Aminiya:
2025-10-13@17:52:55 GMT

Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya

Published: 11th, August 2025 GMT

A safiyar wannan Litinin ɗin ce aka wayi gari da wani mummunan hatsarin tankoki biyu na dakon iskar gas a Zariya, inda direba ɗaya kacal ya tsira da rai, yayin da wasu da dama suka ƙone ƙurmus.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe tara na safe, a kusa da shatale-talen Jirgin Sama Mota da ke titin Kaduna zuwa Zariya, daura da sabuwar Kasuwar Ɗan Magaji.

An kama mutumin da ake zargi da kashe jami’in sibil difens a Jigawa Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’ani

Rahotanni sun nuna cewa motocin biyu sun gogi juna ne yayin da ɗaya ke ƙoƙarin wuce ɗaya, lamarin da ya haddasa kamawar wuta nan take.

An ji wata ƙara mai ƙarfi da ta tashi a lokacin haɗarin, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna yankin.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, mutane da dama sun yi ta tserewa daga gidajensu domin guje wa abin da ka iya zuwa ya komo, yayin da kuma hayaƙi mai yawa ya mamaye hanyar da ya daƙile zirga-zirgar ababen hawa.

Jami’an tsaro da na kashe gobara sun kai ɗauki wurin domin ceto mutane, amma ƙarfin wutar ya hana su samun damar kaiwa kan motocin.

Shugaban Sashen Kula da Hatsari na Ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne sakamakon goguwar motocin dakon gas ɗin biyu, saɓanin raɗe-raɗin cewa tsautsayin ya rutsa da wasu ƙananan motoci ƙirar Golf.

“Direban ɗaya daga cikin motocin ya tsira, kuma mun kai shi asibiti domin samun kulawa. Shi kaɗai ne zai iya ba da cikakken bayani idan ya samu sauƙi,” inji Falgore.

Shugaban Ƙungiyar Direbobi a Zariya, Malam Sa’idu Haruna, ya bayyana cewa ana yawan samun hatsari a wurin saboda yanayin kwana da titin yake da shi.

“Kusan duk wata biyu zuwa uku sai an sami hatsari a nan. Muna kira ga hukumomi su kawo ɗauki,” inji shi.

Haka kuma, shugaban bayar da agajin gaggawa na ƙaramar hukumar Sabon Gari, Abdul Malik Aminu, tare da na Zariya, Abdul’muminu Adamu, sun tabbatar da cewa ba a gama tantance adadin mutanen da suka rasu ba saboda akwai fasinjoji a motocin da ba a gano su ba tukuna.

DPO na ofishin Ɗan Magaji, CSP Auwalu A. Sani, ya ce aikinsu shi ne sanya ido don kare rayukan masu wucewa, amma bai bayar da ƙarin bayani kan hatsarin ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Hatsari iskar gas Motar Dako Zariya

এছাড়াও পড়ুন:

Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Trump Da Al-Sisi Za Su Jagoranci Taron Zaman Lafiya Dawwamammiya Ta Gaza A Masar October 12, 2025 Manyan Labarai Yaƙi Da Boko Haram: An Kashe Sojoji 2,700 A Shekara 12 – Janar Irabor October 12, 2025 Labarai Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa October 12, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 9, sun kwato kudin fansa a Borno
  • Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Byyana
  • An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu
  • Ranar Malamai Ta Duniya: Rashin Kulawa Ke Sa Malamai Barin Aiki
  • Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya