2025-08-10@07:42:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1479
«dattawa ta 10»:
Jaridar Tehran Times, ta nakalto cewa, Iran da Amurka a shirye suke su fara wata sabuwar tattaunawa. Majiyoyin sun ce tattaunawar za ta kasance ba kai tsaye ba, sanann kuma ana sa ran cewa kasar Norway ce za ta kasance mai shiga tsakanin bangarorin biyu. Jaridar ta kasar Iran ta yi nuni da cewa “Tehran ta dage kan cewa batun biyan diyya a kan barnar da aka yi mata a yakin baya-bayan nan ya zama wani muhimmin bangare na duk wata tattaunawa a nan gaba.” A ranar Alhamis kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta duk wata Magana kan wani takamaiman lokaci ko wurin da za a yi shawarwari da Washington, yana mai jaddada cewa “dukkan jita-jita game da hakan...
Dubban mazauna birnin Tel Aviv ne suka taru a tsakiyar birnin a daren jiya Asabar, domin neman kawo karshen yakin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da shirin kara kai hare-hare da kuma mamaye birnin Gaza. Masu zanga-zangar dai na dauke da allula da kuma hotunan wadanda ake tsare da su a Gaza, suna masu kira ga hukumomi da su ba da fifikon sakin su kan fadada ayyukan soji. An kuma bayyana cewa hatta a cikin manyan jami’an soji na Isra’ila, babban hafsan hafsan hafsoshin sojin Isra’ila Eyal Zamir ya yi yunkurin shawo kan majalisar ministoci kan cewa mamaye Gaza ba shi ne zabin da ya dace ba, da kuma tattauna babbar illar da hakan...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar. Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, dukkan ɗaliban aji na ƙarshe na makarantun sakandaren Larabci na gwamnati da suka amfana da wannan tallafi sun kammala rubuta jarabawar NBAIS makon da ya gabata, kuma suna jiran sakamakon. Ya ce wannan tallafi na daga cikin ɗawainiyar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ke yi wajen taimaka wa ɗaliban aji na ƙarshe na sakandaren Larabci domin...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya yabawa yan jarida musamman a khidimar da suka gabatar a yakin kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a lokacinda ya kai ziyarar ganin ido a cibiyar hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa shugaban yay aba da ayyukan da yan jarida a kasar suka yi a lokacin yakin kwanaki 12, na samar da hadin kai tsakanin iraniyawa duk tare da banbanci-bambance da ke tsakaninsu da kuma fadin labaran gaskiyan abinda yake faruwa ga mutanen kasar da kuma duniya gaba daya dangane da yakin. Shugaban yay aba da yadda suka nuna zanga-zangar hadin kai...
Yansanda a kasar Burtaniya ta kama mutane fiye da 200 wadanda suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin London. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai a birnin London na cewa mutane kimani 600-700 ne suka fito suka kuma tsaya a wani wuri kusa da majalisar dokokin kasar wanda ake kira ‘ in Westminster’s Parliament Square ‘ inda suke dauke da kwalaye da rubuton ina son mutuncin ma’aikatar sharia, bana son zalunci. Kafin haka dai gwamnatinn kasar ta haramta zanga-zangar da aka saba gudanarwa a birnin na Lodun a dukkan karshen mako, wato ranar asabar na goyon bayan Falasdinawa da kuma yin allawadai da kasashen yamma musamman gwamnatin kasar Burtaniya wacce daga daga cikin...
Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin ƙalubale da ke fuskantar ‘yan Nijeriya, ciki har da tsadar rayuwa, talauci, yunwa, yawan rashin aikin yi da rashin tsaro, da sauran su. Rahotanni su bayyana cewa akwai tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar dattawa ta 10 a halin yanzu, wanda suka haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Aliyu Wammako (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) da Adams Oshiomhole (Edo)....
Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sulhuntawa da kasashen Armedia da Azarbaijan a fadar white House, amma ta yi gargadin shishigin kasashen waje a yankin Caucasus, da ke makobtaka da Iran. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta ta nakalto wani bayani wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a yau Asabar na cewa, sasantawa tasakanin kasashen biyu wani ci gaba wanda zai iya kaiwa ga tabbataccen zaman lafiya a yankin da kuma ci gaba ga dukkan kasashen yankin. Amma a wani bangare kuma bayanin ya bayyana cewa akwai tsoron kasashen waje musamman Amurka tana iya amfani da wadannan kasashen don cutar da yankin ko wasu kasashe. Don haka ta yi kira ga wadannan kasashe biyu su yi...
Falasdinwa 11 suka rasa rayukansu a yau Asabar a Gaza saboda yunwa, wanda ya kawo adadin wadanda yunwa ta kasashe a Gaza tun lokacinda HKI ta hana shigowar abinci yankin zuwa 212. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na Gaza na fadar haka, sannan masana sun bayyana cewa mai yuwa wannan adadin ya wuce haka, saboda ita yunwa tana hana garkuwan jiki aiki, don haka karamin cuta tana iya kashe mutun saboda yunwa. Sun kara da cewa akwai wasu Falasdinawa da dama a wasu wurare a cikin gaza wadanda basa da lafiya amma yunwa ta karasa su a gida ba tare da sun zo asbiti ba. Larabarin ya kara da cewa a cikin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin Hisroshima a wani ɓangare na dakatar da yaƙin duniya na biyu.! Harin na ranar 9 ga watan!!!!!!!mutane dubu 70 a take bayan mutane 140 da suka mutu kwanaki uku da suka gabata a harin na Hiroshima. An yi ittifakin cewa wannan shine harin da ya tilastawa Japan miƙa wuya a ranar 15 ga watan Agustan wannan shekarar, matakin da ya kawo ƙarshen yaƙin. Bayanai sun...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Shirin gwamnatin mamayar Isra’ila shi ne shirin share al’umma Falasdinu daga kan doron kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Shirye-shiryen da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take yi na mamaye yankin Zirin Gaza da kuma tilastawa al’ummar yankin gudun hijira wani karin shaida ne na musamman da wannan gwamnatin take da niyyar aikata kisan kiyashi a Falastinu da ta mamaye. Ismail Baqa’i ya bayyana shirin gwamnatin ‘yan sahayoniyya na mamaye garin Gaza da sojoji da kuma tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu a matsayin wani shiri na kammala kisan gillar da take yi wa al’ummar Falastinu, yana mai jaddada tofin Allah tsine da Allah wadai da wannan mummunan cin zarafi....
Fitattun matsayi na kasashen Larabawa da kungiyoyi sun yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine da matakin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Kasashe da kungiyoyin Larabawa sun yi Allah wadai da matakin da majalisar ministocin gwamnatin mamayar Isra’ila ta dauka mai hatsari na sake mamaye yankin Zirin Gaza tare da tilastawa Falasdinawa kusan miliyan daya gudun hijira daga birnin Gaza da arewacin zirin Gaza zuwa kudancin kasar. A cikin sanarwar da suka fitar a jiya Juma’a, sun yi la’akari da wannan shawarar da kuma shirin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a matsayin mai hatsarin gaske da zai haifar da bala’in jin kai a zirin Gaza kuma ba za ta taimaka wajen kawo karshen rikicin ba, suna masu...
Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun. ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga kowace ‘yar wasa ta tawagar ƙwallon kwando a tawagar, tare da ba su kyautar gida a Abuja, a lokacin da yake jawabi ga tawagar, Shettima ya ce nasarar da suka samu alama ce ta ƙarfin haɗin kai. “Wannan nasara ta nuna abin da ke faruwa iɗan muka yi aiki tare, matan Nijeriya ba su tama bamu kunya a ɓangaren wasanni ba,...
A gobe Lahadi ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zaman gaggawa kan halin da ake ciki a zirin Gaza, kamar yadda wakilin Al-Mayadeen a birnin New York ya bayyana. Wannan shawarar ta zo ne bayan amincewar majalisar ministocin Isra’ila da shirin firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya hada da shirye-shiryen sojojin Isra’ila na mallake birnin Gaza. Shirin ya tanadi wasu ka’idoji guda biyar na kawo karshen yakin, wanda ya fara da “kwace makaman Hamas,” sannan a dawo da dukkan fursunonin wadanda ke raye ko a mace. Hakan zai biyo bayan kwance damarar zirin Gaza gaba daya, da kafa wata sabuwar gwamnatin da ba ta karkashin ikon kungiyar Hamas ko kuma hukumar Falasdinawa. Za...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince ta bada sama da naira miliyan 156 domin sayen tikitin jirgi na mayar da daliban jihar masu karatun likita har su 184 da suka kammala hutun su a gida zuwa makaranta a kasar Cyprus. Shugaban Hukumar Bada Tallafin Karatu ta Jihar, Alhaji Saidu Magaji, ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, Babban Birnin Jihar. A cewar sa, tuni rukunin farko na dalibai mata su 31 suka tashi ta filin jirgin saman ikko zuwa Istanbul inda za’a dauke su zuwa kasar Cyprus don fara sabon zangon karatu. Alhaji Sa’idu Magaji wanda yake tare da daliban kafin tashin su, ya yaba da kulawar Gwamna Umar Namadi kan tallafawa daliban jihar domin ci gaba da karatun su....
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki daya sannan a samar wa fararen hula agaji a wajen yankunan da ake gwabza yaki.” Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 Kazalika, wasu majiyoyi biyu daga gwamnatin Isra’ila sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa duk hukuncin da majalisar tsaron kasar ta yanke zai bukaci...
Ministan harkokin wajen kasar Iran abbas Aragchi ya rubutawa babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC Hussain Ibrahim Taha, da kuma tokwarorinsa na kasashen Saudiya da Turkiya, Faisal bin Farhan da kuma Hakan Fidan wasiku dangane da bukatar kasashen kungiyar su gudanar da taron gaggawa kan abinda ke faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Aragchi yana cewa, saboda yadda HKI take kara takurawa mutanen Gaza, tana kara daukan matakan keshesu, mung a akwai bukatar kasashen musulmi sun dauki matakai fiye da na baka, wato fadar ‘All..wadai ” kadai. Yakamata kasashen musulmi su dauki matki fiya da haka wanda za’a ganshi a aikace kan Falasdinawa na gaza. Su dauki mataki wanda zai kai ga dakatar...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Kudirin gyaran dokar fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari. Alhaji Hamza Adamu Ibrahim ya yi bayanin cewar, daga cikin shugabanin da suka rike mukaman siyasa da ya kamata su amfana da irin wannan fansho sun hada da Gwamna da Mataimakan Gwamna da Shugaban Majalisar Dokoki da Kuma alfarmar da ya kamata su ci gaba da samu bayan sun bar mulki. Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar, ya gudanar da...
Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da Israila ta dakatar da bude wuta da kawo karshen rikici da Gaza nan take. Sakamakon ya kuma nuna cewa, kaso 80.8 na wadanda suka amsa na ganin cewa mafita ga rikicin Palasdinu ya dogara ne da kafuwar kasashe biyu, inda suka yi kira da a dawo da halaltattun hakkokin kasar Palasdinu. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne a dandalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da...
Falasdinawa masu yawa ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin ‘yan sahayoniyya suka kai kan tantuna da gidaje da ‘yan gudun hijira a Gaza Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu masu yawa da sanyin safiyar yau Alhamis a wasu munanan hare-hare da jiragen yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, inda suka kai harin kan gidajen fararen hula da kuma tantunan ‘yan gudun hijira. Jiragen saman sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wani tanti na ‘yan gudun hijira a yankin Tal, kudu maso yammacin birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa akalla biyar tare da raunata wasu. A yammacin sansanin ‘yan...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana bukatar samar da wata sabuwar hanyar yin mu’amala da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, inda ya bayyana cewa, ba a kayyade lokacin shiga wasu shawarwari da Amurka ba, ya kuma tabo batun muhimmancin dangantakar dake tsakanin Iran da kasashen Rasha, Sin da Masar. A cikin wata sanarwa da ya aikewa gidan talabijin na Iran , Araqchi ya jaddada bukatar samar da sabon tsarin hadin gwiwa tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, yana mai nuni da cewa, abubuwan da suka faru wanda ya kai ga kaiwa kasar Iran hari bisa fakewa da rahotannin siyasa na huumar IAEA, yasa dole ne Iran ta...
Ofishin jakadancin kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kausasan kalamai kan rahotannin dake cewa tsohon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ziyarci yankin Taiwan na Sin da kiran da ya yi wa kasashen yamma su kulla huldar tattalin arziki da yankin. Wani kakakin ofishin jakadancin ya bayyana a jiya cewa, suna adawa matuka da duk wata ziyara da wani dan siyasar Birtaniya zai kai Taiwan bisa ko wane dalili. Kakakin ya kuma nanata cewa, Taiwan bangaren kasar Sin ne da ba zai iya ballewa ba, kana batutuwan da suka shafi yankin, batutuwa ne na cikin gidan Sin da ba sa bukatar katsalandan daga waje. Bugu da kari, ofishin jakadancin ya ce babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar Zirin...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni. Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da wannan kyauta cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook a wannan Larabar. Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina “Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan ’yan wasan da suka rasu fuloti ɗaya da kuma naira miliyan biyar kowannensu,” in ji sanarwar. Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ’yan wasan...
Fararen hula 14 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai El Fasher na Sudan Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Sudan ta sanar da cewa: kungiyar Rapid Support Forces ta kasar Sudan ta Dakarun kai daukin gaggawa ta kashe akalla fararen hula 14 a lokacin da take yunkurin tserewa wani yanki da aka killace a yankin Darfur, bayan shafe sama da watanni 27 ana yaki tsakanin dakarun ‘yan tawaye da sojojin Sudan. Kungiyar lauyoyin gaggawa da ke tattara bayanan cin zarafi da aka yi a yakin, ta kuma watsa rahoton cewa: “An samu raunuka da dama, kana an kama wasu fararen hula da ba a san...
Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan. Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje da lalacewar gonaki da rijiyoyi da sauran su. Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas Mutanen da lamarin ya shafa sun ce suna bukatar agajin gaggawa na abinci da magani da tsaftataccen ruwan sha. Shugaban karamar hukumar ta Tangaza, Isah Salihu Kalenjeni, ya jagoranci wata tawaga...
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira wani zama na gaggawa a jiya Talata, domin tattauna mummunan halin da ake ciki a zirin Gaza, inda ya mayar da hankali musamman kan fursunonin Isra’ila da ke hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinu. A tsakiyar zaman dai batutuwa biyu ne suka dauki hankali: daya daga kasashen yammacin turai don ba da fifiko kan batun sakin fursunonin Isra’ila da aka yi garkuwa da su, da kuma wani wanda ke samun goyon bayan kasashe da dama, wanda ke nuni da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi a kan Falasdinawa sama da miliyan biyu da aka yi wa kawanya. Mataimakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Turai, Asiya ta Tsakiya da Amurka, Miroslav...
Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata. A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana. Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Mista Kamto...
Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na da muhimmanci matuƙa wajen tabbatar da lafiyar yara da kuma inganta cigaban su tun daga ƙuruciya. Ta kuma bayyana cewa makon yana da nufin wayar da kan jama’a musamman a tsakanin iyalai game da amfani da shayar da nono, tare da ƙarfafa gwiwar ma’aikatan lafiya da su ci gaba da fafutukar wayar da kai a fadin karamar hukumar. A nata jawabin, Sakatariyar Lafiya...
Dakarun sojin Nijeriya sun hallaka aƙalla ’yan ta’adda 17 na ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a wasu hare-haren kwantan bauna da suka kai a jihohin Borno da Adamawa a tsakanin ranakun 23 ga Yuli zuwa 2 ga Agustan 2025. Kyaftin Reuben Kovangiya, Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa Ya bayyana cewa sojojin ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun kai hare-haren ne a ƙananan hukumomin Bama, Konduga, Gwoza, Magumeri, da Biu a Jihar Borno, da kuma Michika da ke Jihar Adamawa. A cewarsa, an...
Wasu zauna gari banza sun burma wa wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) wuka har lahira a Kasuwar Shuwarin da ke ci Karamar Hukumar Kyawa a Jihar Jigawa. Kakakin Hukumar NSCDC reshen Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani, ya bayyana cewa an kai wa jami’in hari ne a lokacin da yake bakin aiki a ranar Linitin a lsashin sayar da shanu na kasuwar (Kara), inda ’yan iskan suka kai wa jami’in hari. Ya ce “Maharan da ake zargin suna xauke da wuqaqe ne suka farma jami’in, suka yi masa mummunar varna, inda maharan suka far wa jami’in da wukake, kuma abin takaici, ya rasa ransa nan take. Kakakin ya bayyana cewa, “Wanda abin ya shafa mai suna Sufeto Bashir Adamu...
Hukumar Yaki da Hamada da Sauyin Yanayi ta Kasa ta kammala shirye-shiryen dasa itatuwan dabino miliyan hamsin (50,000,000) a jihohi goma sha ɗaya 11 da ke fama da fari a Najeriya. Daraktan Hukumar, Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin dasa itatuwan dabinon da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya ce za a dasa itatuwan dabino guda dubu dari biyar (500,000), tare da wasu nau’o’in itatuwa na gida a faɗin jihar Jigawa. Alhaji Salihu Abubakar ya yi kira ga jama’a da su rungumi al’adar dasawa da kula da itatuwa domin magance matsalolin hamada, zaizauar ƙasa da sauyin yanayi. A cewarsa, Hukumar tana aiki tukuru a jihohin da ke fama da fari a...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin ‘yan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin yahudawan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. A lokacin da yake halartar taron manema labarai da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya gudanar a yau Litinin, Araqchi ya ce: Na farko dai ya zama wajibi a gare shi ya girmama dukkanin shahidai: shahidan juyin juya halin Musulunci, shahidan tsaro mai alfarma (1980-1988), da dukkanin shahidan da suka sadaukar da rayuwarsu wajenkare kasa, tun farko-farko har zuwa yau, musamman ‘yan jaridu da shahida yakin matsorata masu wuce gona da iri na...
Mashawarcin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Za su koma shawarwari da Amurka ne yayin da suke dauke da makamai a hannu Mai baiwa ministan harkokin wajen Iran shawara Sa’ed Khatibzadeh, ya jaddada cewa: Iran ba za ta sake amincewa da Amurka kan duk wata tattaunawa da za ta iya yi ba, yana mai cewa makomar yankin ba kamar yadda Amurka da Isra’ila suke zato ba. A ziyararsa ta farko da ya kai kasar China bayan hare-haren da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Iran a baya-bayan nan, Khatibzadeh ya yi wata fitacciyar hira da gidan talabijin na Phoenix, inda ya tattauna muhimman batutuwa da suka hada da ci gaban Shirin makamashin nukiliyar Iran, dangantakar shiyya da...
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin Kano, yana da tarihin shekaru 115. An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Mai ba Gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi. Hadimin gwamnan ya ce an yanke shawarar sauya ma’anar wurin,...
Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe. Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa gwamnatin na nan tana duk abin da za ta iya yi don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin. Lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Manir Haidara ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin ta samar da tsaro a duk faɗin jihar Zamfara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
Shugaban kasar Lebanon Josepth Aoun ya yi alkawalin adalci ga iyalan wadanda fashewar tashar jiragen ruwa na Beirut ya sha bayan shekaru 5 da aukuwar hakan. Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau litinin. Ya ce har yanzun ba wanda aka kama ko ake tuhuma da haddasa wannan fashewar tun aukuwarsa a ranar 4 ga watan Augustan shekara 2020. Labarin ya kara da cewa Fashewar tashar jiragen ruwa na Beirut shi ne fashewa mafi muni bayan na manyan manyan makamai kare dangi, inda a wannan karon taki wanda aka yi shi da sinadarin ‘Amonium nitrate’ ya fashe ya kuma kashe mutane 220 sannan wasu kimani 6,500 suka ji rauni da kuma asarar...
Rahotanni daga Gaza na cewa sojojin Isra’ila sun sake buɗe wuta kan Falasɗinawa da ke cikin tsananin buƙatar agaji a kusa da inda ake rabon kayan tallafi a cibiyoyi biyu, a jiya Lahadi. Asibitoci a Gaza sun ce aƙalla Falasdinawa 27 aka kashe. Rahotanni na cewa sojojin sun buɗe wa mutane wuta bayan isa gab da ɗaya daga cikin cibiyoyin rabon agajin na gidauniyar da Amurka da Isra’ila ke mara wa baya a Rafah. Sanan sauran kuma an kashe su ne a sansanin da ke tsakiyar Gaza. Har yanzu sojojin Isra’ila ba su yi martani ba kan wannan rahoton. Hamas ta ce ƙungiyar agaji ta Red Cross kaɗai za ta iya miƙa wa ‘yan Isra’ilar da take riƙe dasu a...
Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi. An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano. Kano tana da gidan yari guda goma. Biyu a cikin birni—Kurmawa da Goron Dutse, yayin da sauran kuma suke a kananan hukumomin Wudil, Kiru, Rano, Sumaila, Bichi, Tudun-Wada, Gwarzo, da Dawakin-Tofa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi. An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano. Kano tana da gidan yari guda goma. Biyu a cikin birni—Kurmawa da Goron Dutse, yayin da sauran kuma suke a kananan hukumomin Wudil, Kiru, Rano, Sumaila, Bichi, Tudun-Wada, Gwarzo, da Dawakin-Tofa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al’umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana. Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya bayyana haka yayin da yake duba aikin jingar ruwan kogi da ya ratsa garuruwan Auyo da Tsidir da Agin da Matsa da Sorakin da Jiyan da Tage da Turabu da kuma Tandanu. Alhaji Hamza Hadejia ya ce daga zuwan Gwamna Umar Namadi kan karagar mulkin Jihar, ya dauki kwararan matakai don kaucewa ambaliyar ruwa, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ya...
Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza ba Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta bayyana cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila sun boye kusan kashi 88% na binciken laifukan yaki ko cin zarafin da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata a kan Falasdinawa a zirin Gaza ba, ba tare da gabatar da tuhumce-tuhumce ko cimma matsaya mai kyau ba tun farkon fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza a watan Oktoban shekara ta 2023. Rahoton ya nakalto Action on Armed Violence yana cewa: gwamnatin mamayar Isra’ila na neman dauke hankalin duniya kan rashin hukunta ta ta hanyar gujewa daukar alhakin manyan laifukan...
A kokarin da Gwamnatin Jihar Jigawa ke yi na kara habbaka harkokin noma, shirin ACRESAL yace sami amincewar gwamnatin na siyo injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana guda 3,000 domin tallafawa manoma. Shugaban Shirin na Jihar, Malam Yahaya Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yana mai cewar, samar da injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana ga manoman na da nasaba da bunkasa aikin gona a jihar Jigawa. A cewar sa, shirin ACRESAL na jihar ya sami sahalewar gyaran karin wasu cibiyoyin renon itatuwa guda 3 a sassan jihar. Malam Yahaya Uba Kafin Gana ya kara da cewar, cibiyoyin renon itatuwan da za’a gyara sune na garuruwan Birnin Kudu da Kafin Hausa da...
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya yi nuni da cewa; yanzu mafi akasarin mutane, ba sa son abin da zai taimaka musu; kawai dai sun fi mayar da hankali wajen sharholiya iri-iri. da yake amsa tambaya a kan me yasa ya fi mayar da hankali wajen ɗora bidiyo, musamman na jarumai mata a Masana’antar Kannywood a shafukansa na sada zumunta, musamman kuma ‘Facebook’? Sai Baba Sadiƙ ya ce; ba komai ba...
Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa. Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana cewa a jiya Asabar yahudawan sun kashe mutane 38 masu neman abinci. Labarin ya kara da cewa, duk tare da sanarwar da gwamnatin HKI ta bayar na tsagaita wuta a wani bangar na zirin gaza, saboda bawa Falasdinawan dama samun agaji daga wasu wurare amma sojojin HK sun ci gaba da kashe Falasdinawan . Zuwa ranar jumma’an da ta gabata, sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa...
Magana ta gaskiya matsala daya ce zuwa biyu ko uku, na farko akwai laifin iyaye, na biyu akwai laifin samari da suke zuwa su yi auren, na uku kuma akwai laifin amaryar wacce ita ce take zaman auren. Bari na fara da maganar farko, dalilin da ya sa na ce laifin iyaye ne shi ne; duk mutumin da ya zo zai auri ƴarka, idan kana da ƴa ta isa aure, ya kamata ka zaunar da shi ka tambaye shi; mene ne ma auren, kuma me yasa yake son ya auri ƴar taka? da yawan samarin da suke yin aure, ba su san ma mene ne auren ba. An Nemi A Kafa Dokar Ta-ɓaci Kan Masu Ƙwacen Waya anyoyin Da Za...
Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’, wato lashe kofin a karo na 10 a tarihi kuma ta ci gaba da jan zarenta na tawagar mata wadda babu kamarta a wannan nahiyar. Nijeriya ta ƙara kafa wani tarihin kasancewar ita ce ta farko da ta lashe sabon kofin na gasar bayan sauya shi da aka yi daga wanda aka saba amfani da shi a baya. A ƙarshen wasan Rasheedat Ajibade ta Nijeriya...
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na bada managartan shawarwari da za su yi wa kananan hukumomin jihar jagoranci wajen gudanar da ayyukan su kamar yadda yakamata. Shugaban Kwamatin Kananan Hukumomi na Majalisar, Alhaji Aminu Zakari, ya bada wannan tabbacin lokacin rangadin kwamatin majalisar a sakatariyar karamar hukumar Birniwa. Alhaji Aminu Zakari Wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa, yace ziyarar Kwamatin na daga nauyin da aka dorawa bangaren majalisa wajen bibiyar yadda Gwamnati ta ke aiwatar da manufofi da shirye shirye domin tabbatar da shugabanci nagari. Alhaji Aminu Zakari yace haka kuma Kwamatin yana la’akari da batun zamantakewar jama’ar da tattalin arziki a matsayin ma’aunin ci gaban rayuwa da koma bayana domin baiwa bangaren zartaswa shawarwari dan bullo...
Saboda haka, ƙarfin APC a zauren majalisar dattawa mai mambobi 109 ya kai 70, kujeru biyu kadai take buƙata ta cika 72 don samun rinjaye na kashi biyu cikin uku. PɗP yanzu haka tana da kujeru 28, yayin da jam’iyyar LP ke da biyar. Jam’iyyar SɗP na da kujeru biyu, yayin da jam’iyyar NNPP da APGA ke da kujeru guda daya kowannansu. A yanzu haka, akwai kujeru biyu na majalisar dattawa da babu kowa. Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), har yanzu ba ta gudanar da zaɓen cire gurbin Sanata Ifeanyi Ubah, mai wakiltar Anambra ta kudu, wanda ya rasu a farkon wannan shekara, da Sanata Monday Okpebholo, mai wakiltar Edo ta tsakiyar, wanda ya bar kujerarsa bayan...
Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina ta kori ɗalibanta 57 kan laifin satar jarabawa. Hukumar gudanarwar jami’ar ta kuma dakatar da wasu dalibai biyar na tsawon shekara guda tare da ba wasu biyu takardar gargaɗi kan aikata laifukan jarabawa. A safiyar Asabar kakakin jami’ar, Hajiya Fatima Sanda, ta sanar da cewa majalisar jami’ar ta amince da matakin ne bayan karɓar rahoton kwamitin ladabtarwa kan laifukan jarabawa na jami’ar. Sanarwar ta ƙara da cewa an dakatar da ɗalibai biyar na tsawon shekarar karatu biyu, tare da soke duk jarabawarsu da laifin ya shafa. Jami’ar ta kuma jaddada cewa ba za ta lamunci aikata laifukan jarabawa ko rashin ɗa’a ba.
Hukumar kula da samar da agaji ta MDD OCHA ta bada sanarwan kissan Falasdinawa fiye da 100 a lokacinda suke kokarin neman abincin da zasu ci. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin shugaban kungiyar ta OCHA Farhan Haq yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa bai kamata mutane sum utu a wajen neman abinci ba. Dokokin kasa da kasa sun tabbatar da cewa, mutum ko menene laifinsa bai kamata a hana shi abinci ba, kuma bai kamata yam utu saboda neman abinci ba. Farhan Haq ya yi gargadin cewa idan wannan halin ya ci gaba, to dukkan duniya sun ji kunya, idan suna da shi, suna ganin Falasdinawa suna mutuwa a lokacinda kowa a duniya...
Masu zanga-zanga a duk fadin siriya sun bayyana rashin amincewarsu da ci gaba da kisan mabiya mazhabar Aalawiyya a bakin nruwan tekun medeteranin. Da kuma rikicn da ya kai ga zubar da jnin mutanen kasar a Sewaida saboda shishigin da HKI take yi a cikin al-amuran cikin gida na kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran kasar suna fadar cewam dubban mutanene suka fito suka kuma taru a babban dandalin da ke tsakaiyar suwaida inda suke kira ga gwamnatin rikon kwarya ta HTS ta janye yan ta’addan da ta tura zuwa yankin suwaida don kashe mutanen yankin. Masu zanga zangar suna dauke da alluna wadanda aka rubuta a kansa : a bude hanyoyi don...
Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa, HKI ba zata iya rayuwa ta kuma aikata abinda take aikatawa a gaza ba, ba tare da tallafin Amurka ba. Don haka Amurka da alhakin duk abinda yake faruwa a Gaza. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Syyid Abdul Malik Badruddin Huthi yana fadar haka a jawabin mako mako da ya saba gabatawa. Labarin ya kara da cewa kawancen gwagwarmaya a yankin ba zasu ajiye makamansu ba, har zuwa lokacinda aka kawo karshen ta’asan da ke faruwa a Gaza. Alhuthi ya bayyana haka ne a dai-dai lokacinda, kawancin masu gwagwarmaya, a yankin wato Hizbullah na kasar Lebanon, Gwagwarmayan musulunci a Iraki da kuma JMI da kuma Yemen suke...
Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba. Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da aka gabatar da ke tabbatar da wannan zargi, wanda hakan ya sa binciken ya tsaya. Kimanin wata biyar ke nan da Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai na Nijeriya suka fara bincike kan zargin, amma har yanzu babu wani sakamako ko rahoto. Aminiya ta gano cewa tun sama da shekara goma da suka wuce, ake zargin wasu ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa da...
Iyalai ‘yan Sudan da dama ne suka taru a babbar tashar jirgin kasa ta birnin Alkahira, dauke da jakunkuna da kayayyaki a lokacin da suke shirin komawa gida bayan da suka tsere daga rikicin Sudan. Suna cikin dubban ‘yan kasar Sudan da suka rasa matsugunansu da ke kan hanyarsu ta komawa daga Masar zuwa yankunan da sojojin Sudan suka kwato kwanan baya daga dakarun gaggawa na gaggawa a birnin Khartoum da bayanta tun farkon wannan shekara. Iyalan sun kasance suna jiran shiga jirgin kasa da zai nufi birnin Aswan da ke kudancin Masar. Daga nan ne za su yi tafiya ta bas zuwa babban birnin kasar Sudan, Khartoum, a cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar....
A wani samame kuma, ƴansanda sun kama wani da ake zargin barayin USB ne, tare da ƙwato kayayyakin da aka lalata, ciki har da wata mota da aka yi amfani da ita wajen gudanar da aikin ba bisa ƙa’ida ba, inda ya ƙara da cewa “an kama su ne biyo bayan bayanan sirri da aka samu a ranar 15 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 0300 na safe.” Wanda ake zargin mai suna Abubakar Sadi mai shekaru 25 dan asalin Kofar Waika ta jihar Kano, an kama shi a wurin da lamarin ya faru, yayin da sauran wadanda ake zargin suka tsere cikin daji. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
A daren Juma’a ne dab da wayewar gari wata motar tirela ɗauke da awaki da kaji wadda ta taso daga Gwauron Dutse a Jihar Kano ta yi haɗari. Motar tirelar wadda take ɗauke da dakon awaki da kuma kwandunan kaji mai yawa a samanta baya ga mutane da ta ɗauko ta yi haɗarin a kusa da kasuwar Ɗan Magaji saman gadar da ke kan hanyar Zariya zuwa Kaduna. Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi Awaki kusan sama da 100 suka mutu da kuma kaji kusan ɗari 500 ne aka ƙeyasta sun mutu. Sai dai ba a sami asarar rai ko ɗaya...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Matukar dai Trump ya bukaci dakatar da inganta sinadarin Uranium gaba daya a Iran, to ba za a cimma wata yarjejeniya ba Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Araqchi ya jaddada a wata hira da jaridar Financial Times cewa: Iran na neman a biya ta diyya kan irin hasarar da ta yi a harin wuce gona da irin kwanaki 12 na ta’addanci kan kasarta. Araqchi ya yi nuni da bukatar Amurka ta bayyana dalilin da ya sa ta kai farmaki kan Iran a tsakiyar shawarwari tare da bayar da tabbacin cewa ba za a sake daukar irin wannan mataki ba. Araqchi ya kara da cewa, warware rikicin makamashin nukiliya na bukatar nemo...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tauraron dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya kammala komawarsa ƙungiyar Galatasaray ta ƙasar Turkiyya daga Napoli, a wata yarjejeniya ta dindindin da ta kai Yuro miliyan 75. Ƙungiyar Galatasaray ta sanar da kammala ɗaukar Osimhen a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa yarjejeniyar ta fara aiki daga nan take. Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru huɗu tare da zakarun na ƙasar Turkiyya, kuma za a biya shi Yuro miliyan 15 a kowace kakar wasa. Hakazalika, zai karɓi ƙarin Yuro miliyan 5 a matsayin hakkinsa na mallakar hoto, yayin da Napoli za ta sami kashi 10 cikin 100 na duk wani kudi da za a sayar da shi...
Jim kadan bayan da kungiyar kai Dauki Gaggawa ta kasar Sudan ta sanar kafa gwamnatin mai mambobi 15, kungiyar tarayyar Afirka ta mayar da martanin kin amincewa da ita. Bugu da kari kingiyar ta tarayyar Afirka ta kira yi kasashen da suke mambobi a cikinta da kuma kungiyoyin kasa da kasa da kar su amince da halarci wannan gwamnatin. Har ila yau kungiyar ta tarayyar Afirka ta kuma yi gargadin cewa matakin da kungiyar ta RSF ta dauka zai iya tarwatsa Sudan ya kuma rusa Shirin zaman lafiya wanda dama yana tangal-tangal. Kungiyar ta RSF ta bayyana Muhammad Hassan al-Ta’aysh a matsayin Fira ministan, sai kuma Janar Muhammad Dagalo a matsayin shugaban kasa. Kasar Sudan ta fada cikin yaki ne...
Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Al-Husi wanda ya gabatar da jawabi a jiya Alhamis, ya bayyana abinda yake faruwa a Gaza da cewa, yana nuni da halayyar keta da mugunta ta ‘yan sahayoniya, don haka ya zama wajibi akan al’ummar musulmi da dukkanin jinsin bil’adama da su kalubalanci wannan irin zalunci da ba shi da tamka. Sayyid Abdulmalik al-Husi ya kuma ce, wadanda aka fi cuta a Gaza su ne kananan yara, sannan kuma ya yi ishara da yadda kasashen larabawa da kuma kungiyoyin kasa da kasa su ka kyale Gaza. Shugaban kungiyar ta Ansarullah ya ce; Da akwai kananan yara 100,000 da suke fuskantar hatsarin mutuwa saboda yunwa a Gaza, daga cikinsu da akwai jarirai 40,000 da suke fuskantar...
Mujallar Qiushi ta kasar Sin za ta wallafi jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping gobe Jumma’a 1 ga watan Agusta, wanda Xi ya taba gabatarwa a gun babban taron kiyaye muhallin halittu na kasar Sin a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2023. Jawabin ya bayyana cewa, bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin ta riga ta shiga sabon mataki na neman samun ci gaba mai inganci, wanda ke bukatar gaggauta kiyaye muhallin halittu da rage yawan iskar Carbon da ake fitarwa. Aikin kiyaye muhallin halittu na fuskantar matsin lamba. Ya kamata a yi kokarin zamanantar da kasar Sin bisa tushen samun daidaito a tsakanin bil Adama da muhallin halittu. (Kande Gao) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
A wani yunkuri na yaki da rashin abinci mai gina jiki da kuma karfafa tattalin arzikin mata a jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi ya jagoranci bikin yaye mata 600 da suka samu horo kan yadda ake sarrafa abincin yara mai gina jiki daga kayayyakin da ake samarwa a gida, wanda aka fi sani da “Tom Brown”. Malam Umar Namadi ya bayyana wannan shiri a matsayin wata dabara ta cikin gida da aka kirkira domin shawo kan matsalolin rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara, da kuma karfafa tattalin arzikin mata. “Muna matukar godewa Allah da ya ba mu hikima da basira don kirkirar wannan tsari wanda zai taimaka mana mu cimma manufofi da dama a lokaci guda.” In ji...

Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Jihar Jigawa ta horas da Malaman makarantun sakandare kimanin dubu 20 ilimin fasahar sadarwar zamani (digital). Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta ƙasa (NITDA) da Cibiyar Zaman Lafiya ƙarƙashin jagorancin Farfesa Hauwa Ibrahim da take Amurka, a ziyarar ban girma da suka kai a gidan gwamnati da ke Dutse. Peter Obi zai lashe jihohin Arewa idan ya koma PDP – Jerry Gana Mun yi asarar shanu 340 a hannun ɓarayi a Yuli — Miyetti Allah Ya ce: “Mun gabatar da cibiya ta dijital don malamai, don sadarwa da kuma kula da ilmantarwa a matakin farko, mun sanya hannu kan haɗin gwiwa na...
A nasa tsokaci game da batun, wakilin musamman na kasar Sin a yankin kahon Afirka Xue Bing, ya ce Sin ta dade tana goyon bayan matakan wanzar da zaman lafiya da ci gaba a yankin. Ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar shawo kan tarin kalubale dake addabar duniya. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Amurka ta bada sanarwan kakabawa gwamnatin jeka na yi ka ta Falasdinawa takunkuman hadawa jami’anta visar shiga kasar a safiyar yau Alhamis. Shafin yanar gizo na labarai ‘abrabNews’ na kasar Saudiya ya bayyana cewa majiyar fadar white House ta bayyana cewa gwamnatin Palasdinawa musamman Mahmood Abbas suna zagon kasa ga kokarin da kasar Amurka ta ke yi don samar da zaman lafiya a Gaza. Labarin ya kara da cewa gwamnatin Falasdinawa tana mu’amala da wasu kasashen wai don amincewa da samuwar kasar Falasdinu a cikin watan satumba mai zuwa a MDD. A yau Alhamis ne wakilin Amurka na musamman a gabas ta tsakiya Steve Witkoff Yake isa HKI don tattauna da gwamnatin saboda rage matsin lambar da wa HK...
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙarin wa’adin shekara guda ga shugaban hukumar Kwastan ta Nijeriya, Bashir Adewale Adeniyi. Kafin wannan ƙarin wa’adin, aikin Adeniyi zai kare ne a ranar 31 ga Agusta, 2025. Sai dai sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce wannan mataki na Tinubu zai ba Adeniyi damar kammala muhimman gyare-gyare da ayyuka da gwamnatin ke aiwatarwa a hukumar. Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje A cikin manyan ayyukan da ake son a kammala akwai shigar da...
Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani A cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025. Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026. Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu...
Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis. Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani A cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025. Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026. Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu...
Aƙalla mutum tara ne suka rasu, yayin da wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji 17 ya kife a Jihar Jigawa. Yawancin fasinjojin da hatsarin ya rutsa da su ’yan mata ne. Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres Lamarin ya faru ne da ranar yammacin Lahadi, 27 ga watan Yuli, 2025, lokacin da kwale-kwalen ya taso daga ƙauyen Digawa a Ƙaramar Hukumar Jahun zuwa ƙauyen Zangon Maje da ke Ƙaramar Hukumar Taura. Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis. Ofishin NEMA na Kano, ya bayyana cewa kwale-kwalen ya kife ne a tsakiyar kogin. Wasu mazauna...
Manchester United ta soma tattaunawa da Paris St-Germain kan golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, amma Chelsea da Manchester City na cikin masu sha’awar golan. (Telegraph – subscription required, external) Yayin da ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince ya koma Liverpool, Newcastle ta saka ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz, mai shekara 24 cikin lissafinta. (Mail – subscription required, external) Crystal Palace ta sanar da Arsenal cewa sai ta fara biya aƙalla fam miliyan 35 kafin ta ɗauko Eberechi Eze, daga baya ta cike sauran kuɗin. (Guardian, external) Palace a shirye take ta biya fam miliyan 27.6 domin ɗauko ɗanwasan baya na Jamus Yann Bisseck, mai shekara 24 daga Inter Milan domin maye gurbin Marc Guehi, da ake alaƙantawa da Liverpool. (Gazzetta dello Sport – in Italian, external) Chelsea na ci gaba da matsi kan Alejandro...
Tawagar Iran ta fice daga taron majalisun dokokin kasashen duniya kafin fara jawabin jami’in gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a zaman taron A wata gagarumar nuna rashin amincewa da tushen zaluncin da ya addabi duniya, tawagogin kasashen Iran, Yemen, da Falasdinu sun fice daga zaman taron Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, bayan da shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” zai fara gabatar da jawabinsa mai kunshe da bayanai neman tunzura jama’a, wanda kuma bayanai suka haifar da cece-kuce a tsakanin wadanda suka zauna suka saurara. A cikin jawabin shugaban majalisar dokokin Isra’ila “Knesset” ya bayyana cewa; Akwai yiwuwar samar da ‘yantacciyar kasar Falasdinu a wajen yankunan Falasdinu, musamman a biranen London da Paris na kasashen Birtaniya da Faransa. Wannan matakin na nuna...
Bayo Onanuga, Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya ce wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu ne kawai saboda ya fito daga Kudancin Najeriya. Yayin wata hira da Trust Radio, Onanuga ya ce maganar cewa ana yi wa Arewacin Najeriya wariya ba gaskiya ba ce, face tsantsar siyasa kawai. Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya Ya ce ƙorafin da Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi na cewa an yi watsi da Arewa wajen naɗe-naɗen muƙaman gwamnati da ayyukan ci gaba, wata dabara ce kawai don rage ƙimar shugabancin wanda ya fito daga Kudu. Ya shawarci ’yan siyasar Arewa...
Shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Aminu Zakari, ya ce kwamatin ya jinkirta rangadin kananan hukumomin jihar 27 a Zango na uku na shekarar 2024 ne a sakamakon zaben kananan hukumomi, don haka akwai bukatar ba su damar gudanar da ayyuka kafin tantance kwazon su. Alhaji Aminu Zakari ya yi wannan tsokaci ne a sakatariyar karamar hukumar Sule Tankarkar a ci gaba da rangadin kananan hukumomi da kwamatin yake yi. A cewar sa, kwamatin zai tantance kasafin kudin karamar hukumar na shekarar 2024 da 2025 na ayyuka ta da jerin ayyukan raya kasa, da takardun biyan kudaden ayyukan da littafin ta’ammalin kudaden na banki. Yace kwamitin zai tantance takardun kudaden shiga tare da...
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da shirin tallafi guda biyu da suka kai fiye da naira miliyan 392, ga membobin kungiyar direbobi ta NURTW da kuma ƴan kungiyar mahauta a jihar Jigawa. Wannan tallafi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na inganta rayuwar masu sana’o’in da ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum. A wajen kaddamar da shirin a filin wasa na Dutse, Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin yana da manufa ta musamman domin tallafa wa jama’a kai tsaye. Ya ce ƙungiyoyin NURTW da mahauta suna da matuƙar tasiri, ba kawai ga membobinsu ba, har ma da al’umma gaba ɗaya, shi ya sa gwamnatinsa ta ga dacewar tallafa musu. Gwamnan ya kara da cewa taimakon...
Ma’aikatar kiwon lafiya a Gaza ta bada sanarwan cewa falasdinawa 7 ne suka mutu a zirin gaza saboda yunwa a cikin sa’o’i 24 da suka gabata wanda ya sa adadin mutanen fa yunwa ta kashe a Gaza kai kai 154. Tashar talabijan ta Prersstv a nan Tehran ta nakalto Asbitin Nasir na Gaza na cewa yawa wadanda yunwa ta kashe sanadiyyar kofar ragon da HKI ta yiwa Gaza ya kai 154 sannan 89 daga cikinsu jarirai ne suka fi yawa ya zuwa yau Laraba. A makon da ya gabata ne hukumar abinci ta duniya wato ‘, the United Nations World Food Program (WFP)” ta bada sanarwan cewa 1/3 na mutanen gaza suna kwana da yunwa saboda rashin abinci sanadayar hana...
Sanata Aniekan, ya gargaɗi jama’a da su daina yaɗa jita-jita ko bidiyo na ƙarya da ka iya tayar da hankali, tare da yaba wa da ƙoƙarin da ofisoshin jakadancin Nijeriya da Ghana da kuma ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ke yi wajen warware matsalar. Ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya, haɗin kai da girmama juna su ne ci gaba da zama ginshikin dangantakar ƙasashenmu biyu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ci gaba da hare-haren da dakarun Isra’ila ke kai wa a Zirin Gaza, yanzu adadin Falasdinawan da suka kashe ya kai 60,034. A cewar wasu alkaluma daga Ma’aikatar Lafiya ta Gaza, baya ga wannan, adadin wadanda aka raunata kuma a yanzu sun haura 145,870. Ma’aikatar ta kuma ce har yanzu ana zargin akwai mutanen kuma da ke karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa, wadanda ba za a iya ciro su daga ciki ba. Fiye da kaso daya cikin uku na mutanen yankin na shafe kwanaki ba su ci abinci ba, kamar yadda wani rahoton samar da abinci mai lakabin IPC na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar. Rahoton ya ce ana samun karin hujjoji da ke nuna ana fama da...
Da safiyar yau Laraba Yahudawa ‘yan share wuri zauna sun kutsa cikin masallacin kudus a karkashin kariyar jami’an tsaron ‘yan sahayoniya, tare da yin ayyukan bautar yahudanci a ciki. Wannan kutsen dai yana zuwa ne a daidai lokacin da sojojin HKI suke ci gaba da kai wa Falasdinawa hare hare a cikin yankuna mabanbanta na Gaza da yammacin kogin Jordan. Rahotanni da suke fitowa daga Falasdinu sun ce ya zuwa yanzu adadin wadanda su ka yi shahada sun haura 18. Daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akawi Fursunonin da aka ‘yanto su a musayar fursunoni tsakanin Hamas da HKI. A yankin Khalil sojojin HKI sun kutsa cikin kauyen Ummul-Khair tare da kame mutane 8 bayan yin kutse a...
An yi kira ga manoma a jihar Kwara da su yi taka tsan-tsan domin hasashen za a samu ruwan sama da kuma tsawa da ake hasashen nan da kwanaki masu zuwa. A wata sanarwa da kwamishinan noma da raya karkara na jihar, Dr, Afees Abolore ya fitar, ya ce a cewar hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ana sa ran wasu sassa na jihar za su fuskanci ruwan sama da kuma yiwuwar tsawa. Ya ce za a fuskanci ruwan sama ne da rana da yamma, tsakanin Litinin 28 ga Yuli da Laraba 30 ga Yuli, 2025. Ya yi bayanin cewa duk da cewa ba a sami ruwan sama ba tukuna, yanayin da ke gaba zai iya...
Sanarwar New York ya jaddada alƙawarin kasa da kasa na kawo ƙarshen yaƙin a Gaza da aiwatar da hanyoyin samar da ƙasashe biyu Majalisar Dinkin Duniya ta sanar a cikin “Sanarwar New York” da yarjejeniyar kasa da kasa kan matakan dole da suka dace don kawo karshen yakin Gaza da aiwatar da Shirin samar da kasashe biyu da zai kai ga kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, da sake gina Gaza, da tura tawagar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya. Sanarwar karshe da taron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar kan sasanta rikicin Falasdinu cikin lumana ya sanar da amincewar kasashen duniya kan daukar matakai na bai daya don kawo karshen hare-haren wuce gona...
Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta bayyana cewa: Laifukan da aka aikata a Yammacin Kogin Jordan na Falasdinu ayyukan ta’addanci ne Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar da cewa tashe-tashen hankula da laifuffukan da tsagerun yahudawan sahayoniyya suke yi a yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye sun zama ayyukan ta’addanci, biyo bayan kashe wani mai fafutukar yaki da mamayar da tsagerun ‘yan sahayoniyya suka yi. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ya ce: “Faransa ta yi Allah-wadai da wannan kisan gilla da kakkausar murya, da kuma dukkan ayyukan ta’addanci da gangan da masu tsattsauran ra’ayi ke yi kan Falasdinawa, wanda ke karuwa a ko’ina cikin yankunan Gabar Yammacin Kogin Jordan.” Ya kara da cewa, wadannan ayyukan wuce gona da irin, hakikanin ayyukan...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗa Muhammad Fa’iz a matsayin Kwamanda Janar na farko na Hukumar Hisbah ta Jihar. Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ne ya tabbatar da naɗin ga manema labarai a Dutse. Ya bayyana cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin Gwamna Namadi na ƙarfafa ayyukan sabuwar hukumar Hisbah da inganta aikinta. A cewar sa, naɗin ya haɗa da Dr. Husaini Yusuf Baban a matsayin Babban Mataimakin Kwamanda Janar, da Lawan Danbala a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar da hedikwatar hukumar, da kuma Yunusa Idris Barau a matsayin Mataimakin Kwamanda Janar naYankin Dutse. Sauran su ne Abdulkadir Zakar, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Hadejia, da Suraja Adamu, Mataimakin Kwamanda Janar, Yankin Gumel, da...

Kwamitin Neman Sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba Ya Gabatar Da Takardar Bukatarsa Ga Majalisar Dattawa
Kwamitin neman sabuwar Karamar Hukumar Kanya Babba daga Karamar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa, ya gabatar da takardar bukatarsa ga kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da kirkiro jihohi da kananan hukumomi a zaman da aka yi a jihar Kano. A yayin mika takardar, Shugaban kwamitin kuma Hakimin Kanya Babba, Makaman Ringim, Malam Mohammed Ibrahim ya bayyana cewar wannan yunkuri ya bi duk sharuddan da kundin tsarin mulki ya shimfida don kafa sabuwar karamar hukuma. Makaman na Ringim ya kara da cewar, daukacin al’ummar yankin Kanya Babba, ciki da wajen mazabar na matukar goyon bayan hakan domin bunkasa ci gaban tattalin arziki da al’umma a yankin. Da yake karbar takardar, Shugaban kwamitin Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril,...
Shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara wanda ke jagorantar ƙasar tun daga shekarar 2011, na fuskantar suka na neman mayar da shugabancin ƙasar mutu ka raba. Wannan dai na zuwa ne bayan Ouattara mai shekaru 83 ya tabbatar da aniyar sake takara wa’adi na hudu a zaben da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba. Za mu halasta kafa ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ila ba ta cika wasu sharuɗa ba — Birtaniya Nijar da Rasha sun ƙulla yarjejeniyar makamashin nukiliya A wani takaitaccen bayani da ya yi, Ouattara ya ce takararsa ta samo asali ne daga buƙatarsa ta kiyaye zaman lafiyar ƙasa a daidai lokacin da ta ke fuskantar kalubalen tsaro da na tattalin arziki. Ya bayyana cewa, “Ni dan takara...
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta ce akwai kwamitoci guda 30 da aka daurawa nauyin bibiyar yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Jihar ke sarrafa kudade domin gudanar da harkokin yau da kullum, gami da ayyukan raya kasa. Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana hakan lokacin wata ziyarar aiki a karamar hukumar Babura. Yayi bayanin cewar, an dorawa Kwamatinsa alhakin duba kananan hukumomi domin tabbatar da shugabanci nagari a yankunan karkara. A cewarsa, kwamatin yana duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da jadawalin kudaden da karamar hukuma ke samu daga kason arzikin kasa, da littafin hulda da banki,da takardun biyan kudade na voucher da kundin bayanan...

Wani Dan Majalisar Iran Ya Yi Kira Ga A Yi Siyasar Kin Gabatar Da Bayanai A Tattaunawa Da Kasashen Turai
Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci. Haka nan kuma ya ce; Daga...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau suka bayar, tare da bin al’ada da dokokin da suka dace. A wata sanarwa da mai taimakawa na musamman kan harkokin yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce sabon Sarkin, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, shi ne ɗa na farko ga marigayi Sarki, kuma kafin naɗin nasa yana riƙe da mukamin Bunun Gusau. Alhaji Abdulkadir ya hau karagar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu. Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare da fahimtar ainihin abin da ke faruwa ba, inda ya ce hakan yana da nasaba da tuggun siyasa da son zuciya. Ya bayyana cewa maƙasudin ambaliyar sun haɗa da ruwan sama mai yawa da toshewar hanyoyin ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya shirya taron manema labaru na yau da kullum. A wajen taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da aka kulla tsakanin Amurka da kungiyar EU. A yayin da yake ba da amsa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana ba da shawarar cewa, ya kamata dukkan bangarori su warware bambance-bambancen tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tattaunawa, domin kiyaye yanayin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Bugu da kari, dangane da taron tattauna batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a kasar Sweden, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka...
Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su. Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Shugaban kungiyar Hamass ya bayyana cewa HKI da gwamnatin kasar Amurka sun janye daga tattaunawa tsakaninsu da kungiyar ne don sake komawa yaki har zuwa lokacinda zasu shafe falasdinawa a gaza. Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran ya nakalto Kkalilul Hayya, yana fadar haka a wani jawabin da aka watsa a tashoshin talabijin nay au Litinin. Alhayya ya bayyana cewa akwai ci gaba a tattaunawar tsagaiuta wuta tsakanin kungiyar da HKI da kuma Amurka, amma janyewar HKI da kuma Amurka a wannan tattaunawar wata dasisa ce don ci gaba da kissan kiyashi a gaza. Ya ce: masu shiga tsakanin sun tabbatar da cewa akwai ci gaba a tattaunawar da ake yi a doha, sai dai sun janye ne don...
Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON. Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100. Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas da tawagar kyautar dala dubu 50.
Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhinin sa kan rahotannin ambaliya mai tsanani da ta faru a Yola, Jihar Adamawa, wacce ta yi sanadiyar mutuwar mutane, da asarar dukiyoyi da kuma raba dimbin jama’a da muhallansu. A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya ce kungiyar NGF na jajantawa gwamnatin Jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayin da suke kokarin tara kayan agaji da daukar matakan rage illar wannan iftila’in. Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yaba da matakin gaggawa da ‘yan sanda da kuma dakarun sojin Najeriya suka dauka na tura rundunonin ruwa, bisa gayyatar gwamnatin jihar, domin taimaka wa al’ummar da abin ya shafa a wannan lokaci...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar a soke ko kara inganta aikin titin gina hanya mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Gabasawa. Wannan mataki ya biyo bayan karɓar rahoton da Kwamitin Majalisar kan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ya gabatar dangane da ambaliyar da ta afku a Zakirai, cikin karamar hukumar ta Gabasawa. Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin, Alhaji Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana wasu muhimman shawarwari da suka hada da: Umurtar kamfanin da ke aikin gina hanyar da ya faɗaɗa magudanar ruwa a yankin da abin ya shafa da kuma gaggauta kai agajin gaggawa ga waɗanda ambaliyar ta shafa. Sauran shawarwarin sun haɗa da tura tawagar ƙwararru daga ma’aikatun ayyuka da muhalli na jihar...
Ministan Harkokin Tsaron Ƙasa, Dakta Bello Mohammed Matawalle, ya baiwa iyalan marigayi Sarkin Gusau, Alhaji Ibrahim Bello, gudummawar naira miliyan biyar da kuma kayan abinci, bayan rasuwarsa a ranar Alhamis da ta gabata a birnin Abuja sakamakon gajeruwar rashin lafiya. Dakta Matawalle, ya bayyana alhininsa bisa wannan rashi na Mai Martaba. Baya ga gudummawar kuɗi, ministan ya kuma bada buhunan shinkafa 20, gero 10, masara 10 da kuma dawa 10 ga iyalan mamacin. Wata tawaga mai ƙarƙashin jagorancin Sanata Hassan Muhammad Nasiha, tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara a zamanin mulkin Matawalle ne suka miƙa gudummawar a madadin ministan. Dakta Matawalle ya bayyana marigayi Sarkin Gusau a matsayin shugaba mai ɗabi’a ta gari, wanda ya kasance...