Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara
Published: 9th, August 2025 GMT
Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa, an fara gurfanar da Kalthum a ranar 13 ga watan Mayu, 2024.
Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Fashewar gurneti ya kashe yara uku a BornoAna tuhumarta da karɓar kuɗi Naira miliyan 1.
Sai dai ba ta kawo kayan ba kuma ba ta mayar musu da kuɗinsu ba.
A lokacin shari’ar, lauyoyin masu shigar da ƙara, Mukhtar Ali Ahmed da Faruku Muhammad, sun gabatar da shaidu da hujjoji.
Mai shari’a ta kuma bai wa Kalthum zaɓin biya tara ta Naira 50,000 maimakon zaman watanni shida a gidan gyaran hali.
Bugu da ƙari, kotun ta umarce ta da ta biya Naira 635,000 a matsayin diyya ga waɗanda ta damfara.
Idan kuma ta gaza biyan diyyar, za ta ƙara fuskantar ɗaurin shekaru biyu a kan waɗanda aka yi mata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Damfara diyya ɗauri Tara
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokokin Yawon Buɗe Ido da Zartar da Shari’a
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokoki guda biyu masu muhimmanci da nufin ƙarfafa harkar yawon buɗe ido da hanzarta gudanar da shari’a a faɗin jihar.
Shugaban majalisar, Yusuf Dahiru Liman, ne ya sanar da amincewar majalisar yayin zaman, ta wanda aka gudanar a harabar majalisar da ke Kaduna.
Dokar farko mai taken “Dokar Kafa Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido, Gidajen Tarihi, Shata Wurare, Lambuna da Wuraren Hutu na Jihar Kaduna, 2024”, na da nufin bunƙasa harkar yawon buɗe ido da raya al’adu a jihar.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Yusuf Dahiru Liman
Da yake gabatar da rahoton kwamitin, Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Harkokin Fasaha, Shari’a da Ilimi, Magaji Suleiman, ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da cikakken bincike kan kudirin kuma ya fahimci cewa yana da amfani wajen haɓaka yawon buɗe ido da al’adu.
Magaji Suleiman ya ce idan aka fara aiki da hukumar, za ta inganta shata wurare, lambuna da wuraren shakatawa a jihar, wanda hakan zai ja hankalin masu zuba jari daga cikin gida da waje.
A nasa jawabin, wanda ya dauki nauyin gabatar da kudirin, Mr. Henry Marah, ya bayyana cewa hukumar za ta taka rawa wajen farfaɗo da al’adun gargajiya na jihar Kaduna wacce ke da yawan kabilu daban daban.
Ya ƙara da cewa dokar za ta taimaka wajen samar da kuɗaɗen shiga ga jihar, ƙirƙiro guraben ayyukan yi ga matasa da kuma cusa tarbiyar al’adu ga matasa masu tasowa.
Barista Emmanuel Kantiyok
Har ila yau, Majalisar ta kuma amince da gyara dokar gudanar da shari’ar laifuka ta Jihar Kaduna ta shekarar 2017.
Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar, Barista Emmanuel Kantiyok, ya bayyana cewa gyaran dokar zai taimaka wajen gudanar da shari’a a kan lokaci da kuma tabbatar da adalci ba tare da la’akari da matsayin mutum ba.
Barista Kantiyok ya ce gyaran dokar zai taimaka wajen rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma ƙara wa talakawa kwarin gwiwa ga tsarin shari’a.
Majalisar ta amince da dokokin ne ta hanyar ƙuri’ar murya da ‘yan majalisar suka kada, karkashin jagorancin Shugaban Majalisar, Yusuf Dahiru Liman.
Daga ƙarshe, majalisar ta tafi hutu kuma za ta dawo zaman ta a ranar 9 ga Satumba, 2025.
Shamsuddeen Mannir Atiku