Jami’an Tsaron Iran Sun Murkushe ‘Yan Ta’adda Kan Ofishin ‘Yan Sanda A Kudu Maso Gabashin Kasar
Published: 10th, August 2025 GMT
Jami’an tsaron kasar Iran sun murkushe ‘yan ta’adda da suka kai hari a ofishin ‘yan sanda a kudu maso gabashin kasar
Wasu ‘yan ta’adda da ake kira “Rundunar Shari’a” sun yi yunkurin kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Saravan da ke lardin Sistan da Baluchestan na kasar Iran a wani tsararren harin wuce gona da iri kan jami’an tsaron Iran, amma jami’an tsaron da aka tura domin kalubalantansu sun yi nasarar mayar da martani mai gauni kan ‘yan ta’addan.
A cewar majiyoyin Iran, an kashe ‘yan ta’adda uku tare da kame biyu a wadannan gumurzun.
Wani dan sanda mai suna Khodadad Baqiri Saravan ya yi shahada a wani artabu da gungun ‘yan ta’adda a birnin Saravan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza August 10, 2025 Iran Ta Cimma Matsayi A Yaki Kwanaki 12 August 10, 2025 Jefa Agajin Abinci Ta Sama A Zirin Gaza Ya Janyo Shahadan Falasdinawa 23 Tare Da Jikkata Wasu 124 August 10, 2025 Tehran Times: Mai Yiwuwa Iran da Amurka su koma Tattaunawa August 10, 2025 Tel Aviv: Dubban yahudawa sun yi zanga-zangar adawa da yakin Gaza August 10, 2025 Welayati: Makircin Amurka da Isra’ila na kwance damarar Hizbullah ba zai yi nasara ba August 10, 2025 Birtaniya: ‘Yan sanda sun kama akalla mutane 365 a zanga-zangar goyon bayan Falasdinu August 10, 2025 Venezuela: An dakile yunkurin kai wasu munanan hare-hare a cikin kasar August 10, 2025 Pezeshkiyan Ya Yabawa Yan Jarida A Ayyukansu A Yakin Kwanaki 12 August 9, 2025 Yansanda A Burtaniya Ta kama Mutane Fiye Da 200 Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Australia ta gargadi Isra’ila game yunkurin mamaye birnin Gaza
A wannan Juma’a ne Australia ta bukaci Isra’ila da ta janye shirinta na mamaye yankin Zirin Gaza, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kai ga barkewar matsaloli na jin kai a yankin.
Ministar harkokin wajen Australiya Penny Wang a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Australia ta yi kira ga Isra’ila da kada ta bi wannan zabi, wanda zai kara ta’azzara matsaloli a zirin Gaza, tana mai jaddada cewa, tilasta tsugunnar da Falastinawa a wajen yankunansu ya sabawa dukanin dokoki na kasa da kasa.
Wang ta sake nanata kiranta na “tsagaita bude wuta, da shigar da kayan agaji ba tare da wani cikas ko tarnaki ba, da kuma sakin fursunonin da Hamas ke tsare da su tun watan Oktoban 2023.”
Ta yi nuni da cewa, batun kafa kasashe biyu ita ce hanya daya tilo ta hanyar samun zaman lafiya mai dorewa, ta hanyar kafa kasar Falasdinu tare da kasar Isra’ila, da zaman lafiya da tsaro a cikin iyakokin da kasashen duniya suka amince da su.”
Duk da ci gaba da sukar da take yi wa Isra’ila, har yanzu Australia ba ta bi sahun kawayenta na yammacin duniya kamar Canada da Faransa ba wajen bayyana aniyarsu ta amincewa da kasar Falasdinu mai ci cin gashin aknta ba. Duk da haka, ta jaddada cewa “za ta yanke shawara a lokacin da ya dace.”
Kalaman na Wang sun zo ne a matsayin mayar da martani ga wata hira da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi da gidan talabijin na Fox News, inda ya bayyana aniyar Isra’ila na kakaba takunkumin soji a daukacin zirin Gaza. Ya ce, “Tel Aviv na son mika wa dakarun Larabawa yankin gabar tekun don tafiyar da shi,” ba tare da fayyace tsari ko kuma kasashen da za su shiga cikin shirin ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6 August 8, 2025 Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliyar Kasar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba August 7, 2025 Manjo Janar Mousawi: Martanin Iran Nan Gaba Zai Kasance Mafi Muni Kan Makiya August 7, 2025 Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Jaddada Shirinsu Na Tunkarar Duk Wata Barazana August 7, 2025 Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa August 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci