Nijeriya Na Asarar Tiriliyan 3.2 Sanadiyyar Watsi Da Noma A Gandun Daji
Published: 8th, August 2025 GMT
Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji
“Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya, don sayarwa”, in ji Ibrahim.
Kazalika, Ibrahim wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar manoma ta ƙasa (AFAN) ya jaddada cewa; idan aka samu goyon bayan ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci da kuma goyon bayan sauran hukumomin, hakan zai bayar da damar gyara Gandun Dazukan da ake da su, musamman wajen kare su daga kwararowar hamada.
Shugaban ya ƙara da cewa, akasarin noman gargajiya a ƙasar nan, ana yin sa ne a karkara, inda manoma a karkara ke shuka ‘ya’yan itatuwa na kayan marmari a Gandun Dazukan ƙasar.
Ya ci gaba da cewa, mazauna karkara na yin amfani da Gandun Dazukan ƙasar wajen yin kiwon dabbobi, wanda hakan ke ƙara bunƙasa ayyuka a tsakanin mazauna karkarar.
Shugaban ya yi nuni da cewa, gudanar da ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar kawo ci gaba ga Nijeriya tare da samar da ɗauki ga marasa ƙarfi, wanda kuma hakan zai bai wa mata da matasa damar jawo su a jiki, domin tafiya tare da su.
A cewarsa, har yanzu ba a makara ba, domin kuwa za a iya yin amfani da Gandun Dazukan ƙasar wajen gudanar da ayyukan noma.
Shugaban ya ci gaba da cewa, hakan zai ƙara taimaka wa a samar da wadataccen abinci a ƙasar da kare kwararowar hamada da kuma annobar sauyin yanayi.
Ya bayyana cewa, za a iya cimma hakan ne kaɗai idan mahukunta a ƙasar suka samar da kyakywan tsari tare da gangamin wayar da kan jama’a da kuma zuba hannun jari
a fannin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Fish farming
এছাড়াও পড়ুন:
Birtaniya za ta amince da ƙasar Falasɗinu
Ƙasar Birtaniya a wannan Lahadin za ta amince a hukumance da kafa ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila za ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawa An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a EnuguTun a watan Yulin wannan shekarar Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce zai goyi kafa ƙasar Falasɗinu yana mai gindaya wa Isra’ilar sharaɗin yanke wannan shawarar.
Starmer ya ce zai amince da ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ilar ba ta ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas ba kafin babban taron Majalisar Dinkin Duniya na watan Satumba.
Kafafen yada labarai sun ruwaito cewa, Starmer zai yi jawabi ga al’umma kan matsayarsa, gabanin babban taron zauren majalisar Dinkin Duniya, inda ƙasashe 10 ciki har da Faransa za su amince da kafa ƙasar ta Falasɗinu.
Sai dai Amurka da Isra’ila sun soki matakin, suna bayyana shi a matsayin saka wa Hamas duk da harin da ta kai na ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Su ma ƙasashen Portugal da Canada da Australia sun ce za su amince da ƙasar Falasɗinun a cikin wannan mako.
Daga gobe Litinin ce sama da shugabannin ƙasashe 140 ne za su hallara a birnin New York domin taron shekara-shekara na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Matsalar jinƙai da ta addabi yankin Falasɗinu za ta kasance a kan gaba a tattaunawar da za ta gudana a taron na bana.
Shugaba guda da ba zai halarci taron a zahiri ba shi ne shugaban Falasɗinawa, Mahmud Abbas, wanda Amurka ta hana biza tare da waɗansu jami’ansa.
A karo na musamman, babban zauren ya kaɗa ƙuri’a a ranar Juma’a domin bai wa Abbas damar gabatar da jawabi ta hanyar bidiyo, yayin da jakadan Falasɗinu zai wakilce shi a cikin ɗakin taron.