Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno
Published: 10th, August 2025 GMT
Hukumar Shari’a ta Jihar Borno ta ƙara wa ma’aikatanta 97 girma bayan wani taro na kwanaki huɗu da ta gudanar a Maiduguri.
Muƙaddashin sakataren hukumar, Saleh Khala Jidda ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa cewa ma’aikatan sun samu ƙarin girma ne saboda ƙwazonsu.
EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan SakkwatoWaɗanda abin ya shafa sun hada da Majistare 10 daga matakin Majistare mataki na ɗaya zuwa Babban Majistare mataki na biyu.
Sai Majistare daga matakin farko zuwa Babban Majistare na biyu.
Sauran sun haɗa manyan Magatakarda daga mataki na ɗaya zuwa na biyu.
Sai dai a gefe guda, hukumar ta ɗauki mataki kan wani alƙalin Babban Kotun Majistare ta 4 da ke Wulari, Maiduguri, mai suna Yusuf Garba.
Binciken da kwamitin ƙorafe-ƙorafen jama’a ya gudanar ya gano cewa alƙalin ya karkatar da kuɗaɗen shiga na gwamnati har Naira 100,000.
Saboda haka aka sauke shi daga muƙaminsa tare da umartar ya kai rahoto ga Babban Magatakarda domin a sake masa muƙami.
Hukumar ta tabbatar wa jama’a cewa tana da niyyar ci gaba da tabbatar da gaskiya da adalci a kotuna.
Sannan ta ce za ta ladabtar da masu cin hanci da rashawa da kuma girmama masu gaskiya da riƙon amana.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ƙarin girma Shari a
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Gaskiya Ba Ne Rahoton Da Ke Cewa An Yi Sulhu Da Bello Turji – Guyawa Isa
“Shin an taɓa yin sulhu a na cin zarafin jama’a, an taɓa yin sulhu a na sa manoma noman dole, an taɓa yin sulhu a na karbar harajin dole, an taɓa yin sulhu ba a ajiye makamai ba?”
Ya ce Turji da sauran ‘yan bindigansa irin su Kachalla Choma da Kachalla Haru ba za su ajiye makami ba, ya ce suna da kwamandoji da makaman da sun fi a kirga.
Guyawa ya bayyana cewa Malamin bai san Turji ba, bai kuma san yankinsu ba, ya ce su da suke a yankin sun tabbatar Turji bai ajiye makami ba, kuma bai yi sulhu da kowa ba.
Ya ce a kwanan baya Turji ya kashe jami’an tsaro tare da ƙone motarsu, don haka idan ya yi sulhu ba zai yi hakan ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp