Tel Aviv: Dubban yahudawa sun yi zanga-zangar adawa da yakin Gaza
Published: 10th, August 2025 GMT
Dubban mazauna birnin Tel Aviv ne suka taru a tsakiyar birnin a daren jiya Asabar, domin neman kawo karshen yakin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da shirin kara kai hare-hare da kuma mamaye birnin Gaza.
Masu zanga-zangar dai na dauke da allula da kuma hotunan wadanda ake tsare da su a Gaza, suna masu kira ga hukumomi da su ba da fifikon sakin su kan fadada ayyukan soji.
An kuma bayyana cewa hatta a cikin manyan jami’an soji na Isra’ila, babban hafsan hafsan hafsoshin sojin Isra’ila Eyal Zamir ya yi yunkurin shawo kan majalisar ministoci kan cewa mamaye Gaza ba shi ne zabin da ya dace ba, da kuma tattauna babbar illar da hakan zai haifar ga tasirin soji da tattalin arziki a irin wannan hali, kamar dai yadda jaridar Isra’ila Hayom ta ruwaito.
Zamir ya kuma nuna damuwarsa kan yadda mamayar Gaza za ta shafi rayuwar fursunonin da ake tsare da su da kuma makomarsu.
Mai Magana da yawun sojin Isra’ila ya ce, Zamir na bayar da shawarar a cimma matsaya, inda ya jaddada bukatar yin sassauci da kuma kara zage damtse wajen ganin an cimma yarjejeniya, ya kara da cewa rundunar sojin kasar ta nuna a shirye ta ke ta amince da duk wasu sharudda da suka hada da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da za ta iya kawo karshen yakin.
A halin da ake ciki, ofishin Netanyahu ya sanar da cewa “Isra’ila” za ta karbe ikon birnin Gaza, ya kara da cewa “mafi rinjayen ministocin majalisar zartaswa sun yi imanin cewa shirin da aka gabatar wa majalisar ministocin ba zai cimma nasarar fatattakar Hamas ba ko kuma mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su ba.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Welayati: Makircin Amurka da Isra’ila na kwance damarar Hizbullah ba zai yi nasara ba August 10, 2025 Birtaniya: ‘Yan sanda sun kama akalla mutane 365 a zanga-zangar goyon bayan Falasdinu August 10, 2025 Venezuela: An dakile yunkurin kai wasu munanan hare-hare a cikin kasar August 10, 2025 Pezeshkiyan Ya Yabawa Yan Jarida A Ayyukansu A Yakin Kwanaki 12 August 9, 2025 Yansanda A Burtaniya Ta kama Mutane Fiye Da 200 Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 9, 2025 Iran Ta Yi Maraba Da Sulhuntawa Tsakanin Armenia Da Azerbaijan August 9, 2025 Falasdinawa 11 Ne Suka Rasa Rayukansu Saboda Yunwa A Gaza August 9, 2025 Shugaban Kwango, Tshisekedi Ya Shigar Yan Tawaye A Gwamnatinsa August 9, 2025 Iran: ‘Yan Sahayoniyya Na Shirin Share Falasdinawa Daga Kan Doron Kasa August 9, 2025 Iran: Amurka Ta Sha Kaye Daga ‘Yan Gwagwarmayar Kasar Yemen August 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mabiya Mazhabar Shi’a Sun Yi Zanga-Zanga A Kano Kan Barazanar Trump Ga Nijeriya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Bisa Rakiyar Jami’an Tsaro Na Ke Ganawa Da Ƴan Bindiga – Sheikh Gumi November 8, 2025
Manyan Labarai Barau Zai Yi Ƙarar Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Gawuna/Garo Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10 November 8, 2025
Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025