Al’ummar Zamfara: ’Yan bindiga sun karɓi N56m domin izinin yin noma
Published: 7th, August 2025 GMT
Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana.
Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya biya Naira dubu 800 kafin a bar mazauna yankin su yi noma.
“Kowanne ƙauye kuma zai sake biyan Naira dubu 800, don bai wa mazauna yankin damar girbe amfanin gonakinsu, wannan ita ce yarjejeniya da muka cimma da shugaban ’yan bindiga da ke kula da wannan yanki, Ɗan Sadiya.”
“Ina magana ne game da gundumata kawai, ban san abin da mazauna wasu gundumomi suka biya wa ’yan bindigar ba a wannan shekara. Amma wani abu da nake da tabbacin shi ne mazauna yankin su biya kafin a barsu su yi noma.
“Ba mu da wani zaɓi illa mu bi umarninsa, in ba haka ba, ’yan bindiga ba za su barmu mu yi noman gonakinmu ba, a ƙalla idan muka yi noma, za mu iya samun wani abu ga iyalanmu,” in ji shi.
Sai dai Yarima ya koka da cewa, duk da biyan kuɗin noma, har yanzu ’yan bindiga sun mamaye ƙauyukansu suna sace dabbobi tare da kwashe kayan abinci.
Ya yi nadama kan yadda mazauna unguwannin da abin ya shafa suke yin amfani da duk abin da suke da shi a ƙoƙarin samun zaman lafiya da ’yan bindigar.
“Muna so mu zauna lafiya da ’yan bindigar, amma gaskiya sun karɓe mana komai, sun yi awon gaba da dabbobinmu sun kwashe kuɗinmu, amfanin noma da sauran kayayyaki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kaura Namoda Manoman gundumar Ɗan Isa Zamfara yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya.
Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi ka iya samar da kudaden shiga ga daidaikun ’yan Najeriya da ma kasar gaba daya.
NAJERIYA A YAU: Abin Da Doka Ya Ce Kan Kisan Jami’an ‘Yan Sanda DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin NajeriyaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa ’yan Najeriya basa samun cin kifi kamar yadda ya kamata.
Domin sauke shirin, latsa nan