Barcelona Ta Tube Ter Stergen Daga Mukaminsa Na Kaftin Din Kungiyar
Published: 8th, August 2025 GMT
Sun kara da cewa,”A cikin wannan lokaci, mataimakin kyaftin na yanzu, Ronald Araujo ne zai karbi aikin kyaftin din, Ter Stegen ya buga wa Barcelona wasanni sama da 400 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Borussia Monchengladbach a shekara ta 2014, ya lashe manyan kofuna da suka hada da gasar zakarun Turai da kuma gasar La Liga shida a kungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yar shekara 17 daga Yobe ta lashe Gasar Turanci ta Duniya
Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin ƙasar Birtaniya.
Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a Gasar ‘UK Global Finals’, sakamakon fintinkau da ta yi wa takwarorinta na ƙasashe daban-daban da ke jin harshen Ingilishi a duniya.
Wannan nasara ta lashe wannan babbar gasa da Nafisa ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a mahaifarta, Jihar Yobe. Nafisa ta wakilci Najeriya ne daga Kwalejin Tulip International College (NTIC), Jihar Yobe.
A wani jawabi da ya gabatar jim kaɗan da sanarwar lashe gasar, wani ɗan uwan Nafisa, Malam Hassan Salihu, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Yobe da Makarantar NTIC bisa irin gudunmawar da suna bayar har ya kai ga samun nasarar ’yar uwarsa a wannan babbar gasa ta duniya. Ya ƙara da yaba wa shugabannin kwalejin bisa ga yadda suke gudanar da karatuttukansu da hakan ne ta kai ga nasarar.
Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje Sanata Buba ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi kyauta“Tabbas wannan nasara da Nafisa ta samu da taimakon Allah (SWT) ne,” in ji shi, kuma nasarar wata babbar shaida ce ga abin da matasan Najeriya za su iya cimma idan aka ba su dama da goyon baya.
“Alal haƙiƙa wannan nasara da Nafisa ta samu ya zama abin farin ciki da alfahari ga duk al’ummar jiharmu ta Yobe da ma ƙasa baki daya,” in ji Malam Hassan.