Kungiyoyin Kwadago Sun Tsunduma Yajin Aiki A Taraba
Published: 11th, August 2025 GMT
Kungiyar Kwadago da ta ‘yan kasuwa ta Nijeriya (NLC da TUC) reshen jihar Taraba sun bayyana shirin fara yajin aiki tun daga karfe 12 na daren Litinin 11 ga watan Agusta, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan sakamakon taron majalisar zartarwa ta jihar da kungiyoyin biyu suka yi a ranar Lahadi a Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Soja ya soka wa ɗan sanda wuƙa har Lahira a Taraba
Wani kurtun soja ya soka wani ɗan sanda mai mukamin Constable, Aaron John da wuƙa har lahira a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba.
Kakakin ’yan sanda na jihar, James Lashen, ya ce wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin, a unguwar Mayo-Goyi, da ke gefen birnin Jalingo.
Lashen ya bayyana cewa marigayi John ya samu kiran gaggawa daga wasu mazauna yankin dangane da sabani da suka samu da sojan.
A yayin da yake kokarin warware rikicin, sai sojan mai suna Dauda Dedan, ya soka masa wuƙa.
Ya ce, “Mun samu rahoton lamarin daga hedikwatar Brigade ta 6 ta Rundunar Sojin Najeriya, da tabbacin cewa za a kamo sojan da ya tsere domin fuskantar hukunci,” in ji Lashen.
Ya ƙara da cewa rundunar soji ta fara bincike kan lamarin, tare da tabbatar wa ’yan sanda cewa za su haɗa kai wajen kamo wanda ake zargi.
“Sojoji da ’yan sanda na aiki tare. Mun kai ziyara har gidan sojan, kuma za mu tabbatar an kama shi domin ya fuskanci hukunci daidai da abin da ya aikata,” in ji Lashen.
Ya jaddada cewa dangantaka tsakanin sojoji da ’yan sanda a jihar Taraba tana da kyau kuma babu wata matsala a tsakaninsu.