Aminiya:
2025-11-27@19:40:37 GMT

EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo 

Published: 10th, August 2025 GMT

Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne.

Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun.

’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi

Gidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun.

Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su.

Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja.

Wani jami’in EFCC ya shaida wa Aminiya cewa samamen ya samo asali ne daga Ofishin EFCC na Legas.

Daraktan Kamfanin OOPL Ventures, Mista Vitalis Ortese, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa suna ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga EFCC.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce zai yi bincike kafin ya yi wa manema labarai ƙarin bayani.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan jami’an EFCC daga Ofishin Ibadan suka kama mutum 56 da ake zargi da aikata damfara a Intanet a wani otal mai suna K-Hotel da ke Itori, a Jihar Ogun.

An kama ɗaya daga waɗanda ake zargin da bindigogi guda biyu.

EFCC ta kuma ƙwato motoci shida masu tsada, wayoyin salula 89, kwamfutoci, da wasu takardu.

Hukumar ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da dukkanin waɗanda ta kama a gaban kotu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Damfara Ɗakin Karatu zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja

Wata tankar mai ta yi gobara a wani gudan mai a yankin Tungan-Bunu da ke Ƙaramar Hukumar Rijau a Jihar Neja, lamarin da ya janyo ƙonewar gidaje da kadarori da masu yawa.

Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne a lokacin da tankar take shirin sauke mai a ranar Litinin da yamma, inda wutar ta bazu zuwa gidajen da ke kusa.

Duk da cewa babu wanda ya rasa ransa, lamarin ya haifar da firgici inda mazauna yankin suka yi ta tserewa suka bar gidajensu yayin da tankar ke ci da wuta.

Tankar mai ta yi hatsari a hanyar Lapai-Agaie Amurka za ta tallafa wa Nijeriya daƙile matsalar tsaro Mayaƙan Boko Haram sun fille kan mata 2 a Borno

A wani lamari ba daban, wata tankar mai ta kife a kan hanyar Lapai zuwa Agaie, lamarin da ya toshe hanya tare da haddasa cunkoson ababen hawa.

Shaidu sun ce tankar, wadda ke ɗauke da fetur daga Legas zuwa Gombe, ta kife ne da misalin karfe 10 na safe a ranar Litinin bayan jikinta ya rabu da kan motar, ya ƙetare hanya, abin da ya tayar da hankalin jama’a.

Wani mazaunin yankin, Malam Mahmud Abubakar, ya ce jami’an tsaro sun garzaya wajen domin tsare yankin, sannan aka tura ma’aikatan kashe gobara don kauce wa tashin wuta.

Ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a yankin Efu-Nda-Egbo na Ƙaramar Hukumar Lapai, inda ya haddasa cunkoson ababen hawa mai tsanani.

Kokarin tuntuɓar Darakta-Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran wayar da wakilinmu ya yi masa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
  • Uganda: An Kama Fiye Da ‘Yan Hamayyar Siyasa 300 A Lokacin Yakin Neman Zabe
  • An buɗe wasu makarantu domin ci gaba da jarawaba a Katsina
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • Abin da ya sa nake haxa harkar fim da harkar karatu-Nabila
  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja