ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki
Published: 10th, August 2025 GMT
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), ta yi gargaɗi cewa za ta iya sake tsunduma yajin aiki saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗauka.
Shugaban ƙungiyar, Christopher Piwuna, ya ce gwamnati ba ta kula da walwalar malamai, ba ta samar da kuɗaɗen gudanar da jami’o’i yadda ya kamata, kuma ba ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma ba.
Wannan na zuwa ne bayan Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa “Babu wata jami’a ko malaman ASUU da za su sake shiga yajin aiki” idan aka ci gaba da tattaunawa da kuma cika buƙatun malaman.
Sai dai ASUU ta ce hanyar da za a guji yajin aiki ita ce kawai a cika musu alƙawuran da aka riga aka amince da su.
Ƙungiyar ta bayyana cewa yawancin malamai suna koyarwa da gudanar da bincike ba tare da kayan aiki ko tallafi ba.
Wasu ma ba sa iya biyan kuɗin mota zuwa wajen aiki, biyan buƙatun yau da kullum, har ma da kuɗin makarantar ’ya’yansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Yajin aiki
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa ta ɗage ranar dawowarta zuwa 7 ga watan Oktoba
Majalisar Dokoki ta Kasa ta ɗage ranar dawowarta daga hutu zuwa 7 ga watan Oktoba, 2025.
Karin bayani na tafe..