Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) murna bisa ci gaba da riƙe matsayin Maturity Level 3 (ML3) na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) wajen kula da magunguna da rigakafi.

Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Bayani da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa, an gudanar da binciken sake tantance matsayin WHO daga 28 zuwa 30 ga Mayu, 2025, inda aka kimanta NAFDAC bisa ka’idojin ƙasa da ƙasa.

Hukumar ta fara samun wannan matsayi na ML3 ne a 2022, inda ta zama hukumar farko a Afrika mai kula da ƙasashen da ba sa samar da magunguna da ta cimma wannan nasara.

Wannan sabon tantancewa ya biyo bayan wani binciken ne  a watan Nuwamban 2024, tare da gudanar da tarukan duba Shirin Cigaban Cibiyoyi(IDP) guda biyar tsakanin Fabrairu zuwa Afriln 2025 domin tantance matakan gyara. WHO ta yaba wa NAFDAC kan ci gaba da samun tsari mai ƙarfi, da ke aiki yadda ya kamata, tare da yaba wa goyon bayan gwamnati wajen ƙarfafa hukumar.

Shugaba Tinubu ya jinjina wa shugabanni da ma’aikatan NAFDAC bisa ƙwarewa da sadaukarwa, yana mai cewa wannan nasara ta ƙara ɗaukaka matsayin Najeriya a fannin kula da  lafiya da shirin kare cututtuka.

Ya ce wannan nasara na daidai da kudirin gwamnatinsa na Renewed Hope Agenda domin sauya tsarin kula da lafiya.

Shugaban ya yi nuni da ci gaba da ake samu, ciki har da inganta  cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 17,000, kyautata kulawa da mata masu juna biyu da na’urorin gano cututtuka a yankunan da ba su da iisassun kayayyakin kula da lafiya, horar da ma’aikatan lafiya 120,000, da kuma ninka yawan masu amfani da shirin  inshorar lafiya na ƙasa cikin shekaru uku.

Ya kuma tabbatar da aniyarsa ta ƙarfafa samar da kayayyakin kiwon lafiya a cikin gida da jawo ra’ayin masu zuba jari a fannin lafiya.

Tinubu ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa NAFDAC a yunkurinta na cimma matsayin WHO Maturity Level 4, mafi girma a duniya kan ingancin sarin kula da magunguna.

 

Daga Bello Wakili

 

 

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita.

Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita.
Rahotannin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) sun nuna cewa, kusan yara 300,000 ne ake haifa da cutar Sikila a duk shekara a fadin duniya, inda yankin Kudu da Sahara a Afirka ke dauke da kashi 75% na wannan yawan.
A Najeriya kadai, ana kiyasta cewa fiye da yara 150,000 ake haifa da cutar Sikila a kowace shekara — hakan ya sa Najeriya ke da mafi yawan masu fama da cutar Sikila a duniya.

NAJERIYA A YAU: Halin Da Shirin Samar Da Tsaro A Makarantun Najeriya Ke Ciki DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan cutar amosanin jini don gano yadda masu fama da ita ke ji a rayuwar su.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
  • Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya
  • Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya