Iraki: An bankado wani yunkurin kai wa masu ziyarar Arbaeen hari
Published: 11th, August 2025 GMT
Jami’an tsaron kasar Iraki sun sanar da gano wata kungiyar ‘yan ta’adda da ta yi niyyar kai wa masu ziyarar Arbaeen hare-hare, wanda aka shirya gudanarwa a kwanaki masu zuwa.
Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa, “tsarin da ‘yan ta’addan ke da shi sun hada da dasa ababen fashewa a kan hanyoyin da masu tattaki ke bi a yankin kudancin kasar da kuma saka guba a cikin kayan abinci da ake ba wa masu tattaki.
Har ila yau, bincike ya nuna cewa kungiyar ta’addanci ta ISIS ta yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen daukar wadannan mambobi nata da aka wanke wa kwakwalwa domin aiwatar da wadannan ayyuka.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, kungiyar na yin hakan ne ta hanyar yin amfani littafai da aka rubuta musamman domin tunzura masu irin wannan Akida ta kafirta musulmi da zubar da jinni, tare da yin amfani da wasu malamai masu irin waannan Akida domin gurbata tunanin matasa musulmi, da kuma saka su hanyar ta’addanci da sunan addini ko jihadi.
A ranar alhamis din da ta gabata ma karamar hukumar Karbala ta sanar da kame wasu mutane 22 da suke Shirin kai hare-haren ta’addancin da suka tsara a lokacin tarukan ziyarar Arbaeen na wannan shekara.
Ko a shekarun baya an yi ta samun irin wadannan matsaloli na ta’addanci daga kungiyoyi masu dauke da akidar takfir da suke kafirta al’ummar musulmi tare da halasta jininsu, inda suke Kallon dukkanin musulmi da ba su a cikinsu a matsayin ‘yan bidi’a mushrikai ko kafirai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Chadi: An Daure Wani Dan Adawa Shekaru 20 A Gidan Kaso Da tara August 10, 2025 Dangantaka Tsakanin Iran da Saudiya Yana Taimakawa Zaman Lafiya A yankin August 10, 2025 Iran Zata Hana Amurka Samar da Hanya A yankin Caucasus Ko Rasha Bata taimaka ba August 10, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare A Kan Garuruwa Da Dama A Yankin Quneitra Na Kasar Siriya August 10, 2025 An Zabi Alkalan Wasa Biyu Daga Kasar Iran Don Alkalanci A gasar Kwallon Kafa ta Mata August 10, 2025 Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza August 10, 2025 Iran Ta Cimma Matsayi A Yaki Kwanaki 12 August 10, 2025 Jami’an Tsaron Iran Sun Murkushe ‘Yan Ta’adda Kan Ofishin ‘Yan Sanda A Kudu Maso Gabashin Kasar August 10, 2025 Jefa Agajin Abinci Ta Sama A Zirin Gaza Ya Janyo Shahadan Falasdinawa 23 Tare Da Jikkata Wasu 124 August 10, 2025 Tehran Times: Mai Yiwuwa Iran da Amurka su koma Tattaunawa August 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take
Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza.
Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi.
Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin.
An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen kasar wadanda suka hada da Tabriz, Ahvaz, Shiraz, Bandar Abbas, Isfahan, da Gorgan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta October 11, 2025 Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza October 11, 2025 Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran October 11, 2025 Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci