Aminiya:
2025-11-27@22:28:35 GMT

Sojoji sun kama wasu kan zargin kitsa juyin mulki a Mali

Published: 11th, August 2025 GMT

Rahotanni daga sojojin da ke mulki a Mali, sun ce sun kama wasu sojoji kusan 30 da ake zargin suna shirin kifar da gwamnati ƙasar.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa cikin waɗanda aka kama akwai Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti da ke tsakiyar ƙasar.

Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo 

Har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba game da lamarin.

Ita ma gwamnatin da ke mulki yanzu ta karɓi mulki ne ta hanyar juyin mulki a shekarar 2021.

Wannan zargi ya ƙara nuna cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tsakanin gwamnatin sojin.

Yanzu haka dai gwamnatin na fuskantar matsalar hare-haren masu iƙirarin jihadi a Arewacin Mali.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hare hare zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa

Daga Salihu Tsibiri

Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga  siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.

Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki.

Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas.

Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa su ma gwamnoni suna da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gwamnatin tarayya, lokaci ya yi da za a duba batun tsaro a matsayin barazana da ba ta da alaƙa da jam’iyya, addini ko ƙabila.

Ya kara da cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba da ta’azzara, akwai bukatar a rufe majalisa gaba ɗaya tare da ayyana dokar ta-baci, har sai an ɗauki matakin gaggawa don kare ƙasar daga halin da take ciki.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ’yan sanda, Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, inda ya yaba wa umarnin shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga wasu manyan mutane domin ƙara ƙarfi a yaki da laifuka a fadin ƙasar.

Sai dai Makki Yalleman ya yi kira da a samar da isasshen kuɗi da na’urorin zamani domin inganta ƙwarin gwiwa da ƙwarewar rundunar ’yan sandan Najeriya a yakin da take yi da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ’yan bindiga.

A nasa bangaren, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya danganta matsalolin tsaro da ake fuskanta ga gazawar bangarorin gwamnati uku wajen tabbatar da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, musamman kan ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da kuma masu yi wa gwamnati tawaye.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ECOWAS ta yi Allah wadai da juyin mulki a Guinea Bissau
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina