2025-09-17@23:12:13 GMT
إجمالي نتائج البحث: 319
«Manjo janar Musawi»:
Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Yakin Haraji Da Cinikayya Ba Zai Gurgunta Fifikon Da Sin Ke Da Shi A Fannin Raya Masana’antun Sarrafa Hajoji Da Kasar Ta Gina A Tsawon Lokaci Ba
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa. Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne. Lin Jian, wanda ya...
Ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Yobe (ALGON) ta karrama Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, da lambar yabo ta karramawa bisa himmar ayyukan raya ƙasa da gwamnatinsa ke gudanarwa a faɗin jihar. Karramawar, wacce aka bayyana a matsayin irinta ta farko a tarihin Jihar Yobe, shugabannin ƙananan hukumomi 17 na jihar suka ba da ita ga gwamna. Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno Da yake jawabi, shugaban ƙungiyar ALGON a Jihar Yobe, kuma shugaban ƙaramar hukumar Damaturu, Alhaji Bukar Adamu, ya yaba da yadda Gwamna Buni yake gudanar da harkokin mulki na bai ɗaya. Ya ce nasarorin da aka samu sun haɗa da fannoni na...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rikicin kwamitin gudanarwa da malaman Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bida (Bida Poly), ya ƙara ƙamari bayan da makarantar ta dakatar da ayyukan Kungiyar Malamai (ASUP) sannan ta kawo sojoji domin kula da jarrabawa da dalibai ke gudanarwa. Ƙungiyar ASUP reshen kwalejin ta shiga yajin aiki mara wa’adi, domin neman a biya su alawus ɗin ƙarin aiki na watanni 18 da suka wuce. Ƙungiyar ta umarci mambobinsu da kada su gudanar da jarrabawar zangon da ta fara ranar Litinin, 15 ga Satumba, 2025. Wani ma’aikacin makarantar ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin an gayyace su ne domin kare ɗalibai da wasu malamai daga shirin da ASUP ke yi na hana gudanar da jarrabawa. ’Yan bindiga sun kai wa sojoji...
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki. A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu...
Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya roƙi Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO ya gaggauta dawo masa da wuta bayan rasuwar wasu marasa lafiya da ke samun kulawa ta ceton rayuwada na’ura. Wata sanarwa da kakakin asibitin, Hauwa Inuwa Dutse ta fitar ta nuna takaici bisa rasuwar marasa lafiyan, tana mai cewa mace-macen waɗanda za a iya kauce wa ne idan akwai tsayayyiyar wutar lantarki. Ta bayyana cewa Asibitin yana AKTH yakan biya kuɗin wuta akai-akai daga kuɗaɗen shigansa, kuma yana kashe kuɗaɗe wajen sanya mai a janareto domin amfani idan aka ɗauke wuta daga KEDCO. Don haka, “Hukumar gudanarwar Asibitin AKTH na roƙon Kamfanin KEDCO da ya taimaka wa ayyukan asibitin ta hanyar dawo da wutar a yayin...
Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
Babban sakatare tsaron kasa na Iran Ali Larijani ya fadi cewa ya zama wajibi kasashen musulmi su hada kai waje guda don tunkarar rashin hankalin Isra’ila da take yi kan alummar falasdinu. A cikin wani bayani da ya aike da shi a shafinsa na X ya ce wannan mataki zai tilastawa shugaban Amurka yin gaggawa wajen mika umarninsa ga gwamnatin Isra’ila bisa hujjar kawo zaman lafiya a duniya da kuma bada kyautar zaman lafiya ta Nobel. Kasar Qatar ta sanar da kiran zaman gagganawa na kasashen larabawa da na musulmi a ranar litinin mai zuwa domin tattaunawa game da harin da Isra’ila ta kai domin kashe jagororin kungiyar Hamas a kasarta. Manyan jami’an hamas da suke tattaunawa kan batun bukatar...
A cikin shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 14, kasar Sin ta samu ci gaba a bangaren sufurin jiragen kasa na cikin birane, da motocin bas na zirga-zirgar yau da kullum, da zirga-zirga cikin aminci. A halin yanzu, akwai layukan dogo 331 a cikin birane 54 dake fadin kasar, inda jimilar tsawonsu ta kai kusan kilomita 11,000, wanda ke matsayi na farko a duniya. Babban rukunin gidajen rediyo da talabin na Sin wato CMG, ya samu wannan kididdiga ne daga ma’aikatar kula da sufuri da jigilar kayayyaki ta kasar a kwanan nan. A yanzu haka, sama da mutane miliyan 200 a kasar Sin sun zabi hanyoyin sufuri masu kiyaye muhalli a kowace rana, wadanda suka hada da miliyan 100 da suke hawa jiragen kasa masu inganci...
Sanata Ibrahim Lamiɗo, mai wakiltar Sakkwato ta Gabas, ya nuna damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ke ƙara tsananta a yankinsa, inda ya ce hare-hare da satar mutane sun zama ruwan dare. A hirarsa da manema labarai, Sanatan ya ce: “Gaskiya abin tsoro ne rayuwa a Gabashin Sakkwato. Kusan kowace rana sai an kai hari, an kashe mutane ko kuma an sace su. Muna cikin tashin hankali sosai.” ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja Gwamna ya aike wa majalisa dokar haramta auren jinsi ɗaya a Kano Ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da yake yi wajen ganin an kawo gyara, wasu ’yan siyasa suna kawo cikas. Sai dai ya ce ba zai fasa jajircewa wajen ganin...
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), ta bai wa Gwamnatin Tarayya sa’o’i 24 don ɗaukar mataki game da buƙatunsu, ko kuma su tsunduma yajin aiki. Wannan matakin ya biyo bayan cikar wa’adin gargaɗin kwanaki 10 da suka bayar a baya. Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da shugabannin Ansaru 2 a kotu Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci Tuni wasu likitoci a Abuja da Jihar Oyo suka tsunduma yajin aiki. Likitocin, waɗanda yawancinsu ke aiki a Asibitocin Koyarwa da na Ƙwararru, suna yawan tafiya yajin aiki saboda rashin biyan wasu haƙƙoƙinsu. A halin yanzu, suna neman a biya su kuɗin horon 2025 da bashin albashin da suka bi, sannan sun buƙaci a...
A yau Laraba kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta soki lamirin harin da aka kaddamar a birnin Doha, fadar mulkin kasar Qatar a jiya Talata, tana kuma adawa da matakin Isra’ila na cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaron kasa na Qatar. Lin Jian ya ce kasar Sin na kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, musamman Isra’ila, da su kara kokari wajen dakile rikicin, da sake fara tattaunawa maimakon akasin hakan. Dangane da sanarwar da Isra’ila ta gabatar wa Amurka kafin ta kaddamar da harin ta sama, Lin Jian ya bayyana cewa, matakin da Isra’ila ta dauka na da...
A halin yanzu, sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda suna ci gaba da habaka cikin sauri, yayin da mulkin kama-karya, son kai, da kuma kariyar tattalin arziki suka kara yawaita. A wannan yanayi, a wajen taron yanar gizo na shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a ran 8 ga watan nan da muka ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarwari uku don karfafa “hadin kan kasashen BRICS” da kuma kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya. Wato na farko nacewa ga kasancewar mabambantan bangarori a duniya. Bugu da kari, a kare adalcin duniya domin ci gaba da bude kasuwanci don samun nasara ga kowa, da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya....
Majalisar Dattawa ta sanar da cewa ba ta amince da buƙatar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya kan komawa bakin aiki, saboda har yanzu ba a kammala shari’ar dakatar da ita ba. Tun dai a ranar 8 ga watan Agustan bana ne Sanata Natasha ta rubuta wa majalisar wasiƙa, inda ta sanar da ita shirinta na komawa bakin aiki a ranar 4 ga watan Satumba, tana mai kafa hujja da cikar wa’adin watanni shida da aka dakatar da ita. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya Ana zargin jami’in sibil difens da harbe abokin aikinsa a Abuja Sanatar ta bayyana cewa kotun tarayya ta yanke hukunci a watan Yulin da ya gabata...

Gwamnatin Tarayya, NUPENG Da Ɗangote Sun Fara Tattaunawa Don Kawo Ƙarshen Yajin Aikin Ma’aikatan Mai
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da jami’an Hukumar Kula da Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), wakilan kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC, shuwagabannin kamfanin ‘MRS Holdings Limited’ da kuma kungiyar ‘yan kasuwa ta kasa (TUC). Da yake bayyana bude taron, Minista Dingyadi ya jaddada aniyar gwamnati na sulhu a tsakanin kungiyar da masu gudanar da masana’antu. Ya bayyana bangaren mai da iskar gas a matsayin jigon tattalin arzikin Nijeriya, yana mai gargadin cewa tsawaita yajin aikin zai haifar da mummunan sakamako ga kasar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya...
Kungiyar Hamas ta jaddada cewa: Tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen dakatar da ta’addanci kan al’ummar Falasdinu Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Lahadin da ta gabata cewa, tana maraba da duk wani yunkuri da zai taimaka a fagen yunkurin da ake yi na dakatar da kai hare-hare kan al’ummar Falasdinu, tana mai bayanin cewa ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma matsaya. A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hamas ta fitar ta ce: “Ta samu wasu ra’ayoyi daga bangaren Amurka ta hanyar masu shiga tsakani don cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta. A wannan...
Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba. Kukan Iyaye A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida. Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros...
’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno. Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58. Tsagin NNPP na ƙasa ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a Edo Wannan harin ya faru ne da daddare a ranar Juma’a, inda maharan haye a kan ɗaruruwan babura, suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje. Wani mazaunin garin, Malam Bukar, ya shaida wa manema labarai cewa: “Sun shigo suna ta kabarbari da harbi kan mai uwa...
“Haka nan, ‘yan bindigan, suna sake kawo wani harin a wannan gari namu na Galadi da misalign karfe 10:15 na daren ranar Laraba, inda suka kewaye baki-dayan Galadin; illa bangare guda shi ma saboda gulbi ya tare wannan gefen ne, inda suka bude wa Galadin wuta ta kowane gefe baki-daya,” in ji shi. Kazalika ya kara da cewa, “Babu shakka, wannan hari ya yi sanadiyyar asarar rayukan mutane biyar, inda kuma wasu hudu ke kwance a gadon asibiti. Sai dai, Allah cikin ikonsa ya sa ba su samu damar tafiya da ko mutum guda ba,sakamakon dauki da aka samu daga wasu jami’an tsaro da suka garzayo daga Shinkafi. “Duk da cewa, a nan muna da jami’an tsaro; amma a lokacin...
Miliyoyin mutanen kasar Yemen sun fito zuwa dandalin taron mutane a dukkan garuwan kasar a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon All…(s) a kasar a jiya Alhamis. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyeed Abdulmalik al-houthi, a jawabin da ya gabatar a karshen tarurrukan, zuwa ga hadin kan kasashen musulmi saboda ma’abucin wannan ranar (s). Ya kuma yi tir da allawadai da ci gaba da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza. Ya kuma yi addu’a ga shahidan gwamnatin kasar wadanda HKI ta kashe a makon da ya gabata. Har’ila yau a cikin Jawabinsa Sayyid Huthi ya bayyana cewa, mutanen yemen da yardarm All..suna daga cikin wadanda suke raya addinin musulunci bayan rauninsa. Sannan daga cikin...
Miliyoyin mutanen kasar Yemen sun fito zuwa dandalin taron mutane a dukkan garuwan kasar a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon All…(s) a kasar a jiya Alhamis. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyeed Abdulmalik al-houthi, a jawabin da ya gabatar a karshen tarurrukan, zuwa ga hadin kan kasashen musulmi saboda ma’abucin wannan ranar (s). Ya kuma yi tir da allawadai da ci gaba da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza. Ya kuma yi addu’a ga shahidan gwamnatin kasar wadanda HKI ta kashe a makon da ya gabata. Har’ila yau a cikin Jawabinsa Sayyid Huthi ya bayyana cewa, mutanen yemen da yardarm All..suna daga cikin wadanda suke raya addinin musulunci bayan rauninsa. Sannan daga cikin...
A yanzu haka yankuna da dama wadanda a baya ba su fuskanci kalubalen matsalar tsaro ba, a yanzu haka sun fara dandana ukubar ta’addanci da bakuntar sansanin ‘yan gudun hijira. Kalubalen tabarbarewar tsaro da kiran da shugaban rundunar tsaro ta Kasa, Janar Christopher Musa ya yi kan ‘yan Nijeriya su dauki matakan kare kai ya haifar da cece- kuce musamman ga galibin jama’a da ke ganin gwamnati ta kasa. Da yawan jama’a na ganin duk da makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro da kwarewar jami’an sojoji amma ‘yan ta’adda sun rinjaye su har suna ikirarin jama’a su dauki matakan kare kai. Janar Musa wanda daga baya ya janye kalamansa, tun da farko ya bukaci ‘yan Nijeriya da...
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku. ’Yan bindiga sun sace basarake a Kogi ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare a 2027. A ’yan kwanakin nan ne aka...

Araghchi : China da Rasha sun bi sahun Iran wajen kin amincewa da yunkurin E3 na dawo mata da takunkumai
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce shi da takwarorinsa na Rasha da China sun aike da wasika ga Majalisar Dinkin Duniya, inda suka yi watsi da matakin da Birtaniya da Faransa da Jamus suka dauka a baya-bayan nan na yunkurin maido da takunkumin kasa da kasa kan Iran a matsayin mataki marar ma’ana. Abbas Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wani sakon da ya wallafa a jiya a Shafin X, kwanaki hudu bayan da kasashen Turai wadanda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar nukiliya ta 2015 suka sanar da kwamitin sulhu na MDD cewa, sun yi amfani da tsarin dawo da dukkanin takunkumin MDD a kan Iran. Ya ce, a cikin wasikar hadin gwiwa da suka aike wa...
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk wata barazana ta makiya a kan akasar. A cikin sakon da ya aike na ranar tsaron sararin sama ta kasa, Janar Mousavi ya yi tsokaci kan yadda yanayin tsaro na yanki da na duniya ke ciki, inda ya bayar da misali da irin abubuwan da al’ummar Iran suka samu a tsawon shekaru 8 a bangaren ayyukan tsaro da kariya, wanda kuma ya tabata a yakin...
Jakadan shugaban kasar Rasha na musamman kan al-amuran yaki a Ukraine ya bayyana cewa masu son yaki a cikin shuwagabannin kasashen turai suna zagon kasa ga kokarin shugaba Trump na kasar Amurka yake yi na kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Kirill Dmitriev yana fadar haka, a shafinsa na X , inda yake zargin shuwagabannin kasashen turai da hana tsaida yaki a Ukraine. Dmitriev ya kara da cewa Brussels na zangon kasa ga shirin tsaida yakin tare da dorawa shugaban kasar Ukraine gabatar da bukatun ba zasu taba yiyuwa Rasha ta amince da sub a. Ya kara da cewa shuwagabannin kasashen Turai suna tsawaita yakin har zuwa lokacinda Al-amura zata sake komawa...
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara da ’yan majalisar dokokin jihar za su koma kujerunsu a ranar 18 ga Satumba, lokacin da dokar ta-ɓaci a jihar za ta ƙare. Wike, ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a jihar. A shekara 2 Gwamnatin Tinubu ta ware wa Legas ayyukan N3.9trn Gwamnan Taraba ya shiryawa gwamnonin Arewa Maso Gabas liyafa Ya kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓe mai lamba 7 a mazaɓa ta 9, Rumuepirikom, Ƙaramar Hukumar Obio-Akpor. Tsohon gwamnan jihar, ya ce zaɓen na gudana cikin lumana idan aka kwatanta da zaɓukan da suka gabata. Ya bayyana cewa zaɓen Ƙananan Hukumomin ya...
A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kanta,a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar gabanin wani taron sirri na kwamitin sulhu na MDD. Kasashen uku da aka fi sani da E3 sun ce a shirye suke su dage mayar da takunkumin har na tsawon watanni shida idan Tehran ta amince da sake baiwa masu binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya damar shiga cibiyoyinta na nukiliya, tare da magance abin da suka kira damuwar da suke da ita game da yawan tataccen sinadarin uranium da ta ke da shi, da kuma shiga tattaunawa da Amurka. Sabanin haka, jakadan...
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya ya kira mummunan halin da ake ciki a Gaza a matsayin abu mafi muni a wannan lokaci ta fsuakr mawuyacin hali da dan adam yake ciki. Yayin da yake magana da manema labarai a birnin New York a ranar Alhamis, Antonio Guterres ya bayyana yadda ake lalata tsarin abinci da ruwan sha da na kiwon lafiya a Gaza, lamarin da ya sa mutane ke fuskantar yunwa. Guterres ya bayyana damuwarsa kan mamayar da sojojin Isra’ila suka yi a birnin Gaza, yana mai cewa hakan na nuni da wani gagarumin ci gaba a yakin. “Daruruwan dubban fararen hula-da suka gaji kuma sun gaji-zasu sake tilastawa yin gudun hijira, tare da jefa iyalai cikin mawuyacin hali. Dole...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A ’yan watanni da suka gabata, matasa da yawa a Najeriya sun dukufa don ganin hakar su ta cimma ruwa wajen samun kudaden kirifto. Amma alamu na cewa a baya-bayan nan wasu daga cikinsu sun sare sun kuma saduda sun dawo daga rakiyar harkar. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan dalilan wasu matasan na yin watsi da harkar kirifto. Domin sauke shirin, latsa nan
3. Karuwar allunan sola ta samar da damar samun karin wutar lantarki, inda ake sa ran samun karuwar wutar lantarki da za ta kai fiye da kaso 5% a wasu kasashe 16 dake nahiyar Afirka. Tambaya ita ce: me ya sa allunan solan kasar Sin samun karbuwa a Afirka? Domin suna da araha, gami da inganci. Kamar yadda muka sani, ana sayar da allon sola mai karfin watt 420 kan farashin kusan dalar Amurka 60 a Najeriya, kuma yana iya samar da wutar lantarki na kWh 550 a duk shekara. Sai dai idan za mu ci gaba da samar da wutar lantarki ta janareta mai amfani da man dizal, kamar yadda aka saba yi, to, a farashin man dizal na...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa ya bayyana cewa: Shirin dawo da takunkumi kan Iran za shafi mu’amalar Iran da IAEA Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin shari’a da na kasa da kasa, Kazim Gharib-Abod yayin da ya dawo daga shawarwarin karshe na shawarwarin da aka yi tsakanin Iran da tawagar kasashen Turai uku a birnin Geneva, ya bayyana cewa: A cikin wannan zagaye na shawarwarin, Iran ta bayyana a fili ga kasashen Turai cewa, ba su da hurumin aiwatar da doka ta yadda za a iya sake dawo da takunkumi da wa’adinsa ya kare kan kasar Iran, kuma babu wata hujja ta shari’a kan matakin...

Wakilin Kasar Rasha A Vienna Ya Sanar Da Sake Dawo Da Ayyukan Hukumar IAEA A Cibiyar Busharhr Na Iran
Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna ya sanar da cewa: An sake dawo da ayyukan IAEA a cibiyar Bushehr Wakilin dindindin na kasar Rasha a kungiyoyin kasa da kasa a Vienna, Mikhail Ulyanov, ya sanar da dawo da ayyukan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa a cibiyar makamashin nukiliya ta Bushehr dake kudancin kasar Iran. A cikin wani sako da ya aike a shafinsa na X, Ulyanov ya rubuta cewa: Iran ta sake tabbatar da cewa, ko da bayan hare-haren da sojoji suka kai wa cibiyoyin nukiliyar kasarta na zaman lafiya da ke gudana karkashin hukumar ta IAEA ba bisa ka’ida ba, abin kunya ne, a matsayinta ta mamba ta hukumar...
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa Birtaniya, Faransa da Jamus suna shirye-shiryen mayar da takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran a shekarun baya. Kasashe uku na Turai, da aka fi sani da E3, sun gana da jami’an Iran a ranar Talata a wani abin da aka bayyana a matsayin dama ta karshe na ceto huldar da ke gabansu na yin amfani da batun yarjejeniyar nukiliyar 2015, wanda wa’adinsa zai kare a tsakiyar watan Oktoba. Duk da cewa jami’an diflomasiyyar Turai sun yi iƙirarin cewa tattaunawar ba ta samar da hanyoyin warware batun kamar yadda suke bukata ba, amma Tehran ta nanata cewa tana nan a shirye don tattaunawa mai ma’ana, muddin aka mutunta haƙƙinta da...
Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja, bayan ya kammala ziyarar aiki a ƙasashen Japan da Brazil. Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya ce jirgin shugaban ƙasa ya tashi daga filin jirgin sama na Brasília a ƙasar Brazil da ƙarfe 12:57 na rana a ranar Laraba. A cewarsa ya iso Abuja da safiyar ranar Alhamis. Ga hotunan yadda wasu manyan jami’an gwamnati suka tarbi shugaban:
A lokacin ziyarar, ya gana da Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva, da sauran manyan jami’an ƙasar. Ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniya guda biyar da suka shafi sufurin jiragen sama, harkokin waje, kimiyya da fasaha, da kuma noma, da wasu muhimman fannoni a ci gaban Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin mukami ba a zaben 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Najeriya nagartattun shugabanni. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karbi wasu matasa karkashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar hadakar ’yan adawa ta ADC. NAJERIYA A YAU: Matakan da ciwon suga ke bi kafin illata mai fama da shi Ruftawar katanga ta yi ajalin uwa da ’ya’yanta 2 a Zariya El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Najeriya na ganin gazawarta karara ba tare da wani ya musu karin bayani ba. “Ba abin da wannan gwamnatin ke...
Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta kara hada kai da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da samar da kayayyakin agaji da tallafi ga wadanda abin ya shafa. Majiyoyin yankin sun ce al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu. Ku tuna cewa, Gwamna Radda a ranar 18 ga Agusta, 2025 ya bar kasar don hutun makonni uku domin duba lafiyarsa a kasar waje. Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da kuma kungiyoyin bayar da agajin gaggawa ga al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
Ƙungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen Jami’ar Tarayya Kashere (FUK), ta yi zanga-zangar lumana, inda ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka yi da sauran buƙatunsu da ba a cika ba. Zanga-zangar ta fara ne daga ofishin ƙungiyar, ta bi ta ginin shugaban jami’ar, sannan ta ƙare a bakin ƙofar shiga makarantar. Dilan ƙwaya ya shiga hannu a Borno Ambaliya: Gwamnatin Yobe ta samar wa magidanta 250 matsugunin wucin gadi Shugaban ASUU na jami’ar, Dakta Shehu El-Rasheed, ya ce gwamnati ta kasa cika alƙawuran da suka jawo yajin aikin watanni takwas a shekarar 2022. Ya ce har yanzu ba a biya malamai albashin baya ba, haka kuma babu ƙarin albashi na tsawon shekaru. Ya ja hankalin gwamnati cewa...
Babban Hafsan Hafsoshin kasar Iran ya bukaci kasar Pakistan ta bada hadin kai da JMI don kawo karshen ayyukan ta’addanci a kan iyakokin kasashen biyu. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Manjo Janar Abdurrahim Musavi yana fadar haka a lokacinda yake zantawa ta wayar taro da tokwaransa na kasar Pakistan Fiel Mashal Asim Munir a yau Talata. Musavi ya godewa kasar Pakistan da taimakawa kasar a yakin kwanaki 12 na watan yunin da ya gabata., sannan yayi nuni da bukatar kasashen biyu su hada kai don murkushe ayyukan ta’addanci a yankin Sisitan Balucistan na kasar Iran da kuma cibiyarsu dake cikin kasar Pakistan. Ya ce akwai bukatar kasashen biyu su hada kai a wannan fagen bayan an...
“Mun yi tattaunawar gaskiya, amma gwamnati tana yi mana wasa,” in ji shi. Ya ce an yi watsi da rahotanni masu muhimmanci, an kafa manufofin da ke cutar da ilimi, sannan an jefa malaman da suka yi ritaya mummunan hali. “Wannan gwamnati ta raina ilimi da malamai. Mun gaji,” in ji shi. Shugaban ASUU ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ƙi ɗaukar mataki, za ta ɗauki alhakin duk wata matsala da za ta biyo baya. Ya kuma kira mambobin ASUU da su fito ƙwansu da kwarkwata wajen tarukan da za a gudanar a manyan jami’o’i a ranar Talata, 26 ga Agusta, 2025, yana mai cewa wannan shi ne mataki na farko da ƙungiyar za ta ɗauka don nuna rashin...
Ministocin harkokin waje na Iran da Saudiya sun bukaci hadin kan kasashen musulmi don magance matsalolin da al-ummar falasdinu take faskanta a gaza. Sun bayyana cewa akwai bukatar kasashen musulmi su san yadda zasu yi don nisar da abinci zuwa yankingaza da kuma kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a yankin. Tashar taabijin ta Presstv ta bayyana cewa Abbas Aragchi ya tattauna da tokwaransa na kasar Saudia Faisal bin Farhan al-Saud ne a gefen taron ministocin harkokin waje na kasashen musulmi OIC na gaggawa wanda aka gudanar a birnin Jidda na kasar Saudiya . Banda haka ministocin sun yi maganar karfafa dangantaka tsakanin kasashen wadanda suka hada da kasuwanci, yawon shakatawa, da kuma al-adu. Sun kuma ya magana...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yakasai ya kawo misalin tattaunawa da aka yi da kamfanoni a kasar China lokacin gwamnatin Abdullahi Ganduje, inda aka kawo tawaga Kano don duba yiyuwar saka hannun jari amma rashin wutar lantarki ya kawo cikas, ganin cewa dokar gwamnatin tarayya a wancan lokaci ta hana jihohi samar da wutar lantarki ta kansu. Ya bayyana roƙo ga gwamnatin Kano ta yanzu da ta mayar da hankali wajen tabbatar da isasshiyar wutar lantarki, musamman ta hanyar wutar solar ko haɗin gwuiwa da manyan kamfanoni kamar Dangote da BlackRhino, don farfado da masana’antun jihar. A cewar Yakasai, damuwa mafi girma ita ce yadda albarkatun Arewa ake dauka zuwa wasu jihohin kudu don a sarrafa, daga bisani kuma a dawo da su a sayar...
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce a shirye yaki da zauna da Trump da Kuma Putin a gefe guda don tattaunawa da kuma kawo karshen zabar da jinin mutanen kasashen su. Tsahar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnatin kasar Ukraine na fadar haka, ta kuma kara da cewa shugaban kasar Amurka Donal Trump a dayan bangaren ya bayyana cewa a shirye yake ya shiga tsakanin kasashen biyu don fita daga wannan yakin wanda ya gajiyar da dukkan bangarorin. Kafin haka dai Donal Trump ya bayyana cewa idan Zeleski yana bukata to zai iya kawo karshen yakin a rana guda, amma da sharadin ya yi watsi da gurinsa na shiga kungiyar tsaro ta Nato sannan ya...
An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka bayyana taron a matsayin mai matukar amfani. Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi, yayin da manzon musamman na Rasha Kirill Dmitriev ya bayyana cewa yanayin taron ya yi kyau. Putin ya jaddada aniyar kasashen biyu na kawo karshen kiyayyar da suke yi da kuma bukatar cimma matsaya domin kawo karshen yakin Ukraine. Ya yaba da yadda Trump ya fahimci muradun Rasha da kuma burinsa na fahimtar ainihin rikicin. A nasa bangaren, Trump ya tabbatar da cewa tattaunawar ta kai ga cimma matsaya a kan batutuwa da dama, yayin da wasu...
“Tsarin mulkin ADC ta bayyana cewa duk wanda ke neman zama shugaban jam’iyyar, dole ne ya kasance mamba nagari na jam’iyya. Wannan shi ne muhimman bukata ta asali wadda ba za a iya yin watsi da ita ko kauce mata ta kowace hanya ba. “A cewar tsarin mulkin ADC, hanyar da ta dace don cike gurbin jagoranci bayan tafiyar Cif Nwosu ita ce, ta hanyar taron kwamitin zartarwa na kasa.” Tsaagin jam’iyyar ta sake tabbatar da cewa Alhaji Nafiu shi ne halastaccen shugabanta na kasa tare da kira ga ‘ya’yan jam’iyyar da su ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da hadin kai. Ya kuma bayyana kwarin giwa kan ikon hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) na kiyaye...
Shugaban hukumar kula da wasanni ta ƙasa (NSC), Bukola Olopade, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Super Falcons ba su samu kuɗin alawus ɗin da aka yi musu alƙawari ba, yana mai cewa an riga an biya duk ƴan wasan, sai kaɗan daga cikinsu da ke da matsalar asusun banki. Ya ce ya tabbatar da hakan ne daga shugabar ƙungiyar, Rasheedat Ajibade, da kuma hukumar kwallon ƙafa ta ƙasa (NFF). Olopade ya ce ba daidai ne a yi iƙirarin cewa ba a biya kuɗin ba, inda ya ƙara da cewa bai kamata a jefa Ajibade cikin matsalar musanta kalaman da ba ta faɗa ba. Ya bayyana cewa waɗanda ke da matsalar asusun banki su kaɗai ba su samu ba, amma...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Suna buƙatar kawar da makaman nukiliya da kuma kawo ƙarshen maganganun rashin jin daɗi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa kan kawar da makaman nukiliya da kuma amincewa da laifukan tarihi a hukumance kamar harin bam din da aka kai kasar Japan. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya nakalto wasu bayanai daga cikin sanarwar da masu rajin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya suka fitar kan bikin cika shekaru 80 da hare-haren nukiliyar da Amurka ta kai a garuruwan Hiroshima da Nagasaki na kasar Japan. Hare-haren nukiliya na Amurka, wanda ya kashe mutane 150,000 a Hiroshima da 80,000 a Nagasaki, ba...
Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran wato (AEOI) Muhammad Eslami ya bayyana cewa babu jada bayana a shirin nukliyar kasar iran, duk tare da takurawar kasashen yamma. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Eslami yana fadar haka a wani taro nay an jarida a nan Tehran a jiya Talata. Ya kuma kara da cewa kasashen yamma masu babakere kan al-amura a duniya suna son haramtawa mutanen kasar Iran ilmin zamani da kuma ci gaba a fasahar Nukliya. Amma gwamnatin kasar Iran ta dage kan cewa yakin kwanaki 12 da suka dorawa kasar ba zai hana ta ci gaba da shirinta na makamashin nukliya ba. A wani bangare a maganarsa, shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran...
Alausa ya ce dakatarwar, wacce ta shafi dukkan nau’o’in manyan makarantun gwamnatin tarayya an yi hakan ne da nufin dakatar da maimaici da barnatar da dukiyar gwamnati, inda za a yi amfani da kudin domin inganta makarantun da ake da su. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Rano, Alhaji Muhammad Naziru Ya’u, na tsawon watanni uku sakamakon zarge-zargen aikata ba daidai ba. An yanke wannan hukunci ne a zauren majalisa ƙarƙashin jagorancin Shugaban Majalisar, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, bayan kwamitin majalisar kan ƙorafe-ƙorafe ya gabatar da rahoton bincikensa. Yayin gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin wanda shi ne shugaban masu rinjaye, Alhaji Lawan Hussaini Dala, ya ce binciken ya samo asali ne daga ƙorafin da kansiloli tara daga cikin goma na Rano suka sanya wa hannu. A cewarsa, ƙorafin ya zargi shugaban da yin sakacin kuɗi, sayar da shaguna, da karkatar da takin zamani da aka ware wa ƙaramar hukumar, tare da wasu zarge-zarge daban. Lawan ya bayyana...
A wani bayanin hadin giwa wanda ministocin harkokin wajen kasashe 27 suka rattabawa hannu, ya bukaci firai ministan HKI Benyamin Natanyahu ya bude hanya don shigoda abinci cikin gaza, don kawo karshen yunwa da ta bayyana a fili. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa daga cikin kasashen da suka sanyawa bukatar hannu har da kasashen Faransa da Burtaniya da kuma tarayyar Turai a yau Talata. Bayanin ya kara da cewa lalle musibar yunwa da ta sami Gaza, ta kai matsayinda mutum ba zai sawwara shi ba, suna bukatar Natanyahu ya bada izinin a shigar da kayakin agaji zuwa gaza ba tare da bata lokaci ba. A wani labarin kuma yawan mutanen da abincin da ake jefawa...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dole ne dukkan kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen laifukan da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza da kuma kawo karshen killacewa da take yi wa yankin. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake karbar takardar shaidar sabbin jakadun kasashen Habasha, Estonia, Djibouti, Laos, Cambodia, Burundi, Latvia, Myanmar, da Nepal. Ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da kara zafafa laifukan da take aikatawa a kan al’ummar Palastinu marasa kariya da ake zalunta a zirin Gaza. Shugaban na Iran ya jaddada cewa: Dole ne dukkan kasashen duniya musamman kasashen musulmi su kara himma da hadin gwiwa wajen dakile wadannan laifuka a Gaza, da...
Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin ƙalubale da ke fuskantar ‘yan Nijeriya, ciki har da tsadar rayuwa, talauci, yunwa, yawan rashin aikin yi da rashin tsaro, da sauran su. Rahotanni su bayyana cewa akwai tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar dattawa ta 10 a halin yanzu, wanda suka haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Aliyu Wammako (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) da Adams Oshiomhole (Edo)....
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon. A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa. Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi...

Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?
Cin zarafin Amurka ta hanyar haraji ya kuma lalata amincinta tsakanin sassan kasa da kasa. A halin yanzu, fannin shigar da kayayyaki na Amurka ya yi kasa zuwa kashi 13% kacal a kasuwannin duniya. Har ila yau, a jiya Alhamis 7 ga wata, bayanai sun nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar kayayyaki ta Sin ta ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba, inda ta samu karuwa tsakaninta da kasashe membobin kungiyar ASEAN, da Tarayyar Turai, da Afirka, da Asiya ta Tsakiya, wanda ke nuna karfin juriya da kuzari. Hakan ya kuma tabbatar da cewa, cin zarafi ta hanyar haraji ba zai haifar da alfanu na dogon lokaci ba, maimakon haka, budadden tsarin hadin gwiwa...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk bayan shekaru hudu, Najeriya na kara yin zabe kuma ko wanne lokaci ‘yan takara kan dauki alkawura. Ko shekaru nawa wadanda ake zabe ke bukata don cika alkawuran da suka dauka? NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin, latsa nan
Babban Hafsan Hafsoshin sojin Iran ya bayyana cewa; Martanin da Iran za ta mayar kan duk wani hari zai kasance murkushewa ne, kuma ba zata jira izinin kowa ba Babban hafsan hafsan sojin kasar Iran ya gargadi makiya, yana mai cewa: Suna yi wa shahidai alkawari cewa: Za su ci gaba da bin tafarkinsu, kuma duk wani sabon harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci azamar mayar da martani daban da na baya. Babban hafsan hafsoshin sojin kasar ta Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada matsayin wadanda suka yi shahada a safiyar yau Alhamis a yayin bikin tunawa da ranar shahidan Iraniyawa a hare-haren wuce gona da iri, yana mai daukar su a matsayin ginshikan tabbatar da...
Ana zargin ‘yan sandan da karya hannun Sawore Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Qasa sun kutsa inda Hukumar ‘Yan sanda ta Qasa ke tsare xan gwagwarmayar neman haqqin bil’Adama Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da qarfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba. Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da qarfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a qoqarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba.. jiya Laraba ne dai Sowore ya masa...

Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba
Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na kawo karshen yakin da take yi da Ukraine ke gabatowa. A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, inda Moscow ta sanar da lalata jiragen Ukraine guda 18. Yakin da ake yi a Ukraine na kara kamari zuwa ci gaba mai hatsari a daidai lokacin da wa’adin da shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya wa Rasha ke gabatowa, da kuma halayensa na tunzura jama’a,...
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi. Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a madadin gwamnan. Da yake isar da sakon Gwamnan, Farfesa Kawuwa ya bayyana muhimmiyar...
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana jin dadinsa kan aikin titin Eiyenkorin zuwa Afon Ojoku zuwa Offa zuwa Odo zuwa Otin mai tsawon kilomita 49 da ake ginawa. Titin siminti na daya daga cikin manyan tituna hudu da ake ba da tallafi a jihar Kwara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na karbar haraji a misalin hadakar kamfanin BUA. Gwamna AbdulRazaq ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da aiwatar da ayyukan karbar haraji da kuma sauran dimbin tallafin da yake baiwa jihar. “Muna duba ayyukan titunan gwamnatin tarayya da na Jihohi, wannan sabon titin Ilorin/Offa ne, kuma za ku ga yadda yake da inganci, dole ne mu gode wa Shugaba Bola Tinubu kan...
A yau Asabar, hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Beijing ta sanar da cewa, an dawo da wutar lantarki da ayyukan sadarwa a dukkan kauyukan da ibtila’i ya shafa a fadin birnin na Beijing, biyo bayan mamakon ruwan sama da iska mai karfi da aka tafka, yayin da kuma ake ci gaba da aikin ceto wadanda suka bace. Ruwan sama da iska mai karfi da aka yi fama da shi daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Yuli ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da mutane tara suka bace, a babban birnin kasar, kamar yadda aka sanar a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin...
Masu zanga-zanga a duk fadin siriya sun bayyana rashin amincewarsu da ci gaba da kisan mabiya mazhabar Aalawiyya a bakin nruwan tekun medeteranin. Da kuma rikicn da ya kai ga zubar da jnin mutanen kasar a Sewaida saboda shishigin da HKI take yi a cikin al-amuran cikin gida na kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran kasar suna fadar cewam dubban mutanene suka fito suka kuma taru a babban dandalin da ke tsakaiyar suwaida inda suke kira ga gwamnatin rikon kwarya ta HTS ta janye yan ta’addan da ta tura zuwa yankin suwaida don kashe mutanen yankin. Masu zanga zangar suna dauke da alluna wadanda aka rubuta a kansa : a bude hanyoyi don...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na da burin kawo cikas ga harkokin tsaro a yankin, yana mai kira ga daukacin kasashen yankin da su yi taka tsantsan wajen tunkarar irin wannan makirci. Araghchi ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da mataimakin firaministan Hadaddiyar Daular Larabawa kuma ministan harkokin wajen kasar Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan a ranar Juma’a. Ministan na Iran ya ce gwamnatin Isra’ila ta saba da dabi’a ta son kai da rashin bin doka da oda. Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da na Hadaddiyar Daular Larabawa sun tattauna kan sabbin abubuwan da ke faruwa a yankin musamman halin da Falasdinu ke ciki. Har ila yau Araghchi da...
Iyalai ‘yan Sudan da dama ne suka taru a babbar tashar jirgin kasa ta birnin Alkahira, dauke da jakunkuna da kayayyaki a lokacin da suke shirin komawa gida bayan da suka tsere daga rikicin Sudan. Suna cikin dubban ‘yan kasar Sudan da suka rasa matsugunansu da ke kan hanyarsu ta komawa daga Masar zuwa yankunan da sojojin Sudan suka kwato kwanan baya daga dakarun gaggawa na gaggawa a birnin Khartoum da bayanta tun farkon wannan shekara. Iyalan sun kasance suna jiran shiga jirgin kasa da zai nufi birnin Aswan da ke kudancin Masar. Daga nan ne za su yi tafiya ta bas zuwa babban birnin kasar Sudan, Khartoum, a cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayar....
Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana Sai dai, abin dubi a nan shi ne, yadda kusan yanzu a kasar, tabbatar da doka da oda, a cikin kasar, ya koma kachokam, a huunun sojin. ɗuba da sashe na 217 na kudin tsarin mulikin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, wannan sashen, ayyukan soji tun daga na matakin rundunar sojin kasa da ta ruwa da kuma ta sama shi ne tabbatar da bai wa Nijeriya kariya, daga duk wani nau’in hare-haren, da ka iya zuwa, daga ketare, musamman ta hanyar, bai wa iyakokin kasar kariya, musamman bayan shugban kasa,...
Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul. Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya Aikin dai wani bangare ne na Naira biliyan 900 da aka ware domin inganta harkokin sufurin jiragen sama a fadin Najeriya. Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan jim kadan da kammala taron majalisar, inda ya ce tuni har an ba...

Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.
Shugaban marasa rinjaye na Majalisar Wakilai Ali Isah, ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai na Majalisar bayan wata ganawa da mai kula da jihar Ribas Sole a Abuja. Ali Isah, ya bayyana cewa mai kula da jihar ta Ribas ya kasance a gidan a wani bangare na ziyarar da ya saba yi domin yiwa kwamitin riko da ke sa ido kan al’amuran gwamnati. Shugaban marasa rinjaye wanda ya jagoranci taron a madadin shugaban kwamitin wanda ya zama shugaban masu rinjaye na majalisar Farfesa Julius Ihonvere, ya bayyana gamsuwa da kokarin da mai gudanarwa shi kadai yake yi na wanzar da zaman lafiya a jihar. Ya ce mai kula da jihar ya tuntubi...
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara, ta bayyana matukar damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin ban tsoro da rashin fahimta. A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren yada labarai na jam’iyyar, Yusuf Idris Gusau, jam’iyyar APC ta ce yawaitar ‘yan fashi da makami, garkuwa da mutane da kashe-kashe a Zamfara ya kai matakin da ba a taba ganin irinsa ba, yayin da ta zargi gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Dauda Lawal da nuna halin ko in kula. A cewar sanarwar, jam’iyyar ta damu matuka da wani faifan bidiyo na baya-bayan nan inda aka ga sama da mutane 200 mazauna Kaura Namoda suna rokon a taimaka musu biyo...
Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran “IRGC” ya bayyana cewa: Hasashen Raunin Iran ya gushe, kuma ba zai sake dawowa ba Kakakin dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ali Mohammad Na’eini ya jaddada cewa: Ra’ayin cewa Iran mai rauni ce ya raguje kwata-kwata, yana mai jaddada cewa; Yakin kwanaki 12 na baya-bayan nan ya fallasa gazawar makiya wajen karya manufofin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, sannan kuma ya nuna cewa duk wani sabon harin wuce gona da iri zai fuskanci martani mai tsanani da gauni da zai wurga makiya cikin mummunar nadama. Hakan ya zo ne a jawabin da Birgediya Janar Na’eini ya gabatar a jiya Laraba a wajen bikin tunawa da shahidi Ramadan...
Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Manjo janar Musawi ya ce, ko kadan Iran ba ta yarda ko gaskata alkawullan Amurka,balle kuma zancen ‘yan sahayoniya. Babban hafsan hafsoshin sojan na Iran ya kuma kara da cewa, sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana domin kalubalantar duk wan igigi na abokan gaba. Manjo janar Musawi ya bayyana hakan ne dai a lokacin da ya yi tattaunawa ta wayar tarho da ministan tsaron kasar Tajikistan Manjo janar Imam Ali Sabir Zadeh. A nashi gefen, ministan tsaron kasar ta Tajikistan, ya fara da yi wa janar Musawi murnar zabarsa sabon hafsan hafsoshin sojan kasar ta Iran, sannan kuma ya nuna bakin cikinsa akan rashin kwamandojin sojan Iran da su ka yi shahada a sanadiyyar harin...
Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta...
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki. Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar masar kan cewa masar bazata taba kyale mutanen Gaza a halin da suke ciki ba har abada. Ya ce: Gwamnatin kasar Masar tana daga cikin kasashen da suka tsaya don ganin an kawo karshen wannan yakin, tare da Amurkan da kuma kasar Qatar don tabbatar da cewa an kawo karshen yakin . Shugaban daga karshe ya gabatar da shawarar samar da kasashe biyu a matsayin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Duk da alƙawuran sojoji na kama fitaccen jagoran ’yan bindiga, Bello Turji domin hukunta shi kan laifunan ta’addanci, har yanzu ɗan ta’addan bai daddara ba, a yayin da suke ci gaba da farautar sa shi da sauran manyan shugabannin ’yan bindiga da ke addabar ’yan Nijeriya. Dakarun sojin da aka tura ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yamma da sauran ayyukan soji a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Tsakiya, sun yi nasarar halaka manyan jagororin bindiga da dama, ciki har da wasu na hannun daman Turji a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, amma dai har yanzu Turji, wanda ke gudun ɓuya bai shiga hannu ba, duk kuwa da neman sa ruwa a jallo da jami’an...
Kwamitin ya nemi a mayar da sama da Naira miliyan 124, kusan dala 795,000 zuwa asusun gwamnatin tarayya, an kuma bayar da karin wasu kudade da suka hada da Naira miliyan 31.7 da dala 155,923.00, a matsayin wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba. An umarci ma’aikatar da ta kwato Naira miliyan 49.4 da aka biya, domin yin gyaran ba tare da bin ka’idojin sayen kayayyakin ba. Kazalika, an raba Naira miliyan 9.2 ga jami’an ofishin jakadancin, ba tare da cikakkiyar shaida ba. Haka nan kuma, an binciki bankin noma; kan basussuka kimanin Naira biliyan 75.6. Kwamitin ya umarci hukumar da ta buga jerin sunayen wadanda ake bi bashi a akalla a jaridu guda uku na wannan kasa tare da...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Aref ya jaddada cewa: Dole ne a kawo karshen kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankin Zirin Gaza cikin gaggawa ta hanyar daukar matakai na zahiri da kuma dauri daga kasashen duniya. Aref ya rubuta a shafinsa na X a jiya Alhamis cewa: “Mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba saboda yunwa sakamakon hana isar da abinci ga al’ummar Gaza da aka zalunta ya kasance tare da yin shiru na kunya daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa da kasa.” Ya kara da cewa: “Dole...
Aikin gina tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin ya samu gagarumin ci gaba sosai, inda gwamnatin kasar Sin ta sanar a jiya cewa, a ranar 18 ga watan Disamban bana, za a kaddamar da manufar kafa “kwastam mai zaman kansa a duk faɗin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan” a hukumance, wadda ke nufin saukaka bincike da ragewa ko soke haraji. “Ana iya cin moriyar manufofin ba da fifikon harajin kudi a tsibirin Hainan”, sannan “mu’amalar Hainan da kasashen duniya za ta kasance cikin ’yanci da lumana”. A ra’ayin jama’a na kasa da kasa, wannan wani muhimmin mataki ne ga kasar Sin na kara fadada bude kofa ga ketare, wanda ba bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar...
Kwamitin zartaswa na Jam’iyyar APC na ƙasa ya naɗa Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa. Nan take aka rantsar da Nentawe Yilwatda a wajen taron. Kwalara: Mutum 13 sun mutu sama da 236 na jinya a Neja Jirgin Rasha mai dauke da mutum 50 ya yi hatsari a China Nentawe ya yi rantsuwar ne da misalin ƙarfe 02:50 na rana a gaban manyan jiga-jigan jam’iyyar yayin taron NEC karo na 14 da ya gudana a ɗakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, ranar Alhamis. Nentawe, wanda ya fito daga Jihar Filato, shiyyar Arewa ta Tsakiya, shi ne ɗan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a zaɓen 2023.
Ta ce: “Kotu ba ta bayar da umarni ba? Ba ku da ikon karɓe fasfona.” Ba a bayyana wata hujja ko dalili a hukumance ba kan dalilin karɓe fasfo ɗin nata ba, lamarin da ya sa wasu suka zargi cewa ana shirya mata maƙarƙashiya irin ta siyasa. An hangi mijinta, Cif Uduaghan, yana kiran waya cikin sauri yayin da lamarin ya ɗauki lokaci. Bayan ‘yan mintuna, jami’an sun mayar mata da fasfo ɗin ba tare da wani bayani ba. An bar ta ta shiga jirgin kafin ya tashi. Wasu daga cikin fasinjojin da suka shaida lamarin sun bayyana abin a matsayin abin kunya, inda suke kallon lamarin a matsayin amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba. Har yanzu, hukumar shige...
Ta ce: “Kotu ba ta bayar da umarni ba? Ba ku da ikon karɓe fasfona.” Ba a bayyana wata hujja ko dalili a hukumance ba kan dalilin karɓe fasfo ɗin nata ba, lamarin da ya sa wasu suka zargi cewa ana shirya mata maƙarƙashiya irin ta siyasa. An hangi mijinta, Cif Uduaghan, yana kiran waya cikin sauri yayin da lamarin ya ɗauki lokaci. Bayan ‘yan mintuna, jami’an sun mayar mata da fasfo ɗin ba tare da wani bayani ba. An bar ta ta shiga jirgin kafin ya tashi. Wasu daga cikin fasinjojin da suka shaida lamarin sun bayyana abin a matsayin abin kunya, inda suke kallon lamarin a matsayin amfani da ƙarfi ba bisa ƙa’ida ba. Har yanzu, hukumar shige...
Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati wajen danne ’yan adawa. Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Kano. Uwa ta kashe ’ya’yan cikinta biyu saboda kuncin rayuwa An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Lamido, ya ce hukumomi irin su EFCC ana amfani da su ne wajen matsa wa ’yan adawa lamba. Ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ke fuskantar tuhuma kan zargin aikata almundahana. A cewarsa bayan Okowa ya koma jam’iyyar APC, an daina tuhumarsa. Ya kafa misali da wata magana da Sanata Adams Oshiomhole ya taɓa yi. Ya ce: “Da zarar ka shiga APC, an yafe...
Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da hankoron Amurka na tunzura kawayenta, musamman gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila, na yunkurin kawo karshen shirin nukiliyar Iran. Shugaban an Iran ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Aljazeera na kasar Qatar a wannan Talata, inda ya bayyana cewa, za a ci gaba da inganta sinadarin Uranium a kasar Iran nan gaba bisa tsarin dokokin kasa da kasa. Wannan yunkuri yasa an ga bangarorin biyu na Amurka da Isra’ila suna matsa lamba a kan sauran bangarori na duniya, tare da bayyana Shirin na Iran a matsayin mai matukar hadari ga duniya, da nufin samun goyon bayan kasashen duniya kan bakaken manufofisu a kan kasar ta Iran. Dangane da zargin da...
Sakatare-janar na kungiyar Hizbullah Sheikh Naim Qasem ya fitar da wata sanarwa inda ya yi kakkausar suka da Allah wadai da abin da ya bayyana a matsayin yakin kisan kare dangi da Amurka da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasdinu a Gaza, yana mai zargin kasashen duniya da yin shiru a kan laifukan da suka zarce dukkan matakan jin kai da kuma kyawawan dabi’u na ‘yan adataka. “Abin da al’ummar Falasdinawan da ake zalunta ke jurewa a Gaza, tun daga cin zarafi na Amurka da Isra’ila, zuwa ta’addanci, kisan kiyashi, jefa su a cikin yunwa, da kashe jama’a, ya wuce duk wani mataki na lamirin dan adam,” in ji Sheikh Qassem. Ya kuma yi kakkausar suka ga gazawar manyan kasashen...
Kungiyar ta malaman musulumi ta fitar da fatawa da a ciki ta bukaci gwamnatoci da al’ummar musulmi da su yunkura cikin gaggawa domin kawo karshen killace yankin Gaza da aka yi, da kuma wajabcin kai musu abinci da magunguna. Kungiyar malaman musulmin ta kuma bayyana abinda HKI take yi na killace mutanen Gaza fiye da miliyan biyu da haka su abinci da magani,musamman mata, yara da manya,wani babban laifi ne da ba shi da tamka a cikin tarihi, tana mai yin kira ga al’ummu da gwamnatoci da su motsa saboda su taimaki raunana. Kwamitin fatawa da yake a karkashin wannan kungiyar ta malaman musulmi, ya dogara da ayoyin alkrur’ani da hadisan ma’aiki ( s.a.w) da manufofi na shari’a da ka’idoji...
“Saboda barazanar tsaro da ke tattare da al’amuran siyasa, da kuma buƙatar kare lafiyata yayin gudanar da aiki, ina roƙon a dawo min da jami’an tsarona,” in ji ta. Ta kuma haɗa da kwafin hukuncin kotun, inda ta jaddada marnin dawo da ita bakin aiki. Sai dai komawarta majalisa ya haifar da ce-ce-ku-ce, domin Majalisar Dattawa ta ce hukuncin kotun da Sanata Natasha ke dogaro da shi ba dole ba ne a aiwatar da shi, domin ba umarni ba ne kai-tsaye. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Sanatan ya kuma buƙaci jama’ar Kano ta Kudu da Kano gaba daya da su haɗa kai: “Yanzu lokaci ne da ya kamata mu haɗe da juna domin samun cigaba. Mu daina rarrabuwar kai, mu tsaya tsayin daka wajen ganin burinmu ya cika. Idan muka haɗa kai, babu abin da zai hana mu samun ci gaba da makoma mai kyau.“ A ƙarshe, ya roki shugabannin al’umma da sauran ƴan ƙasa da su goyi bayan wannan yunƙuri tare da ƙin amincewa da duk wata dabara ta rarrabuwa da za ta hana nasarar da ake fata daga ƙirƙiro Jihar Tiga. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
A dokar hukumar zabe ta 2010 sashe na 124, biyan kudi ga wani a matsayin cin hanci a kowane irin zabe ko karbar kudi ko kyauta domin jefa kuri’a ko hana jefa kuri’a a kowane zabe babban laifi ne da ke da hukuncin tarar naira dubu 500, 000 ko daurin watanni 12 a gidan gyaran hali ko kuma duka biyu. A kowane zabe kama daga na shugaban kasa zuwa kansila, Hukumar Zabe da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na fuskantar kalubale daga masu sayen kuri’a da ke canzawa masu zabe zaben ra’ayin kan su zuwa zaben wanda aka ba su kudi ko ma kin yin zaben. Duk da kama masu sayen kuri’a da hukumomin yaki da cin hanci...
Sanarwar ta ƙara da cewa, sauran kayayyakin da aka raba sun haɗa da irin shinkafa kilogiram 34,800, irin masara kilogiram 80,000, da lita 23,740 na maganin ciyawa, lita 11,735 na maganin kwari, da buhunan sinadarai na gyaran iri 23,470. A yayin jawabin maddamarwar, Gwamna Lawal ya bayyana cewa rabon takin zamani kyauta na nuni da yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin kawo sauyi a jihar Zamfara ta hanyar noma mai ɗorewa da bunƙasa karkara. Ya ce, “Aikin noma shi ne ginshiƙin tattalin arzikin jiharmu, ba sashe kaɗai ba ne, amma asalin al’ummarmu ne. “Gwamnatinmu ta rungumi taken ‘noma abin alfaharinmu ne’. Noma na nuna ainihin ko su wane ne mu da kuma abin da ya kamata mu ba da...
Har ya zuwa yanzu, ’ya’yan JKS na ci gaba da nuna kyawawan misalai a fannin yayata manufar samar da ci gaba mai inganci, da kyautata jagoranci tun a matakin farko, da sauke nauyin dake wuyansu, da gudanar da ayyuka masu cike da kalubale, wanda hakan ya zamo kashin bayan ingiza nasarar jam’iyyar da ma kasar Sin baki daya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kotun Ƙoli ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin sahihin Gwamnan Jihar Edo. Wannan hukunci ya kawo ƙarshen shari’ar da ake yi biyo bayan zaɓen gwamnan jihar da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, 2024. Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Tinubu ne ya buɗe wa Buhari ƙofar zama shugaban ƙasa — Hadimi Kwamitin alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ne, suka yanke hukuncin a ranar Alhamis. Sun yi watsi da ƙarar da ɗan takarar PDP, Asue Ighodalo, ya shigar, kan cewar hujjojin da ya gabatar ba su da inganci. Mai Shari’a Garba, ya ce Ighodalo da jam’iyyarsa PDP ba su kawo hujjoji masu ƙarfi da za...
Shugaban kungiyar Kurdawa ta kasar Turkiya ( PKK) Abdullah Ojlan ya sanar da kawo karshen amfani da makamai a fafutukar da kungiyarsu take yi na kare hakkokinsu a kasar Turkiya. Shugaban kungiyar Kurdawan na Turkiya wanda yake tsare a kurkuku na shekaru masu tsawo, ya aiko da sako na bidiyo da a cikin ya ce; Har yanzu ina kan kiran da na yi a ranar 27 ga watan Febrairu na ajiye makamai”. Ojlan ya kara da cewa; Muna sanar da kawo karshen amfani da makamai ne bisa radin kanmu, haka na kuma ya ce; Mun shiga Zangon aiki da doka da kuma siyasa da tsarin demokradiyya, wanda shi kanshi nasara ce mai dimbin tarihi ba asara ba.” Kuniyar PKK ta...
Ahmed Musa ya ce zai buƙaci haɗin kai daga duk masu ruwa da tsaki domin ciyar da ƙungiyar gaba. Ya kuma ce zai taimaka wajen samar da kayan aiki da tallafin da ƙungiyar ke buƙata domin ta yi fice a sabuwar kakar wasa mai zuwa. Ya ce: “Ina tabbatar wa kowa cewa da goyon bayanku da na mambobin hukumar, zan yi iya ƙoƙarina don dawo da Kano Pillars matsayin ya kamata a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyi ba kawai a Afirka ba, har ma a duniya.” Ƙungiyar Kano Pillars, wacce ta taɓa lashe kofin NPFL sau huɗu, ta fara shirin tunkarar kakar wasa ta shekarar 2025/2026. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
A ƙarshen makon da ya gabata ne fitacciyar ’yar TikTok wacce aka fi sani da Babiana ta fitar da wani sabon bidiyo tana rusa ihu tana kira ga Shugaba Bola Tinubu da wasu mawaƙan kudancin Najeriya da su shiga tsakaninta da ’yan Arewa a kan abin da tace suna yi mata na cin zarafi tun bayan bayyanar bidiyo tsiraicinta a shekarar 2024. Babiana ta yi bidiyon ne cikin harshen Ingilishi inda ta ce ba a yi mata adalci a Arewa kuma ana barazana da rayuwarta. Sojan Isra’ila ya kashe kansa saboda firgicin yaƙin Gaza Wata bas mai daukar fasinja 56 ta yi hatsari a Jos Ta bayyana cewa tsawon shekara ɗaya ta yi tana raɓe-raɓe saboda ba ta son maganganun...
Majalisar Dattawan Nijeriya ta gindaya sharaɗin dawo da Sanata Natasha Akpoti Uduaghan gabanin cikar wa’adin dakatar da ita da ta yi tsawon watanni shida. Majalisar ta ce ala tilas ne dakatacciyar Sanatar ta bayar da hakuri tare da neman afuwa a hukumance gabanin cika umarnin da ta wata Babbar Kotun Tarayya ta bayar na dawo da ita. Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutum 50 a Amurka An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine Shugaban Kwamitin Labarai da Harkokin Jamaa na Majalisar Dattawa, Sanata Adeyemi Adaramodu ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan hukuncin da kotun ta yanke a kan Sanata Natasha. Ya yi bayanin cewa, a yayin yanke hukuncin da ta bayar da...