Aminiya:
2025-09-24@09:57:06 GMT

An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato

Published: 7th, August 2025 GMT

’Yan bindiga ɗauke da makamai sun shiga ƙauyen Bimasa a Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato sun kashe mutum huɗu sun jikkata wasu da dama a daren ranar Laraba.

Ɗaya daga cikin jagorori a ƙauyen ya yi wa Aminiya ƙarin bayani ya ce, a daren ranar Laraba da ƙarfe 12:40 na tsakar dare ɓarayi suka shigo ƙauyen akan babura suna da yawa sun fi mutum 10 a nan take suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi kai tsaye suka harbe mutum biyar, huɗu suka rasu an kai ɗaya asibiti.

’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara

“A haka suka rika harbi ta ko’ina, sun buge shagunan mutane suka kwashe wayoyi a wurin masu caji, shagunan da ke sayar da abinci suka saci abinci da yawa, a lokacin ba su yi garkuwa da kowa ba, suka tafi abinsu.”

Ya ce, a dukkan Ƙaramar hukumar ’yan bindigar sun matsa musu kan haka a yanzu sama da gari 17 duk sun tashi sun dawo cikin hedikwatar Ƙaramar hukumar ta Tureta a Kudu da Arewa duk an bar noma domin tsoron ’yan bindigar kana zuwa gona ana sace ka.

” A yanzu garin Kwarare da Gidan Batare da Kaura da Galadimawa, Ci da sha da Rafin gora da Kuruwa Birni, Dantayawa da sauransu, ba kowa ‘yan bindiga ke yadda suke so a wuraren.”.

Ya roƙi shugaban Ƙaramar hukuma da su yi wata hoɓɓasa da jami’an tsaro don ganin an samu sauƙi musamman mutane na yin noma.

A kullum mutanen yankin cikin fargaba suke ta ‘yan bindiga, abin tausayi da zaran Magrib ta doso mutane za su fara barin gidajensu zuwa wani wurin ɓoyo don kawai su tsira daga harin ’yan bindiga, koyaushe haka ake ya kamata gwamnati ta yi wani abu a lamarin.

Wata majiyar ta ce, sun kashe mutane huɗu, amma sun jikkata mutane sun fi 20 wasu na asibitin Tureta wasu na gida suna jinya.

Ya ce, shugaban ƙaramar hukumar Honarabul Abubakar Aliyu Tureta ya jajanta masu kan halin da ya same su tare da alkawarin tallafawa waɗanda suka samu rauni a harin.

Wakilinmu ya tuntuɓi shugaban Ƙaramar hukumar Tureta kan lamarin, amma ba a samu magana da shi ba domin ba ya kusa da waya a lokacin da aka kira shi kuma bai mayar da amsar saƙon da aka tura masa ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sakkwato Ƙaramar hukumar yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Kama Mutum 4,383, Sun Ceto 1,138 Daga Hannun Mahara Cikin Wata 3

A cewarsa, shugabancin rundunar ya ƙuduri aniyar amfani da dabaru wajen samar da tsaro, ƙwarewar aiki, da ƙarfafa zumunci da al’umma domin rage laifuka a faɗin ƙasar nan.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Yansanda Sun Kama Mutum 4,383, Sun Ceto 1,138 Daga Hannun Mahara Cikin Wata 3
  • Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • ’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi
  • Bayan Sulhu  Da Ƴan Bindiga, An Saki Mutane 70 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Katsina
  • Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina
  • An kashe jami’an tsaro 53 a cikin mako biyu —Bincike
  • Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi
  • Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe
  • Wata Mahanga Ta Daban Ta Kallon Ayyukan Ta’addanci