Bai Wa Shanu Guba: Sojoji Sun Shiga Tsakani Domin Dakile Yunkurin Ramuwar Gayya A Filato
Published: 17th, April 2025 GMT
Dakarun da ke karkashin sashe na 3 na OPSH, da aka tura wurin da lamarin ya faru, biyo bayan kiran gaggawa da aka yi musu, sun tabbatar da cewa, makiyayan sun riga sun yanka shanun da kansu, domin gudun kar a yi asara da yawa. Binciken da aka yi a yankin ya kai ga gano tumatur da ake zargin guba ne da yalon lambu an warwatsa a filin.
A martanin da babban jami’in runduna ta 3 kuma kwamandan OPSH, ya jagoranci wata tawaga mai karfi da suka hada da shugaban karamar hukumar Bassa, jami’in ‘yansanda na shiyya, da sauran masu ruwa da tsaki zuwa wurin domin ganewa idanunsu. Ziyarar ta kwantar da yiwuwar tarzoma tare da dakile duk wani harin ramuwar gayya daga al’ummar Fulanin da abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Yi Juyin Mulki A Ƙasar Madagascar
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya October 15, 2025
Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02% October 15, 2025
Labarai Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba October 15, 2025