Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa
Published: 7th, August 2025 GMT
Falasdinawa masu yawa ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin ‘yan sahayoniyya suka kai kan tantuna da gidaje da ‘yan gudun hijira a Gaza
Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu masu yawa da sanyin safiyar yau Alhamis a wasu munanan hare-hare da jiragen yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, inda suka kai harin kan gidajen fararen hula da kuma tantunan ‘yan gudun hijira.
Jiragen saman sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wani tanti na ‘yan gudun hijira a yankin Tal, kudu maso yammacin birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa akalla biyar tare da raunata wasu.
A yammacin sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat kuwa, jirage masu saukar ungulun Isra’ila sun kaddamar da wani samame a wani gida da ke cikin Hasumiyar Al-Salhi da ke kusa da zagayen Abu Sarar, inda suka yi sanadin shahadar Anas Abdul Rahman al-Jamal da matarsa da kuma ‘ya’yayensa mata guda biyu, kuma ya yi sanadin shahadan fararen hula.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Human Rights Watch Ta Ce: Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Rusa Makarantu Fiye Da 500 A Gaza August 7, 2025 Amurka Ta Kwace Dalar Amurka Miliyon $584 Na Jami’ar California Saboda Gaza August 7, 2025 Mutanen Kasar Lebanon Suna Tsoron HKI Zata Shiga Kasar Daga Kasar Siriya August 7, 2025 Amurka ta Fara Janye Wasu Sojojinta Daga Wurare 3 A Kasashen Iraki Da Siriya August 7, 2025 Kasar Masar Ta Zama Mai Shiga Tsakanin Iran Da IAEA Da Kuma Amurka August 7, 2025 Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba August 7, 2025 Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu August 7, 2025 Jamus: Shahararrun mutane da ‘yan jarida sun bukaci a daina baiwa Israila makamai August 7, 2025 Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya August 7, 2025 Pezeshkian Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Yaki A Gaza August 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan gudun hijira
এছাড়াও পড়ুন:
Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza
A Italiya dubun dubatan mutane ne suka fito kan tituna domin yin Allah wadai da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi a Gaza.
Wannan gangami ya zo ne a ranar da wasu kasashe da dama ke shirin amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a Majalisar Dinkin Duniya, bayan Birtaniya, Australia da Canada a ranar Lahadi.
Duk da cewa Italiya ba ta da niyyar daukar irin wannan matakin a yanzu, A birnin Rome, fiye da mutane 20,000, ne suka taru dauke da tutocin Falasdinu domin nuna goyan bayansu.
An gudanar da zanga-zangar a wasu garuruwa da dama a fadin kasar, ciki har da Milan inda mutane 50,000 suka shiga zanga zangar in ji masu wadanda suka shirya ta.
Saidai Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, an artabu tsakanin masu zanga-zangar da ‘yan sandan Italiya a tsakiyar birnin Milan.
Sauran zanga-zangar sun gudana a Turin (arewa), Florence (tsakiya), Naples, Bari, da Palermo (kudu).
Baya ga haka bayanai sun ce ‘yan darikar Katolika sun shirya taron nuna goyon baya da addu’a a babban birnin Italiya a yammacin yau Litinin.
A cewar wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a, kasha 63.8% na ‘yan Italiya suna ganin halin da ake ciki na jin kai a Gaza ya kasance “mai tsanani,” kuma kasha 40.6% na son amincewa da kasar Falasdinu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya September 22, 2025 Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya September 22, 2025 Dakarun IRGC: Iran Za Ta Tarwatsa Makiya Tare Da Mayar Da Martani Kan Duk Wani Zalunci September 22, 2025 Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi September 22, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula 5 A Kudancin Kasar Lebanon September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci