Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba
Published: 7th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana bukatar samar da wata sabuwar hanyar yin mu’amala da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, inda ya bayyana cewa, ba a kayyade lokacin shiga wasu shawarwari da Amurka ba, ya kuma tabo batun muhimmancin dangantakar dake tsakanin Iran da kasashen Rasha, Sin da Masar.
A cikin wata sanarwa da ya aikewa gidan talabijin na Iran , Araqchi ya jaddada bukatar samar da sabon tsarin hadin gwiwa tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, yana mai nuni da cewa, abubuwan da suka faru wanda ya kai ga kaiwa kasar Iran hari bisa fakewa da rahotannin siyasa na huumar IAEA, yasa dole ne Iran ta sake sabon salon a mu’amala ada wannan hukuma.
Araghchi ya bayyana cewa, Tehran ta gayyaci mataimakin babban daraktan hukumar ta IAEA domin tattaunawa kan sabon tsarin dangantakarsu, yana mai jaddada cewa ziyarar ko alama ba za ta hada da duba cibiyoyin nukiliyar Iran ba, yana mai ishara da cewa Iran ba za ta mika kai bori ya hau ba.
Dangane da batun komawa kan teburin tattaunawa da Amurka kuwa, Araghchi ya bayyana cewa, hakan ya dogara ne da muradu da maslaha ta kasar Iran, yana mai jaddada cewa, tattaunawar wani makami ne kawai na kiyaye muradun al’ummar Iran wajen mu’amala da Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu August 7, 2025 Jamus: Shahararrun mutane fiye da 160 da ‘yan jarida sun bukaci a daina baiwa Israila makamai August 7, 2025 Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya August 7, 2025 Pezeshkian Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Yaki A Gaza August 6, 2025 Araqchi Ya Taya Larijani Murnar Zama Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran August 6, 2025 Japan: An Fara Juyayin Cikar Shekaru 80 Da Harin Amurka Na Makamin Nukiliya A Hiroshima August 6, 2025 Sudan: Dakarun RSF Sun Kashe Fararen Hula 14 Tare Da Jikkata Wasu Na Daban August 6, 2025 IRGC: Bayan yakin Kwanaki 12 Yanayi Ya Sauya Zuwa Ga Amfani Ga Iran August 6, 2025 ‘Yansanda A Iran Suna Amfani Da Kayakin Tsaro Na Zamani A Lokacin 40 August 6, 2025 Iran tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Tsakanun Kasashen Yankin August 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.
Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a mastayin babban birni.
Har ila yau kungiyar ta yi kira da a kara daukar matakan ladabtarwa kan Isra’ila tare da hukunta shugabanninta kan laifukan cin zarafin bil’adama.
Sanarwar ta soki gwamnatin Isra’ila kan yadda take ci gaba da yin watsi da dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin jin kai, tare da bayyana “mummunan cin zarafi” da ake yi wa Falasdinawa.
An fitar da wannan sanarwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun sakar diflomasiyya tsakanin kasashen dake amincewa da Falasdinu a matsayin kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya September 22, 2025 Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya September 22, 2025 Dakarun IRGC: Iran Za Ta Tarwatsa Makiya Tare Da Mayar Da Martani Kan Duk Wani Zalunci September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci