An kashe mutum 24 an sace 144 a mako guda a Zamfara — Rahoto
Published: 11th, August 2025 GMT
’Yan ta’adda sun kashe mutum 24 tare da sace wasu akalla 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara.
Kungiyar Al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hare-haren da suka kai kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban.
Ta bayyana cewa daga ranar 4 zuwa 10 ga watan nan na Agusta, 2025 ’yan ta’adda suka kai hare haren; kauyukan da aka kai wa farmakin sun hada da Sabe, Tungar Yamma, Sauru, Lambasu, Dogon Madacci, Dankalgo, da Kwanar Kalgo a ƙaramar hukumar Bakura.
A Karamar Hukumar Tsafe, hare-haren sun shafi Chediya, Kucheri, Yankuzo, da Katangar Gabas Bilbils.
A Karamar hukumar Mafara, an samu rahoton hare-hare a Tabkin Rama, Matsafa, da Ruwan Gizo, yayin da Rafin Jema a Gummi da ƙauyukan Adabka da Masu a Bukkuyum suma suka fuskanci hari.
Kungiyar ta jaddada cewa ci gaba da kai hare-hare yana nuna bukatar gaggawa ta ƙarfafa matakan tsaro domin kare al’ummomin karkara daga hannun ‘yan bindiga da ke addabar jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane hare hare Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Neman Daukar Karin Matakin Kawar Da Shingayen Dake Hana ‘Ya’ya Mata Zuwa Makaranta A Zamfara
Mahalarta taron masu ruwa da tsaki na yini daya don tabbatar da sakamakon bincike kan al’amuran zamantakewa da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar Zamfara, sun bukaci iyaye, shugabannin al’umma, da gwamnati a dukkan matakai da su magance matsalolin da ke hana yara mata zuwa kammala karatun sakandare.
Kungiyar AGILE da ke Jihar Zamfara tare da hadin gwiwar Media and Publicity Consult ta shirya taron masu ruwa da tsaki na rana daya domin tabbatar da sakamakon binciken da aka yi kan ka’idojin zamantakewa da ke kawo cikas ga ’yan mata matasa da ke hana shiga makarantun gaba da sakandare a jihar Zamfara.
Da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Abubakar Aliyu Liman na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su samar da yanayi mai kyau da zai karfafa gwiwar ‘ya’ya mata su ci gaba da karatu.
Farfesa Liman, wanda kuma shi ne babban mai ba da shawara kan aikin bincike na AGILE a Zamfara, ya bayyana cewa auren dole da rashin goyon bayan iyaye a matsayin wasu manyan matsalolin da suka shafi ilimin ‘ya’ya mata a jihar.
Wakilan Ma’aikatun Mata da Ilimi na Jihar Zamfara sun yaba da tasirin aikin AGILE a Zamfara tare da yin kira da a ci gaba da inganta ayyukan da suka hada da samar da ingantattun hanyoyin ruwa, tsaftar muhalli a makarantu.
Mataimakin kodinetan hukumar AGILE a jihar Zamfara, Dakta Salisu Dalhatu, ya bayyana cewa an kammala makarantu 317 daga cikin 440 da aka ware domin gyarawa a karkashin hukumar ta AGILE, yayin da sama da ‘yan mata 8,000 ke cin gajiyar shirin bayar da tallafin kudi.
Manajan Daraktan yada labarai da tuntuba (MPC), Malam Nasiru Usman Biyabiki, ya ce taron tabbatar da shi an yi shi ne da nufin tace sakamakon binciken don samun ingantacciyar hanyar shiga tsakani.
A cewarsa, gangamin wayar da kan jama’a ya taimaka wajen ganin jihar Zamfara ta kasance cikin jerin jahohi biyar da suka fi aiwatar da ayyukan AGILE a fadin kasar nan.
Taron wanda MPC ta kira, ya kuma yi nazari kan sakamakon da Daraktar ICT ta kungiyar, Hibban Buhari ta gabatar, wanda ya bayyana talauci, al’adu, auren dole, da rashin ingantaccen tsarin karatu a matsayin manyan abubuwan da ke kawo tarnaki ga ‘ya’ya mata da kuma rike su.
Binciken ya ba da shawarar yin amfani da harsunan Hausa, Fulfulde, da Larabci wajen kamfen na wayar da kan jama’a, inda rediyon ya zama cibiyar farko saboda yawan isar da sako.
AMINU DALHATU.Gusau