Aminiya:
2025-08-07@16:25:55 GMT

An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara

Published: 7th, August 2025 GMT

Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.

An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu matsalar tayar motar a kusa da unguwar.

‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore

A yayin da suke ƙoƙarin gyaran tayar ne wasu ’yan bindiga biyar suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta.

Waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu a harin, an bayyana sunayen su da: Alhaji Abdulrazak Ewenla ɗan ƙauyen Ajia da Jimoh Audu daga Gammu.

Mutanen ukun da aka sace sun haɗa da: Kazeem Ajide da Wahidi da Mufutau, duk da cewa har yanzu ba a tabbatar da sunayen mutanen biyu ba.

Bayan afkuwar lamarin, an tura tawagar jami’an ’yan sanda da sojoji da ’yan banga zuwa wurin da lamarin ya afku don tabbatar da tsaro tare da dawo da zaman lafiya.

Rundunar ’yan sandan jihar a cikin wata sanarwa da kakakinta, SP Adetoun Ejire-Adeymi ya fitar a ranar Alhamis, ta tabbatar da faruwar harin.

Sai dai ta yi watsi da wani faifan bidiyo da ke nuna cewa mazauna ƙauyen sun tsere, lamarin da ya haifar da tunanin an ƙauracewa garin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan bindida Kwara

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗaruruwan Tsaffin Jami’an Tsaron Isra’ila Sun Roki Trump Ya A Dakatar Da Yakin Gaza

Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza.

Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana ga Isra’ila”.

“Amincin da kake da shi a wajen Isra’ilawa zai ƙara ba ka damar sanya Firaiminista [Benjamin] Netanyahu da gwamnatinsa a kan hanya daidaitacciya: A kawo ƙarshen yaƙin, a dawo da mutanen da ke tsare a kuma daina gallaza wa Falasɗinawa,” kamar yadda suka rubuta.

Roƙon nasu na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa Netanyahu na ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan soji a Gaza yayin da tattaunawar tsagaita wuta da Hamas ke fuskantar cikas.

Isra’ila ta ƙaddamar da mummuman yaƙi a Gaza sakamakon hare-haren Hamas a Kudancin Isra’ila ranar 7 ga Oktoban 2023 inda aka kashe kusan mutum 1,200 sannan aka yi garkuwa da mutum 251 a Gaza.

Fiye da mutum 60,000 aka kashe sakamakon yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza tun lokacin, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Hamas ta shaida.

‘Ƙawayen Isra’ila sun fara ƙaurace mata’: Ƙasashen duniya sun fara juya wa Netanyahu baya Yadda Birtaniya da ƙasashen duniya 28 suka caccaki Isra’ila kan yaƙin Gaza

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno
  • Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi
  • Yadda kwacen babur da waya ya maye gurbin garkuwa da mutane a Birnin Gwari
  • Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama
  • Hare-haren Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Ya Ragu A Cikin Shekaru Biyu – Ribadu
  • Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina
  • An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa
  • Ƴansanda Sun Kama Ƴan Uwa da Wasu Biyu Kan Ƙirkirar Garkuwa Da Kansu A Abuja
  • Ɗaruruwan Tsaffin Jami’an Tsaron Isra’ila Sun Roki Trump Ya A Dakatar Da Yakin Gaza