Welayati: Makircin Amurka da Isra’ila na kwance damarar Hizbullah ba zai yi nasara ba
Published: 10th, August 2025 GMT
Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu.
Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon.
“Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi.
Ya yi ishara da matakan siyasa da wasu bangarori na Labanon suke dauka da nufin kwance damarar Hizbullah, yana mai bayyana su a matsayin wadanda suka tasirantu da matsin lamba daga Amurka da Isra’ila.
Velayati ya ce Washington da “Isra’ila” sun yi imanin za su iya maimaita wani yanayi irin na kasar Syria a Lebanon, inda suka yi amfani da Jaulani domin aiwatar da wanan manufa, amma wannan mafarkin ba zai zama gaskiya ba, kuma Lebanon kamar kullum, za ta ci gaba da zama mai gwagwarmaya domin rayuwa a cikin martaba da karama.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Birtaniya: ‘Yan sanda sun kama akalla mutane 365 a zanga-zangar goyon bayan Falasdinu August 10, 2025 Venezuela: An dakile yunkurin kai wasu munanan hare-hare a cikin kasar August 10, 2025 Pezeshkiyan Ya Yabawa Yan Jarida A Ayyukansu A Yakin Kwanaki 12 August 9, 2025 Yansanda A Burtaniya Ta kama Mutane Fiye Da 200 Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 9, 2025 Iran Ta Yi Maraba Da Sulhuntawa Tsakanin Armenia Da Azerbaijan August 9, 2025 Falasdinawa 11 Ne Suka Rasa Rayukansu Saboda Yunwa A Gaza August 9, 2025 Shugaban Kwango, Tshisekedi Ya Shigar Yan Tawaye A Gwamnatinsa August 9, 2025 Iran: ‘Yan Sahayoniyya Na Shirin Share Falasdinawa Daga Kan Doron Kasa August 9, 2025 Iran: Amurka Ta Sha Kaye Daga ‘Yan Gwagwarmayar Kasar Yemen August 9, 2025 Guterres: Dole Ne Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Gaggauta Janye Shirinta Kan Gaza August 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea
A kasar Guinea an fara kidaya kuri’un da aka kada na zaben kasa da ake hasashen cewa shugaban mulkin soja zai sami nasara.
Kada kur’iar ta raba gardama akan sabon tsarin Mulki zai sama wani gagarumin mataki na fitar da kasar daga mulkin soja zuwa na farar hula.
Shugaba Janar Mamadi Doumbouya wanda ya yi juyin Mulki zai iya samun damar ci gaba da zama akan Kargar Mulki.
Jam’iyyun hamayyar siyasa a kasar Guinea sun yi kira da a kauracewa kada kuri’ar raba gardamar.
Da akwai mutane miliyan 6.7 da su ka cancanci kada kuri’a a fadin kasar. A bisa dokar zaben kasar, idan kaso 50% su ka kada kuri’a, to za a amince da sakamakon abinda su ka zaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya September 22, 2025 Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya September 22, 2025 Dakarun IRGC: Iran Za Ta Tarwatsa Makiya Tare Da Mayar Da Martani Kan Duk Wani Zalunci September 22, 2025 Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi September 22, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Aiwatar Da Kisan Gilla Kan Fararen Hula 5 A Kudancin Kasar Lebanon September 22, 2025 Ministan Harkokin Waken Falasdinu Ta Yi Kira Ga Karin Kasashe Su Amince Da Samuwar Kasarta September 21, 2025 Iran Da Pakistan Sun Sake Tsara Dangantakarsu Ta Tattalin Arziki September 21, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci