Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano
Published: 8th, August 2025 GMT
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.
Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta bayyana Sadiq a matsayin jarumi, ƙwararre, kuma mai kishin kasa a fannin kafafen sada zumunta.
Gwamna Abba ya ce mutuwar Sadiq Gentle ta girgiza shi sosai, inda ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai kamun kai, haƙuri, da sadaukarwa ga ci gaban Jihar Kano.
Gwamnan ya bayyana kisan da aka yi masa a matsayin keta haddin bil’adama da ba za a lamunta ba, lamarin da bayyana a matsayin ƙoƙarin da wasu bata-gari ke yi domin kawo cikas a zaman lafiya a jihar.
Ya umarci hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike, tare da tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan aika-aikar sun fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci irin wannan ta’asa ba, yana mai bayyana bukatar tsauraran matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Kazalika, Gwamnan ya mika ta’aziyya ga iyalan marigayin, abokan aikinsa, da daukacin jami’an Ma’aikatan Tarihi da Al’adu, yana mai tabbatar musu da cewa Gwamnatin Kano na tare da su a wannan lokaci na jimami da baƙin ciki.
Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne wasu da ake zargi ’yan daba ne suka sassari hadimin gwamnan yayin wani farmaki da suka kai masa har gida da adduna.
Daga bisani an garzaya da Sadiq Gentle Asibitin Murtala da ke birnin Kano inda a nan ajali ya katse masa hanzari.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara
Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.
An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu matsalar tayar motar a kusa da unguwar.
‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun SoworeA yayin da suke ƙoƙarin gyaran tayar ne wasu ’yan bindiga biyar suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta.
Waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu a harin, an bayyana sunayen su da: Alhaji Abdulrazak Ewenla ɗan ƙauyen Ajia da Jimoh Audu daga Gammu.
Mutanen ukun da aka sace sun haɗa da: Kazeem Ajide da Wahidi da Mufutau, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da sunayen mutanen biyu ba.
Bayan afkuwar lamarin, an tura tawagar jami’an ’yan sanda da sojoji da ’yan banga zuwa wurin da lamarin ya afku don tabbatar da tsaro tare da dawo da zaman lafiya.
Rundunar ’yan sandan jihar a cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Adetoun Ejire-Adeymi ya fitar a ranar Alhamis, ta tabbatar da faruwar harin.
Sai dai ta yi watsi da wani faifan bidiyo da ke nuna cewa mazauna ƙauyen sun tsere, lamarin da ya haifar da tunanin an ƙauracewa garin.