“An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi

 

Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna kan hanyar zuwa kauyen Yankuzo, inda rahotanni suka ce an kai ‘yan ta’addan da suka jikkata domin yi musu magani.

 

A cewar majiyoyi da bayanan sirri daga Kauyen, an kashe ‘yan ta’adda fiye da 30 a yayin samamen.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Al’ummar Zamfara: ’Yan bindiga sun karɓi N56m domin izinin yin noma

Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana.

Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya biya Naira dubu 800 kafin a bar mazauna yankin su yi noma.

NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti

“Kowanne ƙauye kuma zai sake biyan Naira dubu 800, don bai wa mazauna yankin damar girbe amfanin gonakinsu, wannan ita ce yarjejeniya da muka cimma da shugaban ’yan bindiga da ke kula da wannan yanki, Ɗan Sadiya.”

“Ina magana ne game da gundumata kawai, ban san abin da mazauna wasu gundumomi suka biya wa ’yan bindigar ba a wannan shekara. Amma wani abu da nake da tabbacin shi ne mazauna yankin su biya kafin a barsu su yi noma.

“Ba mu da wani zaɓi illa mu bi umarninsa, in ba haka ba, ’yan bindiga ba za su barmu mu yi noman gonakinmu ba, a ƙalla idan muka yi noma, za mu iya samun wani abu ga iyalanmu,” in ji shi.

Sai dai Yarima ya koka da cewa, duk da biyan kuɗin noma, har yanzu ’yan bindiga sun mamaye ƙauyukansu suna sace dabbobi tare da kwashe kayan abinci.

Ya yi nadama kan yadda mazauna unguwannin da abin ya shafa suke yin amfani da duk abin da suke da shi a ƙoƙarin samun zaman lafiya da ’yan bindigar.

“Muna so mu zauna lafiya da ’yan bindigar, amma gaskiya sun karɓe mana komai, sun yi awon gaba da dabbobinmu sun kwashe kuɗinmu, amfanin noma  da sauran kayayyaki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Zamfara: ’Yan bindiga sun karɓi N56m domin izinin yin noma
  • An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara
  • ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno
  • Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi
  • Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama
  • Ministan tsaron Ghana da wasu sun rasu a hatsarin jirgin sama
  • Ruftawar Gini Ya Kashe Uwa Da ‘Ya’yanta Biyar A Katsina
  • Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32
  • ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu