An Biya Diyyar Naira Miliyan 277 Ga Wadanda Aikin Ginin Masallacin Gumel Ya Shafa
Published: 7th, August 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta biya iyalai 14 da aikin sake gina Babban Masallacin Gumel ya shafa kudaden diyya da suka kai Naira miliyan 277 da dubu 44.
An gudanar da bikin bayar da takardun cekin kudin ne a Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmad Muhammad Sani, tare da halartar masu rike da sarautu, da shugabannin al’umma da manyan jami’an gwamnati.
Da yake jawabi yayin bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, wanda Babban Sakataren Harkokin Gudanarwa da Kudi na Ofishinsa, Alhaji Abdullahi Sa’idu, ya wakilta, ya shawarci iyalan da su yi amfani da kudaden ta hanya mai amfani wajen gina sabbin gidajensu tare da rungumar sauyin wurin zama cikin hakuri da tawakkali.
Malam Bala Ibrahim ya jaddada cewa an aiwatar da tsarin biyan diyyar bisa adalci da gaskiya domin tabbatar da cewa kowa ya samu hakkinsa yadda ya dace.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Gumel, Hon. Muhammad Gako, ya yabawa Gwamna Malam Umar Namadi bisa wannan karamci, yana mai tabbatar da goyon bayan karamar hukumar wajen nasarar aikin sake gina masallacin.
An bayar dda kudaden diyyar ne domin rage wa iyalan da abin ya shafa radadin sauyin da suka fuskanta tare da bayar da damar ci gaba da aikin sake gina masallacin cikin lumana.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Sanar Da Matakan Fara Bayar Da Ilimin Kafin Firamare Kyauta
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp