GORON JUMA’A 8-8-2025
Published: 8th, August 2025 GMT
Saƙo Daga Hassana Abubakar Jihar Bauchi:
Ina gaida iyayena, sai ƙawayena Anisa Aliyu, Farida Aliyu, Sadiya Garba da sauransu. Sai ‘yan’uwa na gida Maryam Abubakar, Khadija Abubakar, Zainab Abubar, Habib Abubakar, Zahraddeen Abubakar, Sani Abubakar, Anty Karimatu, Kawu Haruna, Yagana, da fatan sun yi juma’a lafiya.
Saƙo daga Maryam Shitu Jihar Kano:
Ina miƙa saƙon gaisuwata zuwa ga ‘Yan’uwana Haj. Marka, da Salamatu Rilwan, da Khajija da Hafsat. Ina miƙa saƙon gaisuwata zuwa ga Ƙawayena Hadiza Jibril, Haj. Sadiya, Abida Ahmad, Zuhriyya Aminu, Suwaiba Sauban, Maman Walid da sauran ƙawayena duk a garin Kano.
Saƙo daga Ahmad Halliru Jihar Katsina:
Ina gaida masoyiyata, abar ƙaunata, muradin zuciyata Leemat Beauty, saƙon na musamman ne zuwa gareta abar alfahari na. Ina gaida abokaina Sulaiman me inkiya, Fauwaz na Azima, Faisal dan boi, Masoyi me jama’a, Safyanu J.k, dan Adamawa, Bello yaron kirki, da duk jama’ar AZ Group.
Maryam Aminu Daga Jihar Katsina:
Saƙon na musamman ne zuwa gare ku abun alfaharina mahaifana Haj Salma Yelwa da Alh. Aminu Yelwa. Ina gaida ƙawayena Fatima Sulaiman Dikko, Hadiza Muhd, da fatan sun yi juma’a lafiya
Saƙo daga Yahanasu Jibirin Minjibir Jihar Kano:
Ina gaida ƙawata Safiyya Kamal, Yayana Ishak, ƙanwata Khadijah, Sadiyya, Khairat, Tally, Nusaiba, Hafasat Ameer, Amina Habib, Zainab Abdullahi Waziri, Jamila Khalil, Maryam Khalil, Fatima Khalil, da fatan sun yi juma’a Lafiyya.
Saƙo daga Abubakar Saddiƙ Bebeji Jihar Kano:
Ina gaida Mamana da Babana, abokan karatuna Umar Faruƙ Bichi, Sani Muhammad, Mustapha Lamin, Isoufou Abdoulaye, Chamsu Mousa, Fatima Garba da dai sauransu, da fatan sun yi juma’a lafiya.
Saƙo daga Chef Maryam daga Jihar Kano Nassarawa LGA:
Ina gaida mahaifiyata da mahaifina, sai ƙawayena Amira Malumfashi, Dr. Intisar Hashim, Ambasador Maryam Alhasan Imam, Haj. Hauwa Balarabe, Rashida Danlami, Zinatu Kabir, Aisha Khalifa, Surayya Hisham, Jamilah Ahmad Maishinkafa, Nr. Zahra’u Babangida, da dai sauransu da fatan
sun yi juma’a lafiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jihar Zamfara: ‘Yan Sanda 390 Sun Sami Karin Girma
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya kawata jami’ai 390 da aka daga matsayinsu zuwa sabon mukami a rundunar.
An gudanar da bikin kawata jami’an ne a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Gusau, babban birnin jihar.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sanda, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya taya sabbin jami’an murna tare da bukatar su tabbatar da cancantarsu da mukaman da aka ba su, ta hanyar rubanya kishin aiki, ladabi da kwarewa a ayyukansu.
Ya jaddada bukatar jami’an da su dage wajen yin aiki da jajircewa da kuma bayar da ingantaccen tsaro ga al’ummar Jihar Zamfara da Najeriya gaba ɗaya.
Daga cikin waɗanda suka sami karin girman akwai CSP Sani Kabiru da CSP Usman M. Nassarawa, waɗanda aka daga zuwa mukamin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda (ACP).
“An daga jami’ai 30 daga matsayin Sifeto zuwa Mataimakin Sufiritandan ‘Yan Sanda (ASP II).” In ji Kwamishinan.
Ya ƙara da cewa, an daga jami’ai 242 daga Sajan zuwa Sufeta, sannan kuma an daga jami’ai 116 daga matsayin Kofur zuwa Sajan.
Da yake magana a madadin sabbin jami’an da aka daga matsayinsu, ACP Usman M. Nassarawa ya nuna godiya sosai ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda bisa amincewar da suka nuna a gare su.
Ya yi alkawarin cewa sabbin jami’an za su ci gaba da kiyaye manyan dabi’un aikin ‘yan sanda na Najeriya – wato gaskiya, jajircewa, ƙwarewa da amincewar jama’a – a hidimarsu ga ƙasa.
Daga Aminu Dalhatu