2025-10-13@18:08:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 130
«bangaren zartarwa»:
Ta ce, “Dole ne akwai kalubale da dama, wanda daga cikinmu muke fuskanta a yayin shigowa wannan masana’anta, amma dai ni babu wani abu da zan iya tunawa, illa wani wanda na iske a masana’antar ya karbi zunzurutun kudi har Naira 50,000 a mabanbantan lokuta da sunan zai yi min rijista a masana’antar, kuma bai yi ba, daga karshe ma na gano cewa; kudin rijistar duka-duka Naira 5,000 ne. A wata hira da Khadija ta yi da gidan Rediyon Hikima, ta bayyana cewa, matukar ta samu abin da ya kawo ta masana’antar (Kudi), to nan da shekara daya ma; za ta iya shiga daga ciki, ma’ana za ta samu miji ta yi aurenta na Sunna. Khadija, wadda ta...
Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya aike da sako zuwa wurin taron kas ana raya salla karo na 32, ya yi ishara da rawar da sallolin farilla suke takawa wajen ayyana makomar mutum a duniya da kuma lahira. Haka nan kuma ya ce; Nauyi ne da ya rataya a wuyan cibiyoyin addini, da malamai da masu riko da addini da su rika yada yin kira da a yi salla da kuma bayyana sauyin da take samarwa a badinin mutum. Bugu da kari jagoran juyin juya halin musuluncin na Iran ya yi kira da a yi amfani da dukkanin hanyoyin sadarwa na zamani domin isar da wadannan sakwannin akan salla. Sakon na jagora ya bayyana taron shekara-shekara da ake yi akan...
Ya gargadi masu kafa kungiyoyi daban-daban a Arewa, yana kiran irin waɗannan ƙungiyoyi “barazana ga haɗin kan Arewa.” Haka kuma ya yaba wa sojojin Nijeriya bisa kokarinsu da sadaukarwa wajen yaki da matsalar tsaro. Alhaji Dalhatu ya kuma yi Allah wadai da “ƙungiyoyin marasa kishin ƙasa” da suka jawo rikicin baya-bayan nan a matatar mai ta Dangote, tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani. A cewarsa, kwanan nan an samu rikice-rikicen maganganu masu karo da juna daga wasu jami’an ACF a matakin kasa da jihohi, wanda hakan ya sa dole a kafa tsarin sadarwa mai tsauri. “Majalisar Amintattu tana da ikon da nauyin Ya bayyana cewa taron, wanda shugabannin jihohi, sakatarori, da mambobin Arewa 100% Focus Group suka halarta, zai...
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fitar da sanarwa game da shirin tsagaita wuta a Gaza Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar da sanarwa a yammacin jiya Lahadi dangane da shirin tsagaita bude wuta a zirin Gaza da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gabatar, inda ta jaddada cewa a ko da yaushe Iran tana goyon bayan duk wani yunkuri na tabbatar da kawo karshen kawar da wata al’umma daga kan doron kasa, laifukan yaki, da cin zarafin bil’adama a Gaza da kuma share fagen tabbatar da ‘yancin cin gashin kan al’ummar Falastinu. Bayanin ya ci gaba da cewa: Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran tana tunatar da al’ummar kasa da kasa alhakin shari’a da da’a na tunkarar kisan gillar da...
Sanarwar ta ce, hare-haren kakkaɓe maɓoyar ‘yan bindigar na zuwa ne a karkashin shirin ‘Operation Lafiya Nakowa’, da nufin fatattakar ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka a jihar Taraba. Ya kara da cewa, harin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ta’addan a kusa da Tarhembe, Tornyi, TY Farm, da ɗaukacin yankin Kando da ke yankin Tati, karamar hukumar Takum, da kuma rahotannin lalata gonaki a karamar hukumar Ussa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya gana da Gwamna Siminalayi Fubara da wasu Dattawan Jihar Ribas. Mai taimaka wa Wike kan yaɗa labarai, Lere Olayinka ne, ya wallafa hoton ganawar a shafukan sada zumunta, inda ya ce kakakin Majalisar Dokokin jihar, Martin Amaewhule, ya halarci taron. An yi wata gagarumar zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a Turai Ban taɓa cewa Buhari yana da alaƙa da Boko Haram ba — Jonathan Ko da yake Olayinka bai bayyana abin da aka tattauna a taron ba, amma wannan ce ganawa ta farko da aka yi tsakanin Wike da Fubara tun bayan da gwamnan ya kori wasu daga cikin muƙarrabansa yayin da yake shirin kafa sabuwar majalisar zartarwa a jihar. Rahotanni sun nuna cewa...
Sojojin HKI sun bada sanarwan cewa zasu fara shirin aiwatar da shirin shugaban Trump na tsagaita buduewa juna wuta a Gaza. Da kuma batun musayar fursinoni gaba daya da kungiyar Hamas. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudia ya bayyana cewa a jiya da yamma ne kungiyar Hamas ta bayyana cewa ta amince da tsagaita wuta tsakaninta da HKI wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya gabatar. Kungiyar ta bayyana cewa ta amince da wasu sassa na yarjeniyar amma sai an tattauna kan wasu. Wata majiyar sojojin yahudawan ta bayyana cewa shuwagabannin kasar sun basu umrnin dakatar da kai hare- hare kan falasdinawa a Gaza. Wannan sanarwan ta zo sa’o’ii kadan bayan da shugaban Amurka ya umurci...
Anyanwu a cikin wasikarsa ya bayyana cewa an kammala dukkan shirye-shirye wasu tsare-tsare don gudanar da taron, kuma za a gudana da shi kamar yadda aka tsara. “Muna tabbatar wa hukumar zabe cewa za mu gudanar da taron kamar yadda aka tsara tun farko ba tare da dagawa ba. “Ya kamata hukumar zabe ta yi watsi da wasikar da shugaban jam’iyyar ya tura mata tun da farko na dage toron,” ya aika wa INEC wasikar ne a ranar 26 ga Satumba ba tare da sa hannunna ba. A cewar sakataren, bai kamata INEC ta yi aiki kan wata wasikar da ba sanya hannunsa hade da na Damagum ba. Wata majiyar ta bayyana cewa abin da ke faruwa yanzu ya nuna...
Sarah Mullally ta zama sabuwar Shugabar Cocin Ingila, wato Archbishop ta Canterbury, inda ta kasance mace ta farko da za ta jagoranci Cocin Ingila inda wannan muƙamin ya samo asali tun zamanin Daular Romawa da kuma al’ummar Anglican na duniya. Sarki Charles III ya amince da naɗin Mullaly bayan kwamitin da aka dora wa alhakin nemo wanda zai maye gurbin Justin Welby, wanda ya yi murabus a farkon wannan shekarar saboda wani zargi na cin zarafi, kamar yadda gwamnatin Birtaniya ta sanar a ranar Jumma’a. Cocin Ingila ita ce ta haifi ɗarikar Anglican a duniya. Mullally, mai shekaru 63, ta zama Archbishop ta Canterbury ta 106. A cikin wata sanarwa, tsohuwar ma’aikaciyar jinya ta bayyana cewa ta fahimci “babban nauyi”...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga daukacin jama’ar kasar Sin da su yi aiki tukuru, tare da ingiza wanzar da zamanantarwa irin ta Sin. Xi, wanda kuma shi ne sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban hukumar zartarwar rundunar sojojin Sin, ya yi kiran ne yayin taron bikin cika shekaru 76 da kafuwar janhuriyar jama’ar kasar Sin, wanda ya gudana yau Talata a babban dakin taruwar jama’a dake birnin Beijing. Shugaba Xi, ya jaddada cewa a gabar da yanayin harkokin duniya ke saurin sauyawa cikin sama da karni guda, dole ne a yi aiki tukuru wajen yayata akidun bai daya na dukkanin bil’adama, da aiwatar da tsarin cudanyar mabanbantan sassa, da ingiza aiwatar da shawarwarin bunkasa ci gaban...
Mahukuntan Taliban a Afghanistan sun sanar da rufe dukkanin hanyoyin sadarwa a fadin kasar, makonni bayan da suka fara katse intanet, domin hana abin da suka bayyana a matsayin tabarbarewar tarbiyya. Wata kungiya mai sa ido kan harkokin yanar gizo ta ce yanzu baki ɗaya ana fama da rashin intanet a kasar. Wani jami’in Taliban ya ce rufewar za ta ci gaba har sai an bayar da wata sanarwa a nan gaba. Shugaban Taliban, Hibatullah Akhund-zada, ya bayar da umarnin fara cire wayoyin sadawar dake ƙarkashin kasa na intanet tun a farkon wannan wata. BBC ta rawaitu cewar kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ya rasa ji ta hanyoyin sadarwa daga ofishinsa na Kabul, ciki har da ta wayar...
Gwamnatin tarayya ta soke bikin faretin da aka shirya gudanarwa domin murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a ranar Laraba, 1 ga watan Oktoba. Wannan sanarwar ta fito ne a ranar Litinin daga Ofishin sakataren gwamnatin tarayya. “Soke faretin bikin ƴancin kai da gwamnati ta shirya gudanarwa a ranar Laraba, 1 ga Oktoba ba zai rage darajar wannan muhimmiyar rana ta tarihi ba,” in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnati na ba da haƙuri kan wannan sauyi, amma sauran ayyukan da aka tsara domin zagayowar ranar za su ci gaba kamar yadda aka tsara. Wannan ya haɗa da jawabin shugaban ƙasa, bukukuwan al’adu, da wasu abubuwa da aka shirya.
Idan aka zo batun “salon zamanantarwa irin na kasar Sin”, za ku so ku ji shin: Takamaime wace irin hanya ce wannan? Me ya bambanta ta da zamanantarwa irin ta sauran kasashe a duniya? A gaskiya dai, fahimtar salon zamanantarwa irin na Sin babu sarkakiya a ciki. Tana nan lullube a cikin harkokin yau da kullum na jama’ar kasar Sin, da ma alakar da ke tsakanin wannan kasar da sassan duniya. Salon zamanantarwa irin na kasar Sin wani tsarin zamanantarwa ne na dimbin jama’a, da zamanantar da samun wadata ta bai-daya domin daukacin al’umma, da zamanantar da tsarin dunkulewar kayayyaki da ruhin wayewar kai, da zamanantar da zaman lumana tsakanin mutum da dabi’ar halitta, da kuma zamanantar da bin hanyar...
Yawan tashoshin fasahar sadarwa ta 5G a kasar Sin ya kai kusan miliyan 4.65 a karshen watan Agusta, kamar yadda alkaluman mahukunta suka nuna a yau Talata. A cewar ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, adadin ya kai kashi 36.3 na adadin tashoshin sadarwar wayar hannu a fadin kasar baki daya. A halin yanzu, ana samun karuwar masu wayar salula a kasar Sin da ke rungumar amfani da fasahohin sadarwa na 5G. Alkaluman da aka fitar zuwa karshen watan Agusta sun nuna cewa, yawan masu amfani da wayar salula na manyan kamfanonin sadarwa uku da kuma kamfanin China Broadnet ya kai kimanin biliyan 1.82. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
Mutune 70 da aka yi garkuwa da su sun samu ƴanci a Jihar Katsina, bayan yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da fitaccen shugaban ƴan bindiga, Isiya Kwashen Garwa. A wani faifan bidiyo da ya bayyana, Garwa ya saki mutane 40 a ƙaramar hukumar Faskari, kwanaki biyu bayan ya fara sakin wasu 30, wanda hakan ya kai adadin zuwa 70 gaba ɗaya. Rahotanni daga mazauna yankin sun ce sakin na baya-bayan nan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin shugabannin al’umma da sansanin Garwa, a wani mataki da ake ganin zai rage tashin hankali da hare-hare a yankin. Duk da haka, Garwa ya nuna rashin jin daɗi kan abin da ya kira sumamen Sojoji a unguwar Ruwan Godiya a lokacin Sallar Juma’a, inda...
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafin makiya zai fuskanci mayar da martani mai muni A cikin wata sanarwa da suka fitar a farkon makon tsaro mai alfarma, na ranar tunawa da arangama da gwamnatin Saddam ta yi da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a tsakanin shekarun 1980-1988, dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) sun jaddada cewa: Duk wani sabon kuskuren lissafi da makiya za su yi, za su fuskanci mummunan martani da zai zame babban darasi a gare su. A cikin bayanin da suka yi na farkon makon tsaro na dakarun IRGC sun bayyana cewa: A hakikanin gaskiya makon tsaro, biki ne na nasarar gwagwarmayar jama’a, kuma abin...
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu. “Na ji wani babban ƙara har sai da ya girgiza gine-ginen da ke kewayen DICON. Mutane na ta gudu daga wurin, amma muna tunanin fashewar bam ne, amma daga baya mun gano cewa daga masana’anta ne,” inji wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa. Shaidun gani da ido sun ce fashewar na da nasaba da samar da hoda mai matukar muhimmanci wajen ƙera hodar harsashi ga sojojin Nijeriya. Daga...
Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Sayinna, da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Sun kashe Hakimin ƙauyen, Malam Murtala Sa’adu, tare da wani mutum mai suna Ibrahim Mai-Kuɗi. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba Mai bai wa shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza shawara, Alhaji Gazali Raka ne, ya tabbatar da harin. Ya ce maharan sun kashe hakimin ne saboda yana taimaka wa ’yan sa-kai wajen tsaro a yankin. An ce maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Alhamis, inda suka dinga harbi a ko ina. Bayan sun kashe mutanen biyu, sai...
Zhakom ya ƙara da cewa, wanda aka cafken da kuma kayayyakin da aka ƙwato suna hannun rundunar domin ci gaba da bincike, kuma rundunar za ta ci gaba da farmakar wadanda suka tsere daga haramtacciyar masana’antar kera makaman. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu. Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido Wada ya jagoranta a Dutse babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, Rundunar za ta hada gwiwa da wadanda abin ya shafa domin fuskanatar kalubalen zirga-zirga don daukar matakin da ya dace. A cewarsa, rundunar ta ci gaba da shirye-shiryen ‘yan sanda da al’umma ke tafiyar da su ta hanyar samar da hadin gwiwa mai karfi da masu ruwa da tsaki da suka himmatu...

Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
Bikin baje kolin hada-hadar ba da hidima na kasa da kasa wato CIFTIS a takaice na shekarar 2025 da aka rufe a yau Lahadi, ya ja hankalin masu saka jari daga tarin kasashen waje. Manyan jami’an kamfanoni na kasashen waje sun bayyana cewa, suna daukar bikin a matsayin wata babban dandamali na more damammaki tare da kasar ta Sin. Game da dalilan da suka sa ake zabar kasar Sin don gudanar da hada-hadar kasuwanci, mataimakin babban darekta mai kula da harkokin gwamnati da manufofi na kasar Sin na kamfanin Johnson & Johnson Mr. Zhao Jun ya ce, “Da farko shi ne, don biyan bukatun gaggawa na Sinawa kimanin miliyan 1400 a fannin kiwon lafiya. Na biyu a Sin akwai wani...
ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan. “An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya, tare da rufe tashar rediyo ta kashin kai a Jihar Neja, kafin ya ƙaru zuwa ga kai hare-haren da aka ɗauki nauyi kan taronmu na Kaduna, sannan kuma da hare-hare a kan ayarin motocin shugabannin ADC a Kebbi. “Haka kuma an kai hari a wurin taron ADC a Alimosho a Jihar Lagos, wannan yana nuna cewa APC ta ji kunya kuma ba ta girma ko...
Wasu matasa da ake zargin ’yan daba ne sun tarwatsa wani taro da dattawan Katsina suka shirya a kan zaman lafiya a jihar jim kadan da fara shi ranar Talata. Hakan na zuwa ne ’yan kwanaki kadan bayan an kai irin makamantan irin wadannan hare-haren a kan tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i da tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami. Wata kungiya mai rajin tabbatar da zaman lafiya a jihar mai suna Katsina Security Community Initiative ce ta shirya taron na ranar Talata da nufin lalubo bakin zaren kan matsalar tsaron da ta addabi jihar. Gwamnatin Tarayya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutun Mauludi Tinubu ya dawo da shugaban NTA da ya sauke Katsina dai ta shafe tsawon shekaru tana...
A wata ziyarar da wata tawagar yan jarida daga Iran suka kai birnin Mosco, kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyin habaka dangantaka na sardarwa tsakanin kasashen biyu. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa hukumar tashoshin talabijin da Radiyo na kasar Iran da kuma na bangaren Rasha sun karan zurfafa dangantaka tsakaninsu a fagen yada labarai a yankin da kuma duniya gaba daya. Labarin ya kara da cewa wannan dangantakar zai sa fuskance labaran karya wadanda kafafen yada labarai na yamma suke yadawa. Har’ila yau yarjeniyoyin aiki tare tsakanin hukumomin watsa labaran kasashen biyu zai samar da labarai iri guda da kuma fadada hanyoyin samun labaran gaskiya a tsakaninsu. Daga cikin yarjeniyoyin dai akwai na tsakanin...
Makami mai linzami na Yemen na fission ballistic shi ne babban mafarkin da ke firgita ‘yan sahayoniyya Jaridar Isra’ila, The Jerusalem Post, ta yi bayanin cewa: Harba makamai masu linzami na gungu fission ballistic daga Yemen yana kara yawan barazanar tsaro, tare da dagula Shirin kakkabo shi, kuma yana janyo wahalar murmurewa daga barnarsa. Jaridar ta ce amfani da makamai masu linzami na gungu fission ballistic da ‘yan Yemen suka yi a kan abokan gabar Isra’ila na wakiltar wani gagarumin ci gaba mai kunshe da damuwa, tare da lura da cewa wadannan makamai masu linzami suna mayar da tsarin kariya na makamai masu linzami na gargajiya irin su Arrow ko Sling na David marasa amfani saboda ba su da kayan...
Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen Sayyeed Abdulmalik Badruddeen Huthi , a jawabinsa na mako-mako da ya saba gabatarwa, dangane da Falasdinu da kuma sabbin al-amura da suka faru ko suke faruwa a yankin da kuma duniya gaba daya ya tabo al-amura da dama. Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye shiryenta da harshen larabci a nan Tehran ta bayyana cewa, shugaban Ansarullah, ya yi gargadi kan cewa, ida HKI tana son dabbaka shirinta na Isra’ila babba, a cikin wannan halin da kasashen larabawa suke rarrabe, hakan zai zama musiba babba. Labarin ya kara da cewa sojojin kasar Yemen sun aiwatar da ayyukan soje a kan HKI a dama a cikin makon da ya gabata, daga cikin cilla makamai...
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kundin tsarin mulki na hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) da asusun samar da ayukka na kasa da kasa (USPF), dukkanin su a karkashin ma’aikatar sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arziki na zamani. A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai ya fitar, ya ce an nada Idris Olorunnimbe a matsayin shugaban hukumar NCC, yayin da Dr. Aminu Waida ya ci gaba da zama mataimakin shugaban zartarwa/Babban jami’in gudanarwa, mukamin da aka nada shi a watan Oktoban 2023 kuma majalisar dattawa ta tabbatar da shi a watan Nuwamba na wannan shekarar. A baya Olorunnimbe ya yi aiki a hukumar kula da ayyukan yi na jihar...
Ministan harkokin wajen kasar Armenia Ararat Mirzoyan ya tabbatarwa JMI kan cewa yarjeniyar sulhu da suka cimma da kasar Azairbaijan ba zai shafi bukatun kasar Iran ko kuma hanata wani hakkinta a yankin kaukas ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Armenia yana fadar haka a safiyar yau Talata, ta wayar tarho a lokacinda yake zantawa da tokwaransa na kasar Iran Abbas Aragchi. A cikin wannan makon ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya jagoranci yarjeniyar zaman lafiya tsakanin kasashen Azarbaijan dangane da yankin karabakh a fadar White House. Sannan akwai labarin cewa za’a gina wani babban titi wanda zai ratsa kasashen bitu. Kasashen dai suna makobtaka da kasar Iran, don haka dangantakarsu...
Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi karin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tantancewa. Bukatar, wacce aka mika ta wata wasika daga bangaren zartarwa, ta nemi amincewar majalisar ta kara kasafin kudi naira biliyan 169,522,463,294.82 domin daukar muhimman ayyukan raya kasa a fadin jihar. Kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya bayyana cewa hukumar zartaswa na kokarin ganin an kara wa kasafin kudin domin gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su shafi rayuwar mazauna. Bayan sun yi duba, ‘yan majalisar sun mika kudirin dokar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar domin tantancewa da daukar matakin da ya dace. A wani labarin kuma, Majalisar ta kuma samu takarda daga bangaren...
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tattaunawa da amincewa. Bisa wasikar da bangaren zartarwa ya aika wa Majalisar, ana neman amincewar ta kan ƙarin kasafin kuɗi na kimanin Naira biliyan 170 domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fadin jihar. Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya bayyana cewa bangaren zartarwa yana neman wannan ƙarin kuɗi ne domin gudanar da ingantattun ayyuka da za su amfani rayuwar al’ummar jihar. Bayan tattaunawa, ‘yan majalisar sun mika kudirin ga Kwamitin Majalisa kan Kasafin Kuɗi domin yin bincike da shirye-shiryen aiwatar da dokokin da suka dace. A wani labarin kuma, majalisar ta karɓi...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ƙasar ya bukaci waɗanda aka naɗa su yi amfani da ƙwarewarsu wajen tabbatar da burin gwamnatinsa a fannin wutar lantarki. Onanuga ya bayyana cewa waɗannan nade-naden suna jiran tantancewar Majalisar Dattawa. Sai dai, domin kauce wa gibin shugabanci a hukumar, Shugaba...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan. Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa suka zabi zama “sojojin baka” ko “karnukan farautar” ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta. Domin sauke shirin, latsa nan
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani kakkausar gargadi kan matsalar ruwan sha da ke kara kamari a zirin Gaza, inda ta bayyana cewa yunwa na ci gaba da rataya a kan al’ummar da ke kara hana samun tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli. A cikin wani sabon rahoto, MDD ta ce kashi 96% na iyalai a Gaza na fuskantar matsalar rashin ruwa, yayin da kashi 90% na al’ummar kasar ba su da tsaftataccen ruwan sha. Ya kara da cewa kashi 75 cikin 100 na mazauna garin suna kokawa wajen shiga bandaki, lamarin da ke kara tabarbarewar bala’in jin kai a cikin ci gaba da kawanya da kuma ta’addancin Isra’ila na tsawon watanni Tun da farko, ofishin kare hakkin bil...
A kwanakin baya, an bude tashar jirgin ruwa ta fasinja ta kasa da kasa ta kasar Sin ta farko, wato tashar jirgin ruwa ta Shekou dake birnin Shenzhen. ’Yan kasuwa daga Argentina, da Chile, da Brazil sun shiga kasar Sin ta tashar bisa sabuwar manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, inda aka rage lokacin daidaita aikin canza jirgi daga awoyi biyu da rabi zuwa kasa da rabin awa. Wannan ya shaida cewa, an aiwatar da manufar shiga kasar Sin ba tare da biza ba, ba ma kawai a filin jirgin sama ba, har ma a tashar jirgin ruwa. Hakan ya hanzarta raya cinikayyar Sin da kasashen waje. Wannan batu ya kasance wani misali, bayan da kasar Sin...
Dandali na NINAuth, wanda NIMC ya tsara kuma ya aiwatar, yana bayar da damar tantance bayanan ‘yan kasa ta hanya mafi dacewa da aminci don tabbatar da asalinsu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnatin Nijeriya ta bayanna cewa za ta soma yi wa ɗaliban jami’o’in ƙasar nan gwajin miyagun ƙwayoyi a wani mataki na daƙile yaɗuwar ta’ammali da ƙwayoyin. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya tare da haɗin gwiwar Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ne za su jagoranci aikin. Sarkin Gudi na Jihar Yobe, Isa Bunuwo Ibn Khaji ya rasu Gwamnatin Jigawa ta horas da malamai 20,000 fasahar sadarwar zamani Hakan na zuwa ne bayan ganawar Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya da kuma ministan ilimin ƙasar, Olatunji Alausa a jiya Laraba. Ɓangarorin biyu sun kuma amince da ɓullo da daftarin koyar da darasin ilimin ta’ammali da ƙwayoyi a makarantun sakandiren...
’Yan bindiga sun tarwatsa kauyuka sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina sannan suka mayar da sama da 6,000 ’yan gudun hijira. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono. Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su....
’Yan bindiga sun tarwatsa kauyaku sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Maharan dai sun rika kashe mazauna kauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa. Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa kauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono. Gwamnatin Tinubu ta mayar da Arewa saniyar ware – ACF DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar Ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauran su. Hakan dai ya haifar da kauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masana kiwon lafiya sun bayyana yadda ruma ke yada matsalolin rashin lafiya ga lafiyar jikin mutum. Musamman a lokuta irin na damina, ruma kan dabaibaye gidajen mutane da dama na tsawon lokaci wanda ka iya jawo matsaloli daban-daban ga lafiya da kuma gidajenmu. NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan irin matsalolin da ruma ke haifarwa ga lafiyar jikin namu. Domin sauke shirin, latsa nan
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin masani a harkar hulɗa da jama’a kuma ma’aikacin gwamnati na gari da ya bayar da gagarumar gudunmawa ga jihar. Ya ce aikin wayar da kai da ya yi ba za a manta da shi ba. Gwamna Bala Muhammad, ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar tare da miƙa ta’aziyya ga iyalansa, abokansa da masarautar Bauchi. Ya bayyana Ilelah a matsayin mutum mai kishin ƙasa da jajircewa a bakin aiki. Ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya jiƙansa kuma ya sanya shi a Aljanna Firdausi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na...
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya yi kira da a tsananta hukunci kan masu cin zarafin ’ya’ya mata, yana mai cewa babu wani musulmi nagari da zai yi wa matarsa dukan da har zai yi mata lahani. A yayin da yake tunatar da malamai da limamai kan muhimmiyar gudunmawar da za su bayar a wannan fage domin yi wa tufkar hanci, Sarkin ya bayyana damuwa kan yadda matsalolin fyade da kuma samun magidantan da ke dukan matansu suka zama ruwan dare a Jihar Kano. Yunwa na ƙara tsanani a Arewa maso Gabashin Nijeriya — ICRC Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh Sarki Sanusi na wannan furuci yayin da ya karbi bakuncin tawagar cibiyar bunkasa bincike (dRPC)...
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa; Iran ba za ta amince da duk wata shawara akan ta dakatar da tace sanadarin Uranium ba wanda halartaccen hakkinta ne.” A jiya Asabar ne majiyar diplimasiyyar jamhuriyar musulunci ta Iran ta sanar da tashar talabijin din ‘almayadin’ cewa; Tace sanadarin Uranium a cikin kasarta hakkinta ne halartacce, kuma babu sauyi a cikin matsayar Rasha dangane da haka.” Wata majiyar Rasha ta ce, gabanin harin HKI akan Iran, a lokacin da ake tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka, Moscow ta amince da a fitar da tataccen Uranium sama da daraja 3.67% daga cikin kasar Iran zuwa Rasha a matsayin bayar da tata gudunmawar na warware sabani. A ranar 20 ga watan...
Kamfanin dillancin labarun “Associated Press” wanda ya sami hotunan tauraron dan’adam na cibiyar sojojin Amurka dake “al-udid” a kasar Qatar, ya nuna yadda harin ya sami wata Qubba, da a cikinta akwai na’urorin sadarwa da Amurka ke amfani da su.” Hotunan tauraron dan’adam na ” Planet Labs” sun nuna yadda Qubbar ta sansanin Amurka a Qatar take sa’o’i kadan gabanin a kai harin a ranar 23 ga watan Yuni. Rundunar Amurka ta 379 mai aikin ttatara bayanai ta kafa wannan Qubbar ne tun a 2016 da kudin da sun kai dalar Amurka miliyan 15. Haka nan kuma tauraron dan’adam din ya nuna yadda qubbar ta bace, da kuma yadda ginin da yake kusa da ita ya illata. Kamfanin dillancin labarun...
Dakarun sojojin Nijeriya na rundunar sojojin sama tare da haɗin gwiwar Operation Haɗin Kai sun kai farmaki kan wasu muhimman wuraren da ’yan ta’adda suka mamaye a tsaunin Mandara da ke Jihar Borno. An samu labarin cewa rundunar sojin sama ta gudanar da samamen ta ne a wani wuri da aka san shi da tudu mai tsauni, wanda ke kan iyakar Nijeriya da Kamaru, bayan samun bayanan sirri. An gurfanar da wasu kan zargin kashe matafiya bikin aure a Jos ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Daily Trust ta ruwaito cewa, samamen share fagen ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya umurci sojoji da su kawar da...
Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tsayar da 24 ga watan Yulin bana a matsayin ranar da za ta gudanar da taronta na Majalisar Zartarwa. Mataimakin Sakataren jam’iyyar, Barista Fetus Fuanter ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Litinin a Abuja. Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe Jami’an tsaro sun hana taron kwamitin amintattun PDP Fuanter ya ce kusoshin jam’iyyar za su gana kafin gudanar da taron Majalisar Zartarwar. Taron da za a gudanar shi ne na biyu ta fuskar girma a cikin jerin tarukan da jam’iyya ke zaman yanke shawara da daukar wasu muhimman matakai bayan babban taronta na kasa. Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba cece-kuce tun bayan murabus...
Jami’an tsaro sun hana mambobin Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar Adwa ta PDP gudanar da taron da suka tsara gudanarwa. A safiyar Litinin din nan ne jami’ai da yawa ne suka kutsa cikin zauren da aka tsara gudanar da taron inda suka bukaci wadanda suka hallara da su watse. Jami’an tsaro da aka jibge a hedikwatar babbar jam’iyyar adawar sun hana mambobin kwamitin amintattu gudanar da taronsu a hedikwatar jam’iyyar. Har zuwa lokacin hada da wannan rahoto, wasu daga cikin ’yan kwamitin amintattun na PDP suna tattaunawa a kan halin da ake ciki. Mun samu rahotannin cewa jami’an sun umurci mambohin su bar ofishin jam’iyar domin ganin ba a gudanar da wani taro a ofishin jam’iyar ba.
“Abin da muke son cimma shi ne, a duk shekara mu tabbatar da ganin mun rubanya yawan madarar da ake samarwa kasar a kasar daga tan miliyan 700,000 zuwa tan miliyan 1.4 daga nan zuwa shekara biyar masu zuwa”, a cewar Ministan. “A Nijeriya akwai sama da Shanu miliyan 20.9, Tumaki sama da miliyan 60, Awakai sama da miliyan 1.4”, in ji shi. Kazalika, Minstan ya kara da cewa; burin shi ne ganin an kara bunkasa tattalin arzikin kasar tare da kuma kara samar da ayyukan yi ga ‘yan kasar. “Ina son fayyace cewa, ba wai batu ne kawai na yawan Shanun da ake da su a kasar nan ba, batu ne na jama’a da samar da ayyukan yi, habaka...
Wasu gungun ƙudan zuma sun kai hari tare da tarwatsa ɗaliban da ke rubuta jarrabawar Hukumar da ke shirya jarrabawar kammala sakandare ta ƙasa ta Najeriya (NECO) a makarantar sakandaren kimiyya ta Mairi da ke Maiduguri a Jihar Borno. Wannan hari na ba-zata da gungun ƙudan zumar suka kai ya tilastawa ɗalibai da malaman makarantar tserewa daga harabar makarantar domin neman tsira. Shugaban APC na ƙasa Ganduje ya yi murabus NDLEA ta kafa cibiyar kula da masu shaye-shaye a Yobe Shaidun gani da ido sun ce, sun ga ɗalibai na barin litattafai da takalma da jakunkuna, har ma da kekunansu yayin da suke gudu daga makarantar. A cewar wani ɗalibin da ke jarabawar da ya nemi a sakaya sunansa ya...
Ga cibiyoyin CBT, Oloyede ya ce dole ne a gargadi wadanda ke da hannu sannan a nemi su sanya hannu kan takardar yarjejeniya. Kuma bayan yarjejeniyar, za a kuma buƙaci su ba da shaidar horar da masu rajistar daliban. Da yake karin haske kan shawarwarin, Oloyede ya ce hukumar ba za ta yi la’akari da duk wani uzuri ba daga cibiyoyin da abin ya shafa a nan gaba ba, duk da ikirarin da suke yi na rashin sani, don haka akwai bukatar su samu horon da ya dace a jami’o’in gwamnatin tarayya da ke kusa da su kafin JAMB ta kara amincewa da su. Cibiyoyin CBT da abin ya shafa da aka gayyata taron sun hada da Misau...
An shiga zaman ɗari-ɗari a garin Makurdi na Jihar Benuwe, bayan ’yan sanda sun harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa wasu masu zanga-zanga a shataletalen Wurukum. Masu zanga-zangar sun fara taruwa da misalin ƙarfe 9:30 na safe domin nuna fushinsu kan kisan mutane sama da 100 a garin Yelewata da ke Ƙaramar Hukumar Guma, a ranar Asabar. Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan Shettima HOTUNA: Yadda aka yi sulhu da ƙasurgumin ɗan fashin daji Ado Aliero a Katsina Tun kafin fara zanga-zangar, jami’an tsaro daga hukumomi daban-daban sun mamaye manyan hanyoyi a birnin Makurdi. Da safiyar ranar Lahadi da misalin ƙarfe 7 na safe jami’an tsaro, ciki har da motar yaƙi ta ‘yan sanda...
Bugu da kari, akwai kuma masu kiwon Tarwada a gonar da sama da su 600, wadanda aka rage yawan adadinsu daga 1,327 zuwa 600, bayan bullar cutar annobar Korona, saboda kalubalen ci gaba da gudanar da sauran ayyukan gonar. A shekarar 2024, masu kiwon Tarwadar a gonar; sun samar da Tarwadar da yawanta ya kai kimanin tan 1,700, wadda kuma aka kiyasata cewa; kudinta ya kai na Naira biliyan 4.5. Wannan ba karamin ci gaba ba ne, musamman duba da cewa; gonar ta kasance abin koyi ga sauran kungiyoyin da ke kiwon Tarwada a daukacin fadin wannan kasa. Bisa wannan nasarori da gonar ta samar, hakan ya nuna yadda take ci gaba da samun yabo daga kasashen duniya, cikin masu...
Majiyar sojan Rasha ta sanar da cewa; Tun daga watan Febrairu na 2024, zuwa yanzu ta tarwatsa tankokin yaki samfurin ” Abrams” kirar Amurka da ta bai wa kasar Ukiraniya har guda 26. Ya zuwa yanzu adadin wadannan tankokin da su ka rage a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5, ba domin adadinsu 31 ne. Kamfanin dillancin labarun ” Sputnik” ne ya bayyana cewa; adadin tankokin yakin na Amurka da su ka saura a tare da sojojin Ukiraniya ba su wuce 5 ba. Tun a watan Janairu na 2023 ne dai tsohon shugaban kasar ta Amurka Joe Biden ya sanar da bai wa Ukiraniya tankokin yaki samfurin Abrams a karkashin taimakon kayan yakin da take bai wa kasar....
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya aika da sakon taya murnar Babbar Sallah ga al’ummar Musulmi, yana kira gare su da su rungumi darajoji na sadaukarwa, biyayya da hakuri irin wanda Annabi Ibrahim (AS) ya nuna. A wata sanarwa da Daraktan Yada labarai na gidan gwamnati, Ismaila Uba Misilli ya fitar, Gwamnan ya yi kira da a yi addu’o’in zaman lafiya da haɗin kan Jihar Gombe da Najeriya baki ɗaya. Ya jaddada muhimmancin nuna soyayya, tausayi da zama mai ƙyau da maƙwabta a rayuwar yau da kullum. “Yayin da muke murnar Babbar Sallah, mu yi tunani kan abin da take nufi biyayya, sadaukarwa da ƙwarin gwiwa,” in ji Gwamna Yahaya, yana mai ƙarfafawa al’umma da su ci gaba da...
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Gwamnatin jihar Zamfara tana taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar wannan rana ta Babbar Sallar. “Babbar Sallah tana bai wa Musulmi damar girmama sadaukarwar da Annabi Ibrahim (AS) ya yi na ɗansa domin biyayya ga umarnin Allah. “Tana tunatar da mu muhimmancin imani, rashin son kai, da sadaukarwar da muke da ita ga al’umma da bil’adama, ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen yin tunani a kan kimar sadaukarwa da biyayya ga Allah Maɗaukakin Sarki. “Dole ne mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙi da duk wani nau’i na munanan ɗabi’u da kuma laifuka da suka shafi al’ummarmu. “Haƙƙinmu ne na gamayya mu yi aiki don tabbatar da tsaron al’ummarmu,...

Masu Bincike Na Sin Sun Cimma Sabon Sakamako A Fannin Saurin Sadarwa Tsakanin Tauraron Dan Adam Da Doron Duniya
Wasu masu binciken fasaha na kasar Sin, sun cimma sabon sakamako a fannin saurin sadarwa tsakanin tauraron dan adam da doron duniya, inda suka karya matsayin saurin da ake da shi a baya, ta amfani da salon X-band mai tasha guda. Rahotanni na cewa masu binciken, daga cibiyar binciken harkokin sadarwar samaniya ko AIR, karkashin hukumar lura da binciken kimiyya ta kasar Sin, sun cimma nasarar gudanar da sadarwa da saurin da ya kai megabit 2,100 duk dakika, adadin da ya haura wanda ake iya samu ta fasahar “microwave”, da karin kaso 75 bisa dari na saurin sadarwar. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin dimokuraɗiyya, dangantaka tsakanin bangaren zartarwa da majalisun dokoki tana taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da shugabanci a tsakanin al’umma. A galibin kasashe masu bin tsarin na dimokuraɗiyya, ’yan majalisa kan kasance masu wakiltar al’umma da kare muradunta, da sa ido da kuma bayar da shawarwarin da suka dace ga bangaren zartarwa domin ci-gaban kasa. Sai dai a Najeriya, a wasu lokutan akan zargi ’yan majalisa da zama ’yan-amshin-Shata. Ko me ya sa haka? Shin yaya ya kamata dangantaka ta kasance a tsakanin bangaren zartarwa da majalisar dokoki a tsarin mulkin dimokuraɗiyya? NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC DAGA LARABA: “Abba Al-Mustafa Ba Shi...
Kamfanin dillancin labarun Sputnik na Rasha ya sanar da cewa; sojojin kasar sun harba makamai masu linzami samfurin Iskander akan manyan akwatunan dakon kaya 100 dake dauke da makamai a tashar jiragen ruwa ta Odessa. Sanarwar ta kuma kunshi cewa makaman da sojojin na Rasha su ka tarwatsa sun hada kananan jiragen ruwa na yaki na kai farmaki da ba su da matuki, jiragen sama marasa matuki, da kuma albarusai. Haka nan kuma harin ya shafi manyan dakunan ajiye makamai a cikin tashar jiragen ruwan na Odessa. Sanadiyyar wannan harin harshen wuta ya tashi wanda ya dauki lokaci yana ci. A gefe daya an yi musayar fursunoni a tsakanin sojojin Rasha da kuma na Ukiraniya wanda shi ne mafi girma...

Hunan Ya Ruwaito Samuwar Karin 6.3% Na Kayayyakin Da Ake Fitarwa Zuwa Afirka Tsakanin Janairu Da Afrilu
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan Harkokin wajen kasar Omman ya bada sanarwan cew za’a gudanar da tattaunawa zagaye na 5 tsakanin Iran da Amurka kan shirin Iran na makamshin nukliya a ranar 23 gawatan Mayun da muke ciki a birnin Roma nakasar Italiay. Tashar talabijin ta Presstv a nnan Tehran ta ce Har yanzun ba’a ji tabakin kasashen biyu ba bayan wannan sanarwan. Sai dai kafin haka Iran tace tana tunanin dakatar da halattan taron saboda yadda jami’an gwamnatin kasar Amurka suka bayyana cewa duk wata yarjeniya da Iran sai ta hada da hana ta tace Uranium. Amma iran ta dage kan cewa ba zata bar hakkinta wanda yarjeniyar NPT ta bata ba na tashe Uranium karkashin kula na hukumar IAEA ba.
A yau Jumma’a, babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya yi hadin gwiwa da kawancen gidajen rediyon Turai na EBU wajen gabatar da rahoton Report ITU-R BT.2550, wato fasahar tsara shirye-shiryen bidiyo da rediyo ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta 5G, a shafin intanet na kwancen harkokin sadarwa na duniya wato ITU. Lamarin da ya nuna cewa, CMG ya taka muhimmiyar rawa a fannin tsara shirye-shirye masu inganci, ya kuma kai matsayi na gaba a fannin fitar da fasahohin tsara shirye-shiryen zamani masu inganci. (Mai Fassara: Maryam Yang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Jigawa ta ce ta dauki mataki mai muhimmanci wajen tabbatar da kiyaye ka’idojin aikin jarida ta hanyar kafa Kwamitin Ladabtarwa da kuma Kwamitin Ilimi da Horaswa. A cikin wata sanarwa da Sakatariyar kungiyar, Kwamared Aisha Abba Ahmed ta fitar, ta bayyana cewa Kwamared Sabo Abdullahi Guri ne zai jagoranci Kwamitin Ladabtarwar tare da Kwamared Mati Ali, da Dr. Musa Idris Barnawa da Yusuf Sulaiman a matsayin mambobi, yayin da Muhammad Askira Musa zai kasance Sakataren kwamitin. Sanarwar ta bayyana cewa an dora wa kwamitin alhakin tabbatar da bin ka’idojin aikin jarida, warware matsalolin rashin ladabi ko sabawa doka cikin aikin, da kuma tabbatar da gaskiya da rikon amana a aikin jarida a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Peng Liyuan Da Uwar Gidan Shugaban Kasar Brazil Sun Ziyarci Babban Zauren Nuna Fasahohin Nishadantarwa Ta Kasar Sin
A jiya ne uwar gidan shugaban kasar Sin Peng Liyuan da matar shugaban kasar Brazil Rosângela da Silvaa wadda ta rako mai gidanta a ziyarar da yake yi a kasar Sin, suka ziyarci babban zauren nuna fasahohin nishadantarwa ta kasar Sin, inda suka kalli abubuwan dake ciki, tare da kallon wasan opera da wasu wake-waken Sin da Brazil. Peng Liyuan ta bayyana cewa, Sin da Brazil suna mu’amala da juna a fannin al’adu, kuma jama’ar kasashen biyu suna ta kara fahimtar juna, da sada zumunta mai zurfi. A nata bangare kuwa, Madam Rosângela ta jinjinawa nasarorin ci gaba da kasar Sin ta samu da kuma yadda ake raya al’adun kasar. Tana fatan kara sa kaimi ga yin mu’amala a tsakanin...
A jiya Talata sojojin HKI su ka kai wani mummunan hari akan asibitin Gaza na “Turai” da kuma zagayensa da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da kuma jikkata wasu da dama. Sojojin mamayar sun yi amfani da jiragen sama wajen kai wadannan munanan hare-haren akan Asibitin da ake kir ana turai, da kuma gefensa a kudu maso gabashin birnin Khan-Yunus. Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; jiragen saman na HKI sun kai hare-haren ne ta hanyar harba makamai masu linzami akan bangare da kuma kula da matsalolin gaggawa na asibitin da kuma bangaren dake kula da asibitin da gyara abubuwan da su ka baci. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wasu hare-haren a...
Ya ce: “A yau ni ne Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya. Ba kawai ɗan watsa shirye-shirye ba ne ni, ni ne babban mai magana da yawun gwamnatin Nijeriya. “Don haka za ka ga yadda burin da ake ganin kamar an kashe shi shekaru da dama da suka wuce, ya dawo ya amfanar.” Ya ce kafin ya zama minista, ya mallaki tashar rediyo da talbijin har ma da gidan jarida. Ministan ya buƙaci matasa da kada su yi watsi da burin su ko da ba sa ganin damar cimma buƙatar su. Ya ce shauƙin sa ne yake motsa shi wajen yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya ta hanyar ƙarfafa fahimtar kafofin sadarwa. Idris ya kuma bayyana cewa...
A sanarwar da mataimaki na musamman ga ministan kan harkar yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ya bayyana cewa a jawabin sa na buɗe taron, ministan ya nuna jin daɗin sa kan yadda haɗin kai ke ƙaruwa a tsakanin manyan masu ruwa da tsaki a fannin yaɗa labarai a cikin gwamnatin. Ya ce haɗin kan da daidaiton manufa sun ƙara inganta isar da saƙo da kuma fahimtar manufofin gwamnatin Tinubu. Ministan ya yaba da yadda Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take aiki tare da shugabannin hukumomin yaɗa labarai da kuma mataimakan shugaban ƙasa a ɓangaren watsa labarai da dabarun sadarwa. Ya ce wannan haɗin gwiwa ya taimaka wajen tabbatar da cewa saƙonnin gwamnati suna...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa gwamnatin JMI ba zata amince da tattaunawa tare da kara tsuge takunkuman tattalin arziki na koli da aka dorawa kasar ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa yin haka sabawa dokokin kasa da kasa ne. Har\ila yau take hakkin mutanen kasar Iran ne da kuma shigar da shakku a cikin tattaunawar da Amurka take yi da kasar. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta bada sanarwan kakabawa mutanen da kamfanoni 7 wadanda suke mu’amala da kasar Iran a kasashen UAE da Turkiya saboda sayan danyen man kasar Iran da kuma sinadaran manfetur na kasar. Har’ila...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta baiwa ma’aikatan jihar tabbacin ci gaba da jajircewa wajen kyautata jin dadin su da kuma kare hakkokinsu. Gwamna Nasir Idris wanda ya ba da wannan tabbacin a lokacin da yake jawabi ga ma’aikata domin bikin ranar watan Mayu a Birnin Kebbi, ya jaddada cewa ma’aikata aminai ne masu kima wajen ci gaban jihar Kebbi, kuma su kasance masu ruwa da tsaki da ba za a yi watsi da su ba. Gwamna Idris, wanda ya bayyana bikin ranar Mayu a matsayin wani muhimmin lokaci, ya yabawa ma’aikatan bisa jajircewarsu da irin gagarumar gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban jihar. “Kwazonku da jajircewarku sune kashin bayan tattalin arzikinmu. Ina yaba muku kan kokarinku na...
Iran ta sanar da cewa an dage tattauanwa ta karo na hudu da aka shirya gudanarwa tsakaninta Washington a ranar Asabar mai zuwa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ne ya sanar da manema labarai da hakan a yammacin yau Alhamis yana mai cewa an sauya ranar da za a gudanar da tattaunawar ta gaba tsakanin Iran da Amurka da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 3 ga watan Mayu a birnin Rome na kasar Italiya. Esmail Baghai ya bayyana cewa, an dauki wannan matakin ne bisa bukatar ministan harkokin wajen kasar Oman, kuma Za a sanar da sabon lokaci nan gaba. Baghaei ya jaddada aniyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na yin amfani da hanyar diflomasiyya wajen kare muradun al’ummar...
Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai lokacinda kasar take cikar shekaru 80 da samun nasara a kan sojojin Nazi a karshen yakin duniya na II a Abuja. Andrey Podelyshev yace idan kasar Ukraine ta zami da tsagaita wuta a cikin wadannan kwanaki ba laifi, amma kuma idan sojojinta sun kai wani hari a kan rasha ta zata rama da hare-hare masu tsanani. Shugaban Volodimir Zelesky dai tuni ya yi watsi da...
Kasar Sin ta cimma nasarar harba sabon tauraron dan’adam na ayyukan sadarwa mai suna Tianlian II-05, daga tashar harba kumbuna ta Xichang dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar. An harba tauraron ne da karfe 12 saura mintuna 6 na tsakar daren jiya Lahadi agogon Beijing, ta amfani da rokar Long March-3B, kuma tuni ya shiga da’irarsa kamar yadda aka tsara. Tauraron zai rika samar da hidimomin musayar bayanan sadarwa ga kumbunan sama jannati, irin su kumbuna masu dauke da ‘yan sama jannati, da tashar binciken sararin samaniya, domin nasarar ayyukan taurarin dan’adam marasa nisa da doron duniya, da taurarin dan’adam masu taimakawa aikin harba kumbuna. Wannan ne karo na 572 da aka yi amfani da roka samfurin Long...

A Karon Farko A Tarihi Adadin Lantarki Da Sin Ke Iya Samarwa Ta Karfin Iska Da Hasken Rana Ya Zarce Wanda Ake Iya Samarwa Ta Amfani Da Dumi
Sashen masana’antun samar da sabbin makamashi na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya bayan nan, a gabar da ake ta aiwatar da managartan matakai na bunkasa tattalin arziki ba tare da fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi ba. Tun daga shekarar 2013, adadin kayayyakin samar da lantarki daga karfin iska da aka kafa a Sin sun ninka har sau 6, yayin da na samar da lantarki daga karfin rana suka ninka sama da sau 180. Ya zuwa yanzu, sabbin kayayyakin samar da lantarki ta wannan hanya da ake kafawa duk shekara a kasar Sin, sun kai kaso sama da 40 bisa dari kan na daukacin kasashen duniya, adadin da ya yi matukar ba...
Gwamnaton kasar Kongo Democradiyya ta bada sanarwan haramta jam’iyyar Josept Kabila tsohon shugaban kasar. Shafin yanar gizo na labarai, Africa News ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar tana bada wannan sanarwan. Labarin ya kara da cewa, Josept Kabila ya shugabanci kasar ta kwango har zuwa shekara ta 2019, karkashin Jam’iyyarsa ta ‘the People’s Party for Reconstruction and Democracy (PPRD). Daga baya Kabila ya dorawa kansa gudun hijira zuwa kasashen waje a shekara ta 2023. Bai kuma sake dawowa ba sai ranar jummar da ta gabata. Kabila dan shekara 53 a duniya, ya shigo kasar kongo daga kasar Rwanda, sannan ya je ya gana da shuwagabannin kungiyar M23 a birnin Goma, inda daga nan suke ikonsu a kan yankunan...
Kididdigar da hukumar kula da harkokin makamashi ta kasar Sin ta fitar a yau Lahadi ta yi nuni da cewa, zuwa karshen watan Maris din shekarar da muke ciki, yawan wutar lantarki da kasar Sin ke iya samarwa ya kai kilowatt biliyan 3.43, adadin da ya karu da kaso 14.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Daga cikin wutar lantarkin da ake samarwa, yawan wutar lantarki da ake iya samarwa bisa makamashin hasken rana ya kai kilowatt miliyan 950, adadin da ya karu da kaso 43.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kazalika, a sa’i daya kuma, yawan wutar lantarki da kasar ke iya samarwa bisa karfin iska ya kai...
’Yan ta’addar ISWAP sun tarwatsa wata gada da ta haɗa garin Ngirbuwa da garin Goneri a Ƙaramar Hukumar Gujiba da ke Jihar Yobe. Wannan na zuwa ne ƙasa da mako guda da ‘yan ta’addan suka lalata gadar nan ta Mandafuna da ta haɗa garin Biu da Damboa a Jihar Borno. JAMB ta sauya ranar soma jarrabawar bana Manyan jami’an gwamnati sun halarci auren ’yar tsohon Gwamnan Bauchi Majiyar leƙen asiri ta shaida wa Zagazola Makama cewa harin ya afku ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ta hanyar amfani da wani bam wajen lalata sauran sassan gadar. Wannan aikin ta’addanci ya kawo cikas ga zirga-zirga tsakanin al’ummomin biyu da ma sauran al’ummomin yankin,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Zulum ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki da su maida hankali wajen samar da damammaki ga matasa a arewacin Nijeriya. A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Sarakunan Arewa kuma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, taron da aka yi a Jihar Borno an yi shi ne domin karfafa hadin kan jihohin Arewa da kuma tattaunawa kan halin da yankin ke ciki domin tallafa wa shugabannin siyasa wajen magance matsalolin da ke addabar Arewa. Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) da babban hafsan tsaro (CDS) da babban sufeton ‘yansanda (IGP) duk sun samu wakilci a taron sarakunan. Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban kungiyar gwamnonin jihohin Arewa...

Sin Ta Bukaci Amurka Da Ta Dakatar Da Matakin Kare-Karen Harajin Fito Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Duba da cewa, ko a yanzu ma bisa harajin da Amurka ta kakaba, kayayyakin Amurka ba za su iya samun karbuwa a kasuwannin kasar Sin ba, idan har Amurka ta kara yawan haraji kan hajojin Sin, bangaren Sin zai yi watsi da hakan. Sai dai kuma, idan Amurka ta nace wajen neman illata moriyar kasar Sin, Sin din za ta aiwatar da matakan ramuwa, tare da tunkarar wannan yaki har karshensa. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Don haka bangaren Sin ya kalubalanci kasar Amurka da ta gyara kuskurenta cikin hanzari, ta soke dukkan matakan kara buga harajin kwastam kan kasar Sin daga bangare daya, kana ta hau teburin shawarwari tare da kasar Sin, don daidaita matsalolinsu bisa tushen girmama juna. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Muhimmin jigon dabarar raya yankunan a tare shi ne, bude kofar cimma zamanantarwa da samun wadata na bai daya ga dukkan jama’a. (Fa’iza) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo. Zanga-zangar da kungiyar ‘Take-it- Back Movement’ da kungiyoyin fararen hula suka shirya a fadin kasar ya zo daidai da ranar bikin ranar ‘yansanda ta kasa a dandalin Eagle Square da ke Abuja. Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci LEADERSHIP ta tuna cewa, hukumomin ‘yansanda sun yi gargadi...
Jami’an rundunar ‘yansandan jihar Ribas a ranar Litinin sun harba tiyagas (barkonon tsohuwa) kan masu zanga-zangar lumana don nuna adawa da abin da suka kira rashin shugabanci nagari a kasar. Masu zanga-zangar karkashin kungiyar ‘Take It Back’ sun kuma gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas da kuma yadda ‘yansandan Nijeriya ke amfani da dokar leken asiri ta yanar gizo ba ta yadda ya dace ba. Fedpoly Bauchi Ta Sanya Na’urorin Ɗaukan Hoto ‘CCTV’ Don Daƙile Satar Jarabawa Da Inganta Tsaro Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci Sun zargi ‘yansanda da yin amfani da dokar aikata laifuka ta yanar gizo wajen kai hari ga masu fafutukar kare hakkin...
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Abdallah Usman zai jagoranci kungiyar a karon farko cikin makonni 5 a wasan da Pillars zasu kara da Haertland Owerri. Wasan na mako 32 a gasar Firimiya ta Nijeriya da za a buga a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a birnin Kano, zai zama wani mataki da Abdallah zai sake kwantar da hankalin magoya bayan ƙungiyar bayan hatsaniyar da su ka samu a ƙarshen watan Fabrairu. Me Dakatarwar Da Pillars Ta Yi Wa Usman Abdalla Ke Nufi? Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah Pillars na mataki na 8 da maki 44 a wasa 31 da su ka buga, yayinda Heartland Owerri ke matsayi na...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar na farko na Hukumar Fasahar Sadarwa da inganta Tattalin Arzikin ta fasahar zamani ta Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse. Kafin nadin nasa, Dr. Muhammad Hassan shi ne shugaban hukumar Fasahar Sadarwa da Kimiyya ta Jigawa, wato Galaxy ITT. Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa sabo shugaban hukumar ya sami digirinsa na farko a fannin Lissafi daga Jami’ar Bayero, Kano, a shekarar 2008. Daga bisani, ya samu digiri na biyu a fannin Kimiyyar Kwamfuta daga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Afirka (AUST), Abuja, a shekarar 2011, sannan...
Jagunlabi ya ce za a gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa wuraren shakatawa domin samar da kudin shiga wanda hakan zai haifar bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a fannin fasaha da nishadi. Ya bayyana cewa, aikin zai mayar da hankali ne wajen maidowa tare da kiyaye wuraren tarihi, kayayakin tarihi, da inganta ilimin al’adu da inganta sana’o’in cikin gida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A kasar Jordan gwamnatin kasar ta bada sanarwan cewa a gobe Litinin ce za’a gudanar da bukukuwan sallah karama bayan azumun watan Ramadan na kwanaki 30. Muftin kasar ta Jordan Ahmed Hasanat a lokacinda yake bada sanarwan a jiya Asabar yace, ranar Litinin 31 ga watan Maris, ita ce ranar Sallah daya ga watan shawwal shekara ta 1446 Kmariya. Kasashen Saudia, Qatar, UAE, Kuwait, Bahrain, Yemen, da kuma Palestine sun bada sanarwan cewa yau Lahadi ce sallah karama a kasashensu. Sai kuma kasashen Oman, Siriya da sun bayyana cewa gobe litinin ne salla karama. A tarayyar Najeriya ma, sultan Sa’ad Abubakar na sokoto ya bada sanarwan sallah a yau Lahadi. Majalisar koli ta al-amuran musulunci a Najeriya, karkashun shugabancin sultan...
Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya a birnin Kano sun haramta daban da aka saba yi a karshen watan azumi a birnin. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Jami’an tsaron kasar suna bada wannan sanarwan ne bayan da sarki na 15 Wato Aminu- Ado Bayero ya bada sanarwan janye daban da ya shirya gabatarwa a kwanakin salla Karamah. Shugaban Jami’an tsaron ya bayyana haka ne a wani taron yan jarida da ya gabatar a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa baza su amince da gudanar da taron Durba a karamar sallah a wannan shekara ba. Kakakin yansada na jihar Kano Haruna Kiyawa, ya sanya sanarwan a shafinsa na Facebook. Kafin haka aranar 18 ga watan Maris da muke ciki...
A yayin da watan Ramadan ɗin wannan shekara yake bankwana, ga abubuwan da malamai suka bayyana game da fitar da Zakkar kono, wato Zakatul Fidr ga duk wanda ke da hali. Sahabi Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar Zakkar kono domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.” Majalisa ta buƙaci a rage kuɗin data don sauƙaƙa wa ’yan Najeriya Ban taɓa fuskantar tsangwama a Kannywood ba — Prince Aboki Daga cikin hikimar bayar da ita, akwai sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abin da za su ci a lokacin Ƙaramar Sallah. Yadda ake fitarwa Mutum zai fitar wa kansa da kuma waɗanda...

Karfin Lantarki Da Tashoshi Masu Amfani Da Makamashi Mai Tsafta Ke Samarwa A Sin Ya Kai Kilowatt Biliyan 2
A karon farko, karfin lantarkin da tashoshin samar da lantarki da ba sa amfani da man fetur da kwal da Sin ta kafa suka samar, ya zarce kilowatt biliyan 2 zuwa karshen watan Fabrairu. Wannan na kunshe ne cikin sabon rahoton da majalisar kula da lantarki ta kasar Sin ta fitar, wanda ya ce adadin shi ya dauki kaso 58.8 na baki dayan lantarkin da tashoshin samar da lantarki na kasar Sin ke samarwa. Karfin lantarki da tashoshin samar da lantarki daga sabon makamashi da suka hada da iska da na hasken rana ke samarwa, ya kai kilowatt biliyan 1.46 zuwa karshen watan da ya gabata, adadin da ya dauki kaso 42.8 na jimilar lantarkin da kasar ke samarwa. (Mai...

Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin da Talata a matsayin hutun sallaGwamnati Ta Ayyana 31 Ga Maris Da 1 Ga Afrilu A Matsayin Ranakun Hutu Don Bukin Eid-el-Fitr Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 31 ga Maris, da Talata, 1 ga Afrilu, a matsayin ranakun hu
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300 a Yobe Tsohon hadimin gwamnan Kano, Abdullahi Tanka Galadanci, ya rasu Ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan cikin nasara, tare da yin kira a gare su da su ci gaba da halaye nagari da suka koya a watan. Haka kuma ya jaddada muhimmancin soyayya, yafiya, da haɗin kai wajen gina al’umma. Tunji-Ojo, ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan...
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG ya gabatar da taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take gabatarwa ga duniya” a ran 20 ga watan nan da muke ciki a kasar Rasha. Kuma Shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Jakadan Sin dake kasar Rasha, Zhang Hanhui da wakilan bangaren siyasa da ba da ilmi da yada labarai na kasar Rasha sun halarci taron don tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen biyu da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha da musanyar al’adu da kuma hadin kan kafofin yada labarai da sauransu. Wakilai na Rasha sun hada da Andrey Denisov, mataimakin shugaba na farko na kwamiti...
A yau Lahadi, kwararren masanin tattalin arziki dan kasar Amurka Jeffrey Sachs ya bayyana cewa, matakan kariyar cinikayya da Amurka ke aiwatarwa babban kuskure ne. Jeffrey wanda ya halarci dandalin bunkasa kasa na Sin na shekarar nan ta 2025 a birnin Beijing, ya kara da cewa Amurka na kara karkata ga salon kariyar cinikayya karkakin manufofinta na tattalin arziki. Sai dai a daya hannun, kasar Sin na kara fadada bude kofarta. Ya ce Amurka na ingiza salon rufe fasahohinta, yayin da Sin ke kara gabatarwa duniya da fasahohin ci gaba. Dukkanin wadannan na nufin Sin za ta zamo mai cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin duniya a shekaru masu zuwa. Daga nan sai mista Jeffrey ya nuna damuwa game da...
Fitaccen jarumi a Masana’antar Kannywood Sadik Sani Sadik ya ce shi ba fadakarwa yake yi a fim ba, inda ya ce neman kuɗi kawai yake yi. Jarumin ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Gidan Rediyon Freedom, inda a ciki yake cewa ba tarbiyya yake koyarwa ba, ballantana a ce yana bata tarbiyyar. Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas A cewarsa, “Ni ban ce ina fadakarwa ba. Ni Sadik Sani Sadik ban ce ina fadakarwa ba. Ban ce ina tarbiyyantarwa ba. “Tarbiyya ana ba yaro daga gida ne, fadawarka kuma malamai ne ke yi. Ni ba mai fadakarwa ba ne. Ni mai neman kudi ne....

Jami’ai: Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Na Kara Kuzarin Ci Gaban Kasashe Masu Tasowa Da Karfafa Zamanantarwa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar dokokin jihar Kano ta wanke Arc. Ibrahim Yakubu Adamu a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jiha. A yayin aikin tantance kwamishinonin, ya jaddada mahimmancin kiyaye babban tsarin ga birane da yankunan karkara. Ya kuma yi alkawarin bayar da gudunmowarsa wajen sauke nauyin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora masa. Adamu wanda a baya ya taba rike mukamin Manajan Darakta na Hukumar Kula da Tsare-Tsare Birane ta Jihar Kano (KNUPDA), ya bayyana jin dadinsa ga majalisar a yayin zaman majalisar. Shugaban majalisar Jibril Ismail Falgore ya bukaci Adamu da ya kara samun nasarori a KNUPDA tare da yi masa fatan Alheri a sabon mukaminsa. Nadin Adamu ya yi daidai da...