Mutanen Kasar Lebanon Suna Tsoron HKI Zata Shiga Kasar Daga Kasar Siriya
Published: 7th, August 2025 GMT
Jami’an tsaro a kasar Lebanon sun bayyana damuwarsu da yiyuwar sojojin HKI su farwa kasar da yaki da nufin kwace kasar da kuma sunan yaki da kungiyar Hizbullah.
Jaridar da nation ta kasar amurka ta bayyana cewa, HKI ta jibje sojojin masu yawa da kuma tankunan yaki a kusa da Jabal sheikh da suka mamaye, don mai yuwa ta fadawa kasar Lebanon ta kuma mamaye gabaci da areawacin kasar kafi ta fuskan kungiyar Hiszullah wacce tafi bada karfinta a kudancin kasar.
Wasu majiyoyin tsaro guda 2 a kasar ta Lebanon wadanda basa son a bayyana sunayen na fadar cewa sojojin HKI a kan iyakar kasar Lebanon da Siriya sun bayyana cewa a hankali a hankali sojojin HKI suna matsowa kusa da kan iyakar kasar da kasar Siriya.
Tun bayan faduwar gwamnatin Bashhar al-Asad jiragen yakin HKI sun ci gaba da yin luguden wuta a yankunan Bika na gabacin kasar Lebanon, wanda ya nuna irin shirin da suke na sake mamayar kasar ta Lebanon.
Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a kan garin Baalabak da yankin bika da sunan wargaza sansanonin cilla makaman Hizbullah.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka ta Fara Janye Wasu Sojojinta Daga Wurare 3 A Kasashen Iraki Da Siriya August 7, 2025 Kasar Masar Tana Ta Zama Mai Shiga Tsakanin Iran Da IAEA Da Kuma Amurka August 7, 2025 Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba August 7, 2025 Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu August 7, 2025 Jamus: Shahararrun mutane da ‘yan jarida sun bukaci a daina baiwa Israila makamai August 7, 2025 Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya August 7, 2025 Pezeshkian Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Yaki A Gaza August 6, 2025 Araqchi Ya Taya Larijani Murnar Zama Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran August 6, 2025 Japan: An Fara Juyayin Cikar Shekaru 80 Da Harin Amurka Na Makamin Nukiliya A Hiroshima August 6, 2025 Sudan: Dakarun RSF Sun Kashe Fararen Hula 14 Tare Da Jikkata Wasu Na Daban August 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Ukraine: Fiye Da ‘Yan Afirka 1000 Ne Suke Taya Rasha Yaki Da Kasar Ukiraniya
Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ne ya bayyana cewa da akwai ‘yan asalin kasashen Afirka 1,400 da suke cikin rundunonin Rasha suna tayata yaki.
Ministan harkokin wajen kasar ta Ukraine, Adriy Sabiha ya ce; Moscow tana jan hankalin ‘yan Afirka akan su rattaba hannu akan wata yarjejniyar aiki, wacce take daidai da yankewa kansu hukuncin kisa.
Har ila yau, ministan harkokin wajen kasar na Ukraine, ya rubuta a shafinsa na X cewa; ‘yan kasashen wajen da ake dauka a cikin sojojin Rasha, ana aike su zuwa inda za a yi saurin kashe su.”
Jami’an gwamnatin kasar ta Ukraine sun sha yin kira ga gwamnatocin kasashen Afirka da su hana ‘yan kasarsu yi wa Rasha aikin soja da hakan yake da hatsari.
A gefe daya, kasar Afirka Ta Kudu ta bayyana cewa za ta gudanar da bincike akan yadda aka yi ‘yan kasarta 17 su ka shiga yakin, bayan da su ka aike da sako suna neman a taimaka musu su koma gida.
Shugaban kasar ta Afirka Ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce, ‘yan kasar da su ka tafi yakin matasa ne da shekarunsu suke a tsakanin 20 zuwa 39,bayan da aka shafa musu zuma a baki na samun aiki mai tsoka.
A watan da ya gabata ma dai kasar Kenya ta sanar da cewa da akwai ‘yan kasashenta da ake tsare da su a cikin sansanonin sojan Rasha,bayan da su ka shiga cikin rikicin ba tare da saninsu ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jirgin Kasan Dakon Kaya Na Farko Daga Rasha Ya Iso Kasar Iran A Yau Asabar November 8, 2025 Lebanon: Mutane 2 Sun Jikkata Sanadiyyar Harin “Isra’ila” A Garin Bint-Jubail November 8, 2025 Araqchi: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin November 8, 2025 Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta November 8, 2025 Iran Da Mexico Sun Karyata Zarge-Zargen Da Aka Yi Kan Jamhuriyar Musulunci Ta Iran November 8, 2025 Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila November 8, 2025 Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta November 8, 2025 Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe November 7, 2025 Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma November 7, 2025 Unicef: Kananan Yara 47 ” Isra’ila” Ta Kashe A Yammacin Kogin Jordan November 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci