Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan
Published: 10th, August 2025 GMT
Yayin ziyararsa a kasar Indiya kwanan nan, shugaban kasar Philippines ya bayyana cewa, idan Sin da Amurka suka yi taho-mu-gama kan batun yankin Taiwan, Philippines ba za ta iya killace kanta daga ciki ba. Irin wannan furucin nasa yana da ban mamaki, wanda ya saba da alkawarin da Philippines ta yi na tsayawa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana, zai kara illata dangantakarta da kasar Sin, da zaman lafiya da tsaro a wannan shiyya.
Rura wutar rikici kan yankin Taiwan, yunkuri ne da Philippines ta yi na dogaro kan Amurka tare da ba ta hadin-kai, don hana ci gaban kasar Sin. Amma batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne na cikin gidan kasar Sin, kuma yadda za’a daidaita batun, harka ce ta al’ummar kasar zalla. Furucin shugaban Philippines ya saba da dokokin kasa da kasa da tsarin mulki na kungiyar ASEAN, tare da kawo babbar illa ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin shiyyar gami da muradun jama’ar Philippines. Mai yiwuwa dogaro kan Amurka zai iya kwantar da hankalin gwamnatin Marcos ta Philippines, amma hakikanin gaskiya shi ne, za ta girbi abun da ta shuka. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Bukaci Afganistan Ta Mayarwa Amurka Sansanin Jiragen Sama Na bagram
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bukaci kasar Agfanistan ta mayarwa kasar Amurka san sanin sojojin sama na kasar wanda ke Bagram ko kuma zata ga ba dadi.
Kafanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka da farko a shafinsa na zumunta na ‘ Truth Social’.
Shugaban ya gargadi Taliban kan vewa idan sun ki mayarwa Amurka sansanin sojojin Bagram to wani abu ba dadi zai faru da sun.
Trump ya dade yana zargin gwamnatin shugaba Biden da ya gada da yin ba dai-dai ba, daga ciki har da ficewa daga kasar Afganistan bayan mamaya na tsawon shekaru 20 ba tare da shiri ba.
Amurka ta mamaye kasar Afganistan tun shekara 2001 har zuwa 2022 inda suka kifar da gwamnatin Taliban da sunan ta bawa shuwagabannin kungiyar Alka’ida mafaka. Sun ci gaba da mamayar har zuwa sake dawowan Talabin a karo na biyu kan madafun ikon kasar.
Amurkawan sun kashewa sansanin sojojin sama na Bagram kudade de, tare da girma kayakin aiki na zamani da kuma hanyoyin tashin jiragen sama har guda biyu a cikinta.
Gwamnatin Taliban dai tace ba zata sake barin wani dan mamaya ya shiga kasarsu ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Ingila Da Canada Da Kuma Australia Sun Bayyana Amincewarsu Da Samuwar Kasar Falasdinu September 21, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Yi Kira Ga Samar Da Tattalin Arziki Da Shugabancin Kwararru September 21, 2025 Arakci Ya Kore Cewa Ya Zanta Da Steven Witkoff Na Amurka September 21, 2025 Hizbullah Ta Yi Gayyar Tunawa Da Zagayowar Shahadar Sayyid Hassan Nasrallah September 21, 2025 Hamas Ta Yi Bukaci A Hukunta HKI Akan Rusa Asibitoci September 21, 2025 IRGC: Duk Wani Sabon Kuskuren Abokan Gaba Zai Fuskanci Mayar Da Martani Mai Tsanani September 21, 2025 Israila Ta Kai Hari Kan Wata Mota A Kudancin Labanon September 21, 2025 Iran Za ta Iya Shawo Kan Duk Wani Takunkumi Da Aka Sanya Mata . September 21, 2025 Pakistan:Yarjejeniyar Tsaro Da Suka Kulla Da Saudiya Kamar Kawancen Tsaro Na Nato Ne. September 21, 2025 Matatar Mai Ta Dangote Ta Kawo Ƙarshen Dogon Layin Mai A Nijeriya September 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci