Hukumar Alhazai ta Jigawa Ta Shirya Bitar Ga Malaman Bita na Kananan Hukumomi 27
Published: 17th, April 2025 GMT
A kokarin ta na ci gaba da inganta ayyukan ta, hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta gudanar da bitar sanin makamar aiki ga malaman bita na kananan hukumomin jihar 27.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo wanda ya jagoranci gudanar ta taron a shelkwatar hukumar dake Dutse, ya ce an shirya taron ne domin nusar da malaman ayyukan daya rataya a kawunan su domin cimma burin da aka sanya a gaba.
A cewar sa, hukumar zata sanya malaman bitar a cikin kwamitocin hukumar daban-daban domin samun nasarar gudanar da aikin hajjin bana.
Yana mai cewar, a matsayin su na jagororin maniyata aikin hajji, akwai bukatar su kasance da maniyata tare da fadakar dasu akan aikin hajjin da zasu gudanar a kasa mai tsarki.
Alhaji Ahmed Umar Labbo
Alhaji Ahmed Umar Labbo, yace tuni hukumar ta karbi fasfo na maniyata kuma sun shigar dasu cikin runbun yin biza.
Kazalika, Labbo yayi nuni da cewar, wannan shine karon farko da gwamnatin jihar ta dauki nauyin malaman bita zuwa aikin hajjin bana domin hidimtawa maniyatan aikin hajjin bana.
A nasa tsokacin, Daraktan fadakarwa da wayar da kai na hukumar, Alhaji Abdullahi Aliyu, yayi jawabi ga malaman bitar kan nauyin da ya rataya a kawunan su.
Yana mai kira a gare su dasu sadaukar kai domin taimakawa maniyyata a kowanne fannin da hukumar ta umarce su domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Wasu daga cikin malaman bitar da suka zanta da Radio Nigeria,sun yabawa Gwamna Umar Namadi da shugaban hukumar alhazai ta jihar, Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa amincewa da daukar nauyin su domin jagorantar maniyatan aikin hajjin wannan shekarar.
Usman Mohammed Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Bitar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo
এছাড়াও পড়ুন:
An rufe makarantun Filato saboda matsalar tsaro
Hukumar Ilimi ta Matakin Farko ta Jihar Filato (PSUBEB) ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandire na gwamnati a faɗin jihar sakamakon fargabar tsaro da ta taso a kwanakin nan.
A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce za a rufe ƙananan makarantun sakandare tun daga Asabar, 22 ga Nuwamba, 2025, yayin da makarantun firamare za a rufe su daga Litinin, 24 ga Nuwamba, 2025.
H-JRBDA ta yi alƙawarin magance ambaliyar ruwa a Jigawa Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jiharWannan mataki na zuwa ne bayan sace ɗalibai a wasu makarantu da ke jihohin Kebbi da Neja a ‘yan kwanakin da suka gabata, abin da ya tayar da hankalin iyaye da hukumomi.
PSUBEB ta sanar da cewa rufe makarantun mataki ne na wucin-gadi domin daƙile duk wata barazana da ka iya tasowa, tare da tabbatar wa jama’a cewa gwamnati na ɗaukar lafiya da tsaron ɗalibai da muhimmanci.
Hukumar ta buƙaci Hukumomin Ilimi na Kananan Hukumomi, shugabannin makarantu da shugabannin al’umma da su ba da cikakken haɗin kai wajen aiwatar da umarnin, tare da zama masu kula da duk wata alama ta rashin tsaro a yankunansu.