Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore
Published: 7th, August 2025 GMT
Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Kasa sun kutsa inda ake tsare dan gwagwarmaya Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da karfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba. Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da karfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a kokarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An Zargin Akantan jihar Nasarawa Da Shiga Harkokin Siyasa
Kungiyar masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa reshen jihar Nasarawa ta kalubalanci kungiyar tabbatar da gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari (NS-TA&G), da su tabbatar da zargin nuna son kai wajen sauke nauyin da babban Akanta Janar na jihar, Ahmed Musa Mohammed ke yi.
Ko’odinetan kungiyar na jiha Abimiku Dangana Solomon ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga wani jawabi da Mista Lazarus Salaki, ko’odinetan kungiyar NS-TA&G2 na jihar ya yi a wani taron manema labarai da aka gudanar a garin Lafia babban birnin jihar.
Mista Abimiku Dangana ya ce, hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan bai hana masu rike da mukaman gwamnati da ma’aikatan gwamnati shiga harkokin siyasa da shiga jam’iyyun siyasa ba.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa, shari’ar INEC da Ahmed Musa inda mai shari’a Ayoola da Justice Mohammad Uwais suka jaddada cewa dokokin ma’aikatan ba za su iya maye gurbin tanadin tsarin mulki ba.
“Muna kalubalantar Hukumar NS-TA&G2 da ta ba da shaidar nuna fifiko na musamman da ake zargin an yi mata ko kuma an yi kasa a gwiwa wajen sauke nauyin da Akanta Janar na Jiha ke yi.
Idan za a iya tunawa wata kungiyar da abin ya shafa a karkashin Mista Lazarus Salaki, ta yi kira ga Mista Musa Ahmed Mohammed, Akanta Janar na Jihar Nasarawa ya yi murabus, bisa zarginsa da hannu a harkokin siyasa yayin da yake rike da wani mukami mai muhimmanci.
Kungiyar ta kuma bayar da misali da umarnin da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Mohammed Uban-doma Aliyu ya bayar a ranar 16 ga Afrilu, 2024, inda ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa masu burin shiga zabe da su yi murabus ko kuma su dakatar da harkokin siyasa har sai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana matsayarta.
Mista Lazarus Salaki ya yi zargin cewa, duk da wannan umarnin, wasu da aka nada sun ci gaba da yakin neman zabe da kuma gudanar da taron siyasa yayin da suke kan mukamansu.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.