tsoron sake komawa gidan jiya.

Bayanai dai na cewa yanzu matafiya na bin hanyar ta Kaduna zuwa Birnin Gwari, wacce babbar mahada ce tsakanin kudanci da arewacin Najeriya, ba tare da wata barazana ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Birnin Gwari

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)

Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna tsoron wanda zai yi tunani a gaba, saboda duk wanda ya kawo wani ilimi sai ka ji an ce Zindiki ne, sai a so a halaka shi ma idan ba a yi wasa ba. Toh abin da ya dinga faruwa kenan har Allah Ya kawo falasfawa na Greeks Socrate, wasu sun ce Annabi ne, suka zo suka canza ilimi shi kan shi wannan Socrate din kashe shi aka yi da aka ce ko ya ce bai yarda da wannan ilimi ba, ko ya sha dafi shi kuma ya ce Allah ba zai ba shi ilmi ba, don haka gwara ya sha dafi ya mutu ya yarda ya sha, ga shi su wanda suka kashe shi ba sunansu shi kuwa har yau sunansa a duniyar ilimi ba zai bace ba. Toh Allah kuma Ya kawo juyin juya hali daga karni na 1800 har ya zuwa 1900 ilimin ya soma yalwata da aka fara rubuta shi, wasu na cewa ba mahaukaci sai wanda ya ba da aron littafi, ba wanda ya fi shi hauka sai wanda ya dawo da shi, wannan a lokacin da ake rubuta littafi da hannu kenan amma yanzu ya kare, an ce Shehu ya zo gidan daya daga cikin shehunnanmu yana duba library sai ya ga wani littafi sai ya ce ka ga wannan littafi na neme shi ban samu ba, ba ni aro sai ya ce Shehu na ba ka aro dauki, sai Shehu ya ce masu hikima sun ce babu mahaukaci sai wanda ya ba da aron littafi, ba wanda ya fi hauka sai wanda ya dawo da littafi, ya ce ni dai ba zan zama mahaukaci ba, sai Shehu ya yi masa wasa.

To da aka soma rubutun, China kamar su suka soma, to da buga littafi ilimi ya soma ya]uwa zuwa ga jama’a, ilimi ya fito daga dakin bauta, ya fito daga masarautar sarakuna ya shiga gidan kowa, a da kuwa yana gidan sarakuna ne kawai, ilimi ya soma yaduwa har Allah ya kawo Rediy,o tana daga cikin abin da ya yada ilimi, ta yi hobbasa wajen wayar da kan komai, dan haka a kula da rediyo yana da matukar kyau saboda galibin mutane rediyon nan ita ce hanyar daukar maganarsu, Allah ya saka wa Shehu Ibrahim Inyass (RA) da alkhairi, ya sha wahala wajen sa karatun Kurani a ciki, har Allah ya kawo talabijin, har “cable” din nan ta zo, yanzu fa za ka iya ganin duniya a cikin abu, karshen wayewa, karshen ci gaba a yanzu kuma wayar salula, wadannan wayoyi da suke hannunmu sun sa a yanzu babu jahili sai dai dakiki wanda ya ki sani da gangan, amma wayar nan babbar farfesa ce ta kowane karni, idan fannin jinya ne za ta fada ma har abin da hankalinka ba zai taba kawowa ba, haka a fannin alheri, idan fannin tarihi ne za ta kai ka har inda kudinka ba zai iya kai ka ba. Alhamdu Lillah, mun gode Allah.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Dausayin Musulunci Manzon Allah (SAW) Ne Ya Kafa Tushen Wayewar Kai A Duniya October 17, 2025 Dausayin Musulunci Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taɓa Yi (2) October 10, 2025 Dausayin Musulunci Annabi (SAW) Shi Ne Mai Girman Duk Wani Mai Girma Da Allah Ya Taba Yi October 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal
  • NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu
  • Matsalar Tsaro: Yadda Dabarun Uba Sani Suka Mayar Da Tsoro Zuwa Kyakkyawar Fata A Jihar Kaduna
  • Yadda Duniya Ta Fara Wayewa Tun Daga Zamanin Annabi Nuhu (AS) Har Manzon Allah (SAW) Ya Zo Ya Cika Komai (2)
  • Sama da gidaje 8,000 za su samu wutar lantarki daga hasken rana a Gombe
  • Genoa ta naɗa Daniele De Rossi sabon kociya
  • Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
  • Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos
  • Likitoci sun wayar da kan mata kan cutar Sankara a Gombe