Afrika Ba Ta Cikin Jerin Fannonin Da Muke Ba Fifiko – Amurka
Published: 9th, August 2025 GMT
Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu ƙasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban ƙasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alaƙar tarihi tsakanin ƙasar Laberiya da Amurka.
A hakika, rashin mutuntawa da shugaba Trump ya nuna a fili, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa wajen ganawar, ba domin neman ƙarfafa dangantaka ba ne, sai dai don tabbatar wa Amurka ɗin damar samun ma’adanan da take buƙata, da yiwuwar sanya waɗannan ƙasashen dake nahiyar Afirka amincewa da karɓar baƙin haure da ake korarsu daga Amurka.
Wataƙila, shugaba Trump ba ya mai da hankali sosai kan ɗa’a a fannin diflomasiyya, amma idan aka kwatanta da shugabannin ƙasar Amurka da suka gabace shi, to, a ƙalla yana bayyana komai a fili ba tare da rufa-rufa ba.
Maganarsa da matakan da ya ɗauka, dukkansu na isar da saƙo zuwa ga ƙasashen Afirka cewa: “Ba ku cikin jerin fannonin da Amurka take nunawa fifiko.”
“Za mu iya musayar wasu abubuwa, amma kada ku yi tsammanin za ku samu riba ko alfanu sosai.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya sake naɗa Buba Marwa a matsayin shugaban NDLEA
Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Birgediya-Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya) a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Bayo Onanuga, Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labaru, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma’a.
An kama ’yan Najeriya 3 a Kenya kan zargin aikata damfara Majalisar Wakilai ta dage lokacin fara yin jarabawar WAEC a kwamfuta zuwa 2030An fara nada Marwa a watan Janairu 2021 ta hannun
Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ne ya fara naɗa Buba Marwa a muƙamin a watan Janairun 2021, bayan ya jagoranci Kwamitin Shugaban Kasa na Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi daga shekarar 2018 zuwa Disamba 2020.
Sabon nadin na nufin tsohon hafsan soja dan asalin jihar Adamawa zai ci gaba da rike mukamin har zuwa shekarar 2031.
Marwa, wanda ya taba zama gwamnan soja na jihohin Legas da Borno, ya kammala karatu a Makarantar Soja ta Najeriya da kuma Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA).
Bayan ya zama cikakken soja a shekarar 1973, Marwa ya yi aiki a matsayin babban jami’in 23 Armoured Brigade, ya kasance babban dogari ga tsohon Babban Hafsan Soja, Laftanar-Janar Theophilus Danjuma, sannan ya yi aiki a matsayin Magatakardar Kwalejin Tsaro ta Najeriya.
Haka kuma ya yi aiki a matsayin Mataimakin Mashawarci kan Tsaro a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Washington DC, daga baya kuma ya zama Mashawarci kan Tsaro a Ofishin Jakadan Najeriya na Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya.
Zaman Marwa a NDLEA ya yi fice wajen kama masu fataucin miyagun kwayoyi, inda aka cafke sama da mutane 73,000 da ke harkar fatauci da kuma kwace fiye da tan miliyan 15 na miyagun kwayoyi iri-iri.
A karkashin jagorancinsa, hukumar ta kaddamar da gangamin yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a faɗin Najeriya.
Shugaba Tinubu ya ce: “Sake nadinka alamar amincewa ce da kokarinka na kawar da kasar nan daga annobar fatauci da shan miyagun kwayoyi. Ina rokonka kada ka yi kasa a gwiwa wajen bin diddigin ’yan kasuwar miyagun kwayoyi da ke neman lalata al’ummarmu, musamman matasa.”