2025-09-17@23:24:29 GMT
إجمالي نتائج البحث: 400

«Satar jarabawa»:

    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.  ...
    JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata . Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa  wannan...
    Jami’an kasashen larabawa da na Musulmi sun bukaci daukar kwararan matakai kan Isra’ila bayan harin da ta kai a birnin Doha, inda suka bayyana harin a matsayin “na matsorata, da muggan laifuka.” Da yake jawabi a gun taron ministocin harkokin wajen kasashen a birnin Doha, Sakatare-Janar na kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi kakkausar suka ga harin da Isra’ila ta kai kan Qatar a baya-bayan nan, inda ta bukaci kasashen Larabawa da na musulmi da su dauki matsaya daya kan matakan wuce gona da iri na gwamnatin mamayar. Basem Naim, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Hamas,ne  ya yi wannan kiran...
    Rahotanni sun bayyana cewa an fara taron ministocin harkokin wajen kasashen larabawa da na musulmi a birnin Doha na kasar Qatar, domin share fage na taron shuwagabannin kasashen da zaa yi gobe litinin in mai duka ya kaimu , domin tattaunawa kan harin baya bayan nan da Isra’ila ta kai Qatar, Taron zai tantance matakin...
    Lawal ya ƙara da cewa, ɗaukacin guraren da Jiragen Ruwa ke tsaya, akwai launin da kuma lamba da aka amince,manyan motocin za su rinƙa yin amfani da su, domin yin zirga-zirga  a Tashar ta Apapa. “Misali, a APMT, manyan motocin za su rinƙa yin amfani da lamba  001 mai ɗauke launin ruwan bula, inda kuma...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai halarci babban taron kasashen musulmi da na  Larabawa da za a yi a Doha a ranakun Lahadi da Litinin, taron da Qatar ta kira domin samar da tallafi ga Falasdinawa a Gaza da kuma mayar da martani kan harin da Isra’ila ta kai kan babban birnin kasar a ranar...
    Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran ya gargadi kasashen Larabawa game da harin da gwamnatin mamayart Isra’ila ke kaiwa kan kasashe Limamin da ya jagoranci Sallar Juma’a a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami, ya gargadi gwamnatocin kasashen Masar, Jordan, Bahrain da Saudiyya cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila za...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sheikh Naim Qassem ya bayyana cewa idan kasashen Larabawa ba su goyi bayan ‘yan gwagwarmaya ba, to su ma za su fuskantar hare-haren Isra’ila” A jawabinsa babban sakataren kungiyar ta Lebanon ya bayyana cewa gwamnatin Isra’ila da Amurka suna aikata munanan laifuka a zirin Gaza da kuma yammacin...
    Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ya bayyana cewa ba za a fara aiwatar da shirin cire harajin man fetur na kashi 5 cikin 100 ba nan take. Ministan ya fadi  hakan ne a ranar Talata a wani taron manema labarai a ofishinsa da ke Abuja. Ministan ya kuma ce ba za a...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Dole ne kasashen musulmi da na Larabawa su yi Allah wadai da yin tir da harin wuce gona da iri da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kai kan kasar Qatar Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga ‘yan uwanta na kasar Qatar, yana...
    An samu damar tattauna muhimman abubuwa a babban taron kamar hanyoyin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara na Nijeriya da kuma yankin Bungoma na ƙasar Kenya.   Manyan mambobin kwamitin sun tattauna damarmakin zuba jari a jihohin Ogun da Zamfara a Nijeriya yankin Bungoma na Kenya. A jawabin sa ga masu zuba hannun...
    Kasashen larabawa da kungiyoyin kasa da kasa da wasu kasashen duniya sun yi tir da hare-haren da HKI ta kai kan birnin Doha babban birnin Qatar a kokarinta na kashe shuwagabannin kungiyar Hamasa a yau Talata. Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa babban sakataren MDD Antonio Gotterre ya yi tir da...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta yi watsi da abinda yazo cikin bayanin bayan taro na kungiyar kasashen Larabawa na cewa tsiran Abu Musa da Tumb babba da karami mallakin UAE ne. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan Tehran na fada a cikin bayanin da...
    Ya yi nuni da cewa, dokar za ta bukaci umarnin fara aiki daga ministan kudi kamun a fara.   Edun ya ce, dole ne gwamnati ta zauna tare da masu ruwa da tsaki domin wayar da kan jama’a kafin aiwatar da wannan sabuwar dokar harajin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC).   Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu...
    Tawagar kasar Iran ta maza da mata a wasan wushu a bangaren sanda da taolu ta samu gagarumar nasara inda ta samu lambobin yabo guda guda 10, zinariya 6 Azurfa guda 2 sai kuma tagulla guda 2, a wasan zakarun na washu karo na 17 da aka gudanar a kasar brazil, Gasar Wushu ta duniya...
    Jam’iyyar APC reshen Jihar Jigawa ta gargaɗi mambobinta da su guji aikata rashin ladabi da halayen da ba su dace ba da za su iya kawo rabuwar kai a cikin jam’iyyar. A cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar na jiha, Muhammad Dikuma Umar ya sanya wa hannu, APC ta nuna damuwa kan abin da ta...
    Jakadan kasar Iran a hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya  Redha Najafi ya bayyana cewa Iran da hukumar nukiliya ta duniya sun koma teburin tattaunawa game da shirin nukiliya iran na zaman lafiya domin duba hanyoyin da zaa bi domin ci gaba da aiki tare, Yace iran ta bar kofa a bude domin tabbatarwa...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta sake jaddada haramcin hawa babura daga ƙarfe 7 na dare zuwa 6 na safe, a wani mataki na tsaurara tsaro yayin bikin Mauludi a jihar. Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Bello Yahaya, ya bayyana cewa dokar na da muhimmanci domin hana aikata...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya zargi jam’iyyun adawa da jan APC cikin harkokin siyasa kafin lokacin zaɓen 2027. Sai dai ya ce ba zai bari hakan ya karkatar da hankalinsa daga shugabantar Najeriya ba. NAJERIYA A YAU: Hare-hare Kan Tarurrukan Siyasa Da Alakarsu da 2027 Za a koma rubuta jarabawar WAEC a komfuta Yayin da...
    Gwamnatin Nijeriya ta bayyana goyon bayanta kan shirin mayar da rubuta Jarabawar Kammala Sakandare ta Yammacin Afirka (WAEC) da komfuta wato CBT daga shekarar 2026. Wannan babban sauyin, wanda aka tsara cewa zai fara aiki a shekarar 2026 ya jawo mabambantan ra’ayoyi a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ilimi. An kama wata uwa...
      Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata.   A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yammacin Turai sun fara amfani da takunkumi kan kasar Iran bisa umarnin  ‘yan sahayoniyya da Amurka Dangane da matakin da kungiyar gungun Turai ta dauka na son sake dawo da takunkumin da ya shude kan kasar Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana...
    Kungiyar Zabarmawa ta Najeriya ta karrama Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, da sarautar Garkuwan Zabarmawa, saboda gudummawar da ya bayar wajen ci gaban al’umma da tallafa wa ƙungiya. Da yake bayyana dalilin bai wa gwamnan sarautar a madadin shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sarkin Zabarmawa, Alhaji Bello Zabarmawa, ya ce: “An ba da wannan sarauta...
    Hukumar bada agaji ta MDD mai kula da Falasdinawa UNRWA ta bayyana cewa yara fiye da 660,000 a gaza aka haramtawa karatu a wannan shekarar saboda yakin da HKI ta dorawa yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Philippe Lazzarini shugaban hukumar UNRWA yana fadar haka a wani sakon da ya...
    Sakatare-Janar na Majalisar Hadin Kan Kasashen yankin tekun Farisa ya  bayyana batun kafa Isra’ila babba a matsayin Baban hadari da ke barazana ga dukkanin kasashen larabawa. A wata hira da jaridar Al-Qabas ta Kuwaiti, Jassim Mohammed Al-Budaiwi ya fada a wannan  Lahadin  cewa, kasashe mambobin kungiyar (GCC) sun yi watsi da duk wani buri na...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A wannan makon ne aka bude damar tattauna na kowa da kowa a kasar Guinea dangane da zaben raba gardama na sabon kundin tsarin mulkin kasar. Shafin yanar gizo na labarai Africa News ya bayyana cewa gwamnatin rikon kwarya na kasar ya bayyana cewa tattaunawa kan sabon kundin tsarin mulkin kasar zai gudana ne a...
      Kungiyar AMA Foundation, tare da hadin gwiwar Kwalejin Gwamnatin Tarayya FGC Kaduna, sun hada karfi da karfe wajen ilmantar da marayu a jihar Kaduna.   Ta wannan hadin gwiwa, marayu da suka kammala makarantar firamare a Hauwa’u Memorial School, wadda AMA Foundation ta kafa a Tudun Wada, Kaduna, suna samun damar shiga Makarantar Sakandare...
    Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar Jigawa Alhaji Aminu Zakari, yace ziyarar kwamatin a kananan hukumomin jihar 27 tana bada damar ganawa kai tsaye a tsakanin masu ruwa da tsaki domin karfafa dabi’ar aiki tare da juna da kuma kyautata alaka a tsakanin bangarori daban daban. Ya yi wannan tsokaci ne lokacin da...
    “Na zo Banga domin jajanta muku bisa wannan mummunan hari. Lokacin da abin ya faru bana nan, sai na umarci mataimakina ya jagoranci tawaga ta musamman domin yi muku ta’aziyya. “Na dawo Gusau jiya, kuma abu na farko da na fifita yau shi ne zuwa nan da kaina. Gwamnati za ta ƙara ƙoƙari wajen yaƙar...
    An yi kira ga kwararrun kafafen yada labarai da su tabbatar da madogararsu domin tabbatar da samar da kyakykyawan rahoton abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.   Babban Limamin Masallacin Al-Waheed Central, Imam Mustapha Luqman ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wajen taron hadin gwiwa da kungiyar ‘yan jarida...
    Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya ba da shawarar gudanar da taron kasashen Larabawan yankin tekun Pasha da Iraki da kuma Iran Ministan harkokin wajen kasar Iraki Fuad Hussein ya gabatar da shawarar gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Iraki, Iran, da kuma kasashen larabawan yankin Gulf, a tsarin na 6+2, a gefen taron...
    Wata kotu a kasar Chadi ta daure tsohun firai ministan kasar Succes Masra shekaru 20 a gidan kaso da taran caifa biliyon guda a jiya Asabar. Shafin yanar gizo na Labarai Afrika Newas ya kara da cewa kotun ta tabbatar da laifin kan dan siyasar, kuma dan adawa da gwamnatinn Debi, da laifin watsa wasu...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar.   Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai...
    Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince ta bada sama da naira miliyan 156 domin sayen tikitin jirgi na mayar da daliban jihar masu karatun likita har su 184 da suka kammala hutun su a gida zuwa makaranta a kasar Cyprus. Shugaban Hukumar Bada Tallafin Karatu ta Jihar, Alhaji Saidu Magaji, ya bayyana hakan ga manema labarai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke...
    Kudirin gyaran dokar  fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji...
    Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan. Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje...
    Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na...
    Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin...
    Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe.   Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa...
    Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza ba Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta bayyana cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila sun boye kusan kashi 88% na binciken laifukan yaki ko cin zarafin da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata...
    Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’,...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na bada managartan shawarwari da za su yi wa kananan hukumomin jihar jagoranci wajen gudanar da ayyukan su kamar yadda yakamata. Shugaban Kwamatin Kananan Hukumomi na Majalisar, Alhaji Aminu Zakari, ya bada wannan tabbacin lokacin rangadin kwamatin majalisar a sakatariyar karamar hukumar Birniwa. Alhaji Aminu Zakari Wanda...
    Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Jihar Katsina ta kori ɗalibanta 57 kan laifin satar jarabawa. Hukumar gudanarwar jami’ar ta kuma dakatar da wasu dalibai biyar na tsawon shekara guda tare da ba wasu biyu takardar gargaɗi kan aikata laifukan jarabawa. A safiyar Asabar kakakin jami’ar, Hajiya Fatima Sanda, ta sanar da cewa majalisar jami’ar...
    Bincike a kan zargin da ake wa Hukumar Raya ƙasashe ta Amurka (USAID) da wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida da na ƙasa da ƙasa game da tallafa wa ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP da sauran masu tayar da ƙayar baya a Nijeriya har yanzu bai kammala ba. Kawo yanzu babu wata ƙwaƙƙwarar...
    Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Al-Husi wanda ya gabatar da jawabi a jiya  Alhamis, ya bayyana abinda yake faruwa a Gaza da cewa, yana nuni da halayyar keta da mugunta ta ‘yan sahayoniya, don haka ya zama wajibi akan al’ummar musulmi da dukkanin jinsin bil’adama da su kalubalanci wannan irin zalunci da ba shi da...