Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna
Published: 12th, August 2025 GMT
Yanzu haka mutane huɗu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya, bayan sun jikkata a wani mummunan haɗarin da ya haɗa da tankoki biyu a ƙauyen Kake, yankin Dan Magaji, kan hanyar Zariya–Kaduna. Haɗarin ya jawo mummunar gobara bayan haɗuwar motocin.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tankokin na ɗauke da iskar gas (LNG), yayin da ɗayar kuma babu komai a cikinsa.
Kwamandan hukumar kashe gobara ta ƙasa a Zariya, Aminu Ahmadu Kiyawa, ya ce jami’ansa sun isa wurin cikin gaggawa bayan samun kiran wayar gaggawa. Ya tabbatar da cewa mutum uku sun jikkata sakamakon fashewar gas, yayin da aka ceto mutum guda daga ɗaya tankar, kuma duka huɗun an garzaya da su zuwa asibitin ABU domin samun kulawar likitoci.
Kiyawa ya ƙaryata jita-jitar da ake cewa haɗarin ya rutsa da ƙananan motoci irin su Gulf, yana mai cewa “Lokacin da muka isa wurin, tankoki biyu ne kawai muka gani. Babu wata ƙaramar mota da ta shiga hatsarin.” Shaidun gani da ido ma sun tabbatar da cewa tankoki biyu kacal ne suka shiga haɗarin, kuma babu wanda ya rasu a lokacin da ake haɗa wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Nijeriya ASUU a ranar Lahadi ta sanar da shiga yajin aiki na makonni biyu, wanda zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, a duka jami’o’in gwamnati na ƙasar.
Shugaban ƙungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya sanar da hakan a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, a ranar Lahadi.
Asuu ta ce yajin aikin na gargaɗi ne bayan cikar wa’adin da suka bai wa gwamnatin Najeriya a watan Satumban da ya gabata.
“Yajin aikin gargadin zai kasance cikakke kuma gaba ɗaya, kamar yadda aka amince a taron NEC na ƙarshe,” kamar yadda Piwuna ya bayyana.
RN