Ya ba wa alaramma kyautar motarsa saboda daɗin karatun Alkur’ani
Published: 11th, August 2025 GMT
Wani mutum ya ba da kyautar motarsa da ita kadai gare shi ga wani mai jan baki (alaramma) saboda ƙwarewarsa a haddar Al-kur’ani.
Malam Yusuf Ɗan-Birni, ya kyautar da motar ce a taron wa’azin wata-wata da Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta shirya a garin Kubwa da ke yankin Babban Birnin Tarayya.
Malam Yusuf Ɗan-Birni wanda ke sana’ar gyaran waya, ya bai wa jama’a mamaki a yayin da ake tsaka da karatun da misalin ƙarfe 10 nan dare inda ya miƙa makullan motarsa ga mai gabatar da wa’azin, Sheikh Mahmud Assalafi, ya sanar da shi cewa ya kyautar da ita ga majabaƙinsa, Alaramma Usman Nasidi Gusau.
Wani ganau mai suna Malam Nuhu Abu-Huzaifa ya shaida wa Aminiya cewa, wanda ya kyautar da motar na zaune a kusa da shi, sai ya lura yana zubar da ƙwalla a lokacin da alaramman ke karanta Alƙur’ani Mai Tsarki.
Malam Nuhu ya bayyana cewa, “Malami mai fassara Sheikh Mahmud Assalafi ya yi ta yawatawa da alaramman a cikin ayoyi da surorin Wlqur’ani ta hanyan ƙidayo masa surorin da kuma ayoyin, a inda alaramman ke gano su nan take a cikin sauki.”
Ya ce bayan kammala wa’azin da misalin ƙarfe 11 na dare ya ga wanda ya yi kyautar motar ya tsayar da ɗan acaɓa zai hau da nufin komawa gida.
Ya yi addu’ar Allah Ya daɗaɗa wa Yusuf Ɗan-Birni da iyalansa kamar yadda ya daɗaɗa wa Alaramman, Ya kuma maye masa gurbin motar da ya kyautar da wadda ta fita ta.
A zantawarsa da Aminiya a kan lamarin, Babban Limamin Masallacin Badar da ke Garin na Kubwa inda taron ya gudana, sheikh Abdulmumini Ahmad Khalid, ya nuna farin ciki a kan lamarin tare da bayyana kyautar a matsayin abin da ba kasafai yake faruwa ba.
Ya ce, ba a fi wata guda ba, Dan-Birni ya zo da motar da ya saya ƙirar Fijo 406, cewa ya saye ta domin zirga-zirga da na’urorin daukar karatu a bidiyo da sauran ayyukan masallacin, da yake watsawa ta dandalin sada zumunta.
Ya yi addu’ar Allah Ya saka masa da mafi alheri.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Al Ƙurani Alaramma ya kyautar da
এছাড়াও পড়ুন:
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa.
Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News.
Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a KebbiƊaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki.
Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a fi buƙatar ƙwarewarsa.
Da aka tambayi inda za a tura shi, majiyar ta ce Sufeton Janar na ’yan sanda ne zai bayyana hakan, tare da jaddada cewa Adewale ya yi iya bakin ƙoƙarinsa a matsayin kwamishina.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta ƙasa, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da wannan sauyi, inda ya ce sauyin wajen aiki al’ada ce da ake yi domin inganta ayyukan jami’an rundunar.