Jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Cewa: Iran Ta Cimma Matsayi A Yaki Kwanaki 12
Published: 10th, August 2025 GMT
Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12
Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya.
Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri kan kasarta a fagen diplomasiyya zuwa wani lamari da duniya ta amince da shi.”
Har ila yau Baqeri Kani ya yi ishara da hadin kan kasa a matsayin mafi girman bayyanar da Iran ta taka rawa a wannan yaki yana mai cewa: Wannan hadin kai yana nuna irin gagarumin goyon bayan da jami’an diflomasiyyar Iran suka nuna.
Ya kara da cewa: Goyon bayan jama’a ga manufofi da matakan gwamnatin na iya taimakawa wajen cimma manufofin diflomasiyya. Har ila yau ya bayyana cewa: A halin da ake ciki yanzu, kasashen yammacin duniya, baya ga Amurka, sun taka rawa wajen tallafawa hare-haren da aka kai wa Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jami’an Tsaron Iran Sun Murkushe ‘Yan Ta’adda Kan Ofishin ‘Yan Sanda A Kudu Maso Gabashin Kasar August 10, 2025 Jefa Agajin Abinci Ta Sama A Zirin Gaza Ya Janyo Shahadan Falasdinawa 23 Tare Da Jikkata Wasu 124 August 10, 2025 Tehran Times: Mai Yiwuwa Iran da Amurka su koma Tattaunawa August 10, 2025 Tel Aviv: Dubban yahudawa sun yi zanga-zangar adawa da yakin Gaza August 10, 2025 Welayati: Makircin Amurka da Isra’ila na kwance damarar Hizbullah ba zai yi nasara ba August 10, 2025 Birtaniya: ‘Yan sanda sun kama akalla mutane 365 a zanga-zangar goyon bayan Falasdinu August 10, 2025 Venezuela: An dakile yunkurin kai wasu munanan hare-hare a cikin kasar August 10, 2025 Pezeshkiyan Ya Yabawa Yan Jarida A Ayyukansu A Yakin Kwanaki 12 August 9, 2025 Yansanda A Burtaniya Ta kama Mutane Fiye Da 200 Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 9, 2025 Iran Ta Yi Maraba Da Sulhuntawa Tsakanin Armenia Da Azerbaijan August 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Iran ta cimma
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000.
Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakaduHaka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Kazalika, shugaban ya bai wa hukumar ’yan sandan farin kaya ta DSS umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai a rundunar kare dazuka wato Dakarun Gandun Daji ta Forest Guard.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci DSS ta aika dakarun Forest Guard “domin zaƙulo ’yan ta’adda da ’yan fashi daga dazuka.”
“Babu wani sauran gidan ɓuya ga miyagu,” in ji shi kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewar, za a sake horar da jami’an ’yan sanda da aka janye daga gadin fitattun mutane kafin mayar da su aikin ɗan sandan gada-gadan.
Shugaban ya yi amfani da damar wajen jinjinawa hukumomin tsaro wajen kuɓutar da mutane 34 da aka sace a Mujami’ar Kwara da ɗalibai 24 da aka sace a makarantar jihar Kebbi, yayin da ya ce suna ɗaukar matakan da suka dace wajen kuɓutar da ɗaliban makarantar mabiya ɗarikar Katolika da ke Jihar Neja.
Tinubu ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar a kan gudumawar da jami’anta ke bayarwa da kuma gabatar da ta’aziyar rasuwar Janar Musa Uba da ƴanta’adda suka yiwa kisan gilla, yayin da ya buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da tashin hankali.
Shugaban ya buƙaci majalisar ƙasa da ta sake fasalin dokokin tsaro domin bai wa jihohi damar samar da ’yan sanda na kashin kan su, yayin da ya ce gwamnatin tarayya za ta taimaka musu.
Tinubu ya kuma buƙaci Masallatai da Majami’u da su dinga neman taimakon jami’an tsaro a duk lokacin da za su gudanar da taron ibadun su, musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.
Shugaban ya kuma jajanta wa gwamnatoci da kuma mutanen jihohin Kebbi da Borno da Zamfara da Neja da Yobe da kuma Kwara saboda kisan gillar da ƴan ta’adda suka yiwa mutanen su.