2025-08-05@11:20:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3768
«Gwamnonin Najeriya»:
Tosin Demehin ta nuna godiya da jin daɗinta, tana mai cewa wannan girmamawa daga jiharta na ƙarfafa mata gwuiwa da sauran ’yan mata masu burin taka leda a matakin duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
Gwamnatin kasar Burtaniya ta bayyana cewa zata fara amfani da wata yarjeniya da ta cimma da kasar Faransa kan maida dukkan yan gudun hijira ko bakin hauren da suke shigo kasar ta kwale-kwale zuwa kasar kasar ta Faransa. Daga yau Talata. Shafin labarai na yanar gizo Arab News ya nakalto cewa gwamnatocin biyu sun amince...
Tsohon jami’in harkokin wajen Tarayyar Turai Joesp Borrell, ya yi gargadi game da ci gaba da rashin taka rawar gani daga bangaren kasashen Turai dangane da ayyukan cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi, yana mai cewa irin wannan rashin hankali ya sa kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta zama abokiyar tarayya a cikin...
Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza. Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana...
Gwamnatin tarayya ta ce tace a shirin ta sauya wuraren dake bushe a sassan arewacin Nijeriyaza a raba naira miliyan miliyan 3.4 kuma akasarin wadanda zasu amfana da wannan za su kasance mata ta hanyar Shirin ACReSAL. Da yake jawabi a wajen bude taron kwanaki 10 na masu ruwa da tsaki kan tsarin kula...
Kungiyar masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa reshen jihar Nasarawa ta kalubalanci kungiyar tabbatar da gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari (NS-TA&G), da su tabbatar da zargin nuna son kai wajen sauke nauyin da babban Akanta Janar na jihar, Ahmed Musa Mohammed ke yi. Ko’odinetan kungiyar na jiha Abimiku...
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere. A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban...
Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle. Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu....
Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba wa ɗalibar nan ’yar shekara 17 daga Jihar Yobe da ta lashe Gasar Turanci ta Duniya, Nafisa Abdullah Aminu, kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa ta OON. Ya buƙaci a gayyato Nafisa da malamanta na harshen Turanci...

Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida a matsayin martani ga harajin Trump
Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi. Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen...
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya. Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69...
Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi da kuma takin zamani kyauta ga al’ummar mazaɓarsa. Da yake ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobin garin Goɗɗiya da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, Sanata Buba ya ce, “A bana, za mu yi allurar rigakafin dabbobi 85,000 a wannan yankin na Majalisar Dattawa.” Ya...
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan. Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin...
Hukumar Yaki da Hamada da Sauyin Yanayi ta Kasa ta kammala shirye-shiryen dasa itatuwan dabino miliyan hamsin (50,000,000) a jihohi goma sha ɗaya 11 da ke fama da fari a Najeriya. Daraktan Hukumar, Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin dasa itatuwan dabinon da aka gudanar a Dutse, babban birnin...
Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata D’Tigress kyautar Dala dubu 100 da gidaje da lambar girmamawa ta OON, a matsayin karramawa bayan lashe kofin gasar ta bana. Shugaban ya kuma ba masu horar da ’yan wasan dala 50,000 kowannensu. Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin...
Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da ta kafa domin gano haƙiƙanin gaskiya kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Ali Namadi da shiga sha’anin belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. Shugaban kwamitin, Barista Aminu Hussain, ne ya miƙa rahoton ga Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk...
Rundunar sojin kasar Sin (PLA) ta yi sintiri a yankin tekun kudancin Sin daga ranar 3 zuwa 4 ga wata. Kakakin rundunar PLA ta kudancin kasar Tian Junli ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne biyo bayan matakan Philippines na sanya kasashen dake wajen yankin cikin abun da ta kira...
An nemi wata jaririya sa’o’i kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu...
An nemi wata jaririya saoi kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu...
Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin...
An nemi wani jariri sabuwar haihuwa an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririn ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarsa da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu ruwan sama...
Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe. Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun...
Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da tsawa na kwaki uku a faɗin ƙasar daga ranar Litinin. NiMet ta fitar da wannan hasashen ne ranar Lahadi a Abuja, lamarin da ke ƙara barazanar ambaliya a wasu jihohin ƙasar. Shirin kashe N712bn kan...
Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri. Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a...
Akalla mutane 11 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwannin Kagara da San-Isa da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara. Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa an kai hare-haren ne a unguwannin Kagara da San-Isa tare da wasu kauyukan da ke kewaye. Waɗanne Ƙasashe Ne...
Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka. Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi. Ƴan wasan...
Majalisar zartaswar jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da kashe kudade wajen ayyuka a sassa daban daban nufin tabbatar da amana da aka dora wa gwamnati. Da yake karin haske ga manema labarai yayin taron da ya saba gudanarwa, kwamishinan yada labarai Alh. Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta...
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa. Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau,...
ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa. Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan...
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani kakkausar gargadi kan matsalar ruwan sha da ke kara kamari a zirin Gaza, inda ta bayyana cewa yunwa na ci gaba da rataya a kan al’ummar da ke kara hana samun tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli. A cikin wani sabon rahoto, MDD ta ce kashi 96% na...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ga alama kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu a fafutukar da ake yi ta ganin iyaye mata sun shayar da jariransu nono zalla a wata shida na farko. Rahotanni sun ce duk da daɗewar da aka yi ana wayar da kai har yanzu matan da suke shayar da...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al’umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana. Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji...

Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Bayyana Cewa: Masu Shirin Halaka Gaza Suna Son Mamaye Duniyar Musulmi Ne
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Masu shirin halaka Gaza suna neman hadiye duniyar Musulunci ne Dakarun kare juyin juya halin Musulunci nanIran sun yi gargadin cewa; Bangarorin da ke shirya kisan kiyashi a Gaza ba wai kawai halakar al’ummar Falastinu ba ne kawai, a’a suna neman mamaye yankuna masu...
A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki. Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP). Ya ce: “Kwarewa...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da babban shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar a shekarar 2025. An fara dashen ne yankin Yanbawa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda. Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Gwamnan ya ce wannan shiri na nufin...
Ma’aikatan agajin gaggawa a lardin Hebei na arewacin kasar Sin da ambaliya ta aukawa, sun karfafa kokarin gyara tituna da gadojin da suka lalace, domin tabbatar da isar da kayayyakin agaji da na aikin ceto ba tare da tangarda ba. Ruwan sama dake ci gaba da sauka a kwanakin baya-bayan nan ya haifar da ambaliya...
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Najeriya. El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya. Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka...
Gargaɗin ya yi daidai da irin wannan sanarwar da ofisoshin jakadancin Amurka a Jamaica da Uganda suka fitar kwanan nan, a wani ɓangare na yaƙi da dabi’ar karya ƙa’ida shige da fice. A cikin watan Janairun 2025, hukumomin Amurka sun sake jaddada aniyarsu na ƙarfafa ikon kula da iyakoki kan yin amfani da damar zama...
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗa Hon. Ismaila Ahmed Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi, bayan rasuwar Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Kaji. Sabon Sarkin na Gudi, Ismaila Ahmed Gadaka, ya shahara da ƙwarewa a fannoni da dama. Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba Ma’aikatan jinya sun...
Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya...
Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa. Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana...
Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka...
“daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi. Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba....
Ya danganta mutuwar ta ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, kan rashin samun rancen kudaɗen da za su ci gaba da ka kasuwancin su da rashin kayan aiki, da rashin kasuwa da ba a samu sosai da kuma rashin gudanar da ingantaccen shiri, kafin su fara gudanar da kasuwancinsu. Ya sanar da cewa, ya zama...
Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’,...
Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta ce Gwamnatin Tarayya ta yi sakaci game da ɓacewar ɗan gwagwarmaya Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata. A wata sanarwa da ta fitar, Amnesty, ta ce abin takaici ne ganin cewa shekara shida kenan da Dadiyata ya ɓace ba tare da wani sahihin bayani...
“Kazalika sarkin ya bayyana cewa, mun kuma duba yanayinmu. Me muke da shi? Me za mu iya yi? Me ya kamata mu yi domin inganta rayuwar mutanenmu? Allah ya albarkaci ƙasarmu, ƙasa ce mai faɗi sosai, kuma ta dace da ayyukan noma. Mun kuma yi la’akari da fannin ilimi. Jihar Neja, an san tana gaba...
Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake...