Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza
Published: 11th, August 2025 GMT
Sojojin mamayar Isra’ila sun harba wata mugunyar ‘karfin wuta’ da jiragen saman yaki kan yankin kudancin Gaza
Bayan tsakar dare ne jiragen yakin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da luguden wuta a kudancin birnin Gaza.
Cibiyar yada labaran Falasdinu ta nakalto majiyoyin da ta bayyana a matsayin na cikin gida na cewa: Jiragen saman sojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-haren wuce gona da iri, inda suka harba makamai masu linzami sama da 20 cikin ‘yan mintuna a kudancin mahadar Al-Musalaba da Dawla da kuma kusa da masallacin Ali, inda suka nufi kudu.
Wakilin cibiyar ya ruwaito cewa, galibin hare-haren sun fi karkata ne a kan titin 8 da ke kudancin Gaza.
Wadannan hare-haren dai na zuwa ne a daidai lokacin da barazanar da sojojin mamaya ke yi na kaddamar da wani gagarumin farmaki a kan birnin na Gaza ke kara ta’azzara, da nufin kwace iko da birnin da kuma raba mazauna birnin da tilastawa kauracewa gidajensu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza August 11, 2025 Shugaban Iran: Dole ne duniya ta kawo karshen laifukan yakin Isra’ila a Gaza August 11, 2025 Israila Ta Kashe ‘Yan Jarida 4 A Harin Da Ta Kai Kan Tantinsu A Gaza August 11, 2025 Iran: Ba a yanke wani abu game da tattaunawa da Washington ba August 11, 2025 Kwamitin Tsaro ya yi zaman gaggawa kan Shirin Isra’ila na mamaye Gaza August 11, 2025 Iraki: An bankado wani yunkurin kai wa masu ziyarar Arbaeen hari August 11, 2025 Chadi: An Daure Wani Dan Adawa Shekaru 20 A Gidan Kaso Da tara August 10, 2025 Dangantaka Tsakanin Iran da Saudiya Yana Taimakawa Zaman Lafiya A yankin August 10, 2025 Iran Zata Hana Amurka Samar da Hanya A yankin Caucasus Ko Rasha Bata taimaka ba August 10, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare A Kan Garuruwa Da Dama A Yankin Quneitra Na Kasar Siriya August 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
Kungiyar Hizbollah ta kasar Lebanon ta bayyana cewa Isra’ila na yin kuskure idan ta na tunanin kashe-kashe da kisan gillar da ake wa mambobi da kwamandojinta zai kawo karshen kungiyar.
Wannan na zuwa ne bayan kisan gillar da Isra’ila ta yi wa babban kwamandan sojin kungiyar da wasu makusantansa a ranar Lahadi, a wani hari da ta kai a kudancin babban birnin Lebanon.
Haitham Ali Al-tabataba’i da aka fi sani da Abu Ali, ya yi shahada ne tare da wasu dakarun hizbullah guda 4 a wani mummunan hari da Isara’ila ta kai a heret hareik dake kudancin birnin beirut.
Tabataba’I yana daya daga cikin jajircaccen dakarun kungiyar hizbullah , kuma ya taka rawa sosai wajen tsarin tsaron kungiyar tun shekarun farko da aka kafata.
Kisan nasan ya kara nuna irin yadda isra’ila ke keta yarjejeniyar dakatar da tsagaita bude wuta da aka cimma, kuma kisan nasa zai kara karfafa jajircewa a turbar gwagwarmaya a yankunan labanon da falasdinu.
Da yake bayyana hakan Shugaban Majalisar Zartarwa ta Hizbullah, Sheikh Ali Damoush ya ce duk lissafin Isra’ila game da kungiyar ya cutura, saboda ta yi imani da cewa kisan gillar manyan mutane da kwamandojin soja na kungiyar zai iya kai ta ga nasara in ji, a ranar Litinin.
“Irin wadannan kisan gillar suna karfafa kudurin kungiyar na fuskantar mamayar Isra’ila,” in ji shi yayin da yake jawabi a jana’izar Shahid Haytham Ali Tabatabai.
Ya yi wa Tabatabai godiya, yana mai jaddada cewa ya taka rawa a lokacin yakin farko na Hezbollah.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gagi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci