Aminiya:
2025-11-27@21:56:13 GMT

Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr

Published: 10th, August 2025 GMT

A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League.

Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi.

MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da Pakistan

Martinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara.

Kafin haka, ya shafe shekaru bakwai yana murza leda a Real Sociedad bayan fitowa daga makarantar horas da kwallon kafarta, sannan ya shafe shekaru shida a Bilbao.

Martinez, wanda ya buga wa kasar Spain wasanni 21 tsakanin 2013 zuwa 2023, ya koma Al-Nassr wadda ta kare a mataki na uku a gasar Saudi Pro League a kakar da ta gabata, wadda Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa mafi zura kwallaye da kwallaye 25.

AFP

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Barcelona Inigo Martinez

এছাড়াও পড়ুন:

An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina

Hukumar kula da makarantun firamare da sakandare ta Jihar Katsina ta sanar da sake buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarabawar zangon farko na shekarar karatu.

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Sani Danjuma Suleman, ya fitar a madadin Shugaban hukumar, ta ce makarantun firamare, sakandiren je-ka-ka-dawo da kuma makarantu masu zaman kansu za su buɗe daga yau Talata domin ci gaba da jarabawar zangon farko.

Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran makarantun kwana za su ci gaba da kasancewa a rufe har sai lokacin da hali ya ba da dama.

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Gwamnatin Katsina ta rufe makarantun bayan ƙaruwar hare-haren sace ɗalibai da masu garkuwa da mutane suka sake farfaɗowa da su a wasu yankuna.

Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne da nufin daƙile matsalar tsaro da kuma sa ido a kan al’amura.

A ƙarshe, hukumar ta roƙi haɗin kan iyaye da masu kula da ɗalibai domin su ci gaba da ba wa shirin goyon baya tare da ƙarfafa ɗaliban su dage da karatu wajen rubuta jarabawar da suke yi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos
  • Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
  • Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa
  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya
  • Reuters: Kungiyar Likitoci Ba Da Iyaka Ba Ta Fice Daga Asibitin Darfur Bayan Bude Wa Ma’aikatanta Wuta
  • Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai