2025-08-06@23:15:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7461

«tsaron kasa»:

    Majalisar Dokokin Bauchi ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a fadin jihar domin haɓaka ci gaba, inganta shugabanci, da kawo sauƙin gudanar da mulki. Wannan na ƙunshe ne a wani ƙudiri da dan majalisar mai wakiltar mazabar Disina, Sale Hodi Jibir, ya gabatar a yayin zaman da Kakakin Majalisar, Abubakar Y. Sulaiman, ya jagoranta. Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama A cewar Jibir, ƙudurin yana dogaro ne da tanadin kundin tsarin mulki na 1999 wanda ya bai wa majalisun dokokin jihohi damar fara shirin ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi, matuƙar an cika wasu sharuɗa da suka haɗa da goyon bayan kashi biyu...
    Kwanturola na shiyyar, Kwanturola AM Alkali, ya yaba wa jami’an bisa yadda suka nuna kwarewa a yayin gudanar da aikinsu.   Kwanturolan ya kuma yabawa muhimmiyar rawar da jama’a ke takawa, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su marawa hukumar kwastam baya a yakin da take yi da zagon kasa ga tattalin arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Za a fara watsa shirin talabijin na musamman mai mai taken “Karfin Al’adu – Tushe da Aikace-Aikacen Tunanin Al’adu na Xi Jinping a Zhejiang”, ta kafar tashar telabijin ta CCTV-1 ta kamfanin CMG, daga yau Laraba 6 ga watan Agustan nan. Za a rika watsa shiri daya duk rana, daga shirin mai jimillar kaso hudu. A lokacin da Xi Jinping ya yi aiki a Zhejiang, kafin ya zama shugaban kasar Sin daga bisani, ya jagoranci ci gaban bangaren al’adun yankin, ta yadda aka samu nasarori masu ma’anar tarihi. Wadannan nasarori sun ba da gudummawar gaske ga habaka tunanin al’adu na Xi Jinping, ta fuskar ka’idoji da kuma aikace-aikace. Shirin ya mayar da hankali kan wannan tsari na tarihi, wanda ke...
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni. Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da wannan kyauta cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook a wannan Larabar. Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina “Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan ’yan wasan da suka rasu fuloti ɗaya da kuma naira miliyan biyar kowannensu,” in ji sanarwar. Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ’yan wasan...
    Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa; Dole ne kasashen musulmi su hana ci gaba da aikata laifuka a Gaza Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim, ya jaddada bukatar kasashen musulmi su dauki matakin hana ci gaba da bala’in jin kai a Gaza ta hanyar diflomasiyya da kuma matsin lamba na siyasa. A safiyar yau Laraba ne shugaba Pezeshkian ya tattauna da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim ta wayar tarho, inda ya jaddada cewa: “Aikin ta’addancin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aiwatar a Gaza ba abin da za a amince da shi ba ne ga kowane mai ‘yanci,” yana mai bayyana fatansa na ganin “kasashen Musulmi za su yi aiki...
    Ya kuma bayyana cewa, tuni aka mika wanda ake zargin ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasa Abbas Araqchi, ministan harkokin wajen kasar Iran, ya taya Ali Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar. A cikin sakon taya murna, Araqchi ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon sakataren majalisar koli ta tsaron kasar, tare da yi masa fatan samun nasara a sabon mukamin nasa. A cikin sakon taya murnarsa, Araqchi ya bayyana cewa, shi da takwarorinsa na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a shirye suke su ba da hadin kai sosai ga Larijani wajen gudanar da muhimman ayyukansa, musamman a fannonin diflomasiyya...
    Birnin Hiroshima na kasar Japan ya yi juyayin cika shekaru 80 da harin makamin nukiliyar Amurka Birnin na Hiroshima ya gudanar da bikin juyayin cika shekaru 80 da kai harin makamin nukiliyar Amurka ta yi a yau Laraba tare da halartar kasashe fiye da 100, inda mahalarta taron suka yi shiru na dan wani lokaci. Kafin a fara yin shiru, a daidai lokacin da bam din nukiliyar Amurka ya fado a kudancin kasar Japan, da dama daga cikin mahalarta taron sun ajiye furanni a wurin taron tunawa da wadanda harin ya rutsa da su. A wajen bikin juyayin, Hiroshima ta sake yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su dauki matakin kawar da makaman kare dangi. Wakilai daga kasashe da...
    Fararen hula 14 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai El Fasher na Sudan Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Sudan ta sanar da cewa:  kungiyar Rapid Support Forces ta kasar Sudan ta Dakarun kai daukin gaggawa ta kashe akalla fararen hula 14 a lokacin da take yunkurin tserewa wani yanki da aka killace a yankin Darfur, bayan shafe sama da watanni 27 ana yaki tsakanin dakarun ‘yan tawaye da sojojin Sudan. Kungiyar lauyoyin gaggawa da ke tattara bayanan cin zarafi da aka yi a yakin, ta kuma watsa rahoton cewa: “An samu raunuka da dama, kana an kama wasu fararen hula da ba a san...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wasu manyan jami’an gwamnati biyu a Ƙasar Ghana, sun rasu tare da wasu mutum shida a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a ranar Laraba. Hatsarin ya faru ne a yankin Ashanti da ke Kudancin ƙasar. Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Ministan Tsaro, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Mohammed, na cikin jirgin soja tare da wasu fasinjoji uku da ma’aikatan jirgin guda uku. Jirgin ya tashi daga birnin Accra, babban birnin Ghana, zuwa garin Obuasi lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa. Rundunar Sojin Ghana ta ce sun daina samun saƙo daga jirgin yayin da yake cikin tafiya. Julius Debrah, shugaban ma’aikatan fadar shugaban...
    “Bari in yi bayani a fili: ba za mu yarda da duk wata dabi’a wacce za ta ruguza dabi’un da muke tsaye a kai ba. Dole ne kowane jami’in gwamnati ya kasance mai lura da al’amuransa, ba wai kawai ofishin ku kuke wakilta ba, har da mutuncin gwamnati baki daya.” In ji Gwamna Abba Kabir   Gwamna Yusuf, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya jaddada cewa, duk wanda aka samu yana taimakawa ko aikata laifuka to zai fuskanci cikakken fushin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    Da safiyar Larabar nan ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da taron tattaunawa game da batun rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda a jawabinsa game da aniyar Isra’ila ta tsananta hare-haren soji, da mamaye daukacin zirin Gaza, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana matukar damuwa kan hakan, yana mai kira ga Isra’ila da ta kauracewa wannan mataki mai hadari, yana mai fatan daukacin sassan da lamarin ya shafa za su gaggauta kaiwa ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai tsorewa. Geng Shuang, ya kuma jaddada muhimmancin aiwatar da sahihin mataki na dakatar da bude wuta yadda ya kamata, ta yadda hakan zai kubutar da rayukan al’umma, tare da bayar da damar sakin wadanda ake tsare...
    Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya.   Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Wasu manyan jami’an gwamnati biyu a Ƙasar Ghana, sun rasu tare da wasu mutum shida a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a ranar Laraba. Hatsarin ya faru ne a yankin Ashanti da ke Kudancin ƙasar. Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Ministan Tsaro, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Mohammed, na cikin jirgin soja tare da wasu fasinjoji uku da ma’aikatan jirgin guda uku. Jirgin ya tashi daga birnin Accra, babban birnin Ghana, zuwa garin Obuasi lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa. Rundunar Sojin Ghana ta ce sun daina samun saƙo daga jirgin yayin da yake cikin tafiya. Julius Debrah, shugaban ma’aikatan fadar shugaban...
    Gwamnatin kasar Sin ta samar da kudi har yuan biliyan 1.015, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 142 ga lardunan kasar daban daban, domin gudanar da ayyukan jin kai, sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa da ta shafi wasu sassan kasar. Rahotanni na cewa ma’aikatar kudin kasar, da ma’aikatar gona da raya karkara, da ma’aikatar albarkatun ruwa ne suka samar da kudaden, wadanda za a yi amfani da su a ayyuka daban daban na tallafawa yankunan da ambaliyar ta shafa, ciki har da birnin Beijing, da lardin Hebei, da Mongolia ta gida da Guangdong. Kana cikin kudin za a samar da tallafin sake shukar da ruwa ya lalata, da ma kayayyakin aikin gona da ambaliyar ta shafa. Kazalika, za a yi amfani da bangaren...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi maƙarrabansa cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin da aka ɗora masa, ya yi murabus. Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya yi biyo bayan belin wani da ake zargin dilan miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Danwawu. Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Wannan lamari ya tayar da ƙura, wanda hakan ya sa Gwamna Abba, ya ɗauki mataki. A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan lamarin. Hakan ta sa ya jaddada buƙatar dukkanin mambobin majalisar da sauran manyan...
    Manoma a Jihar Sakkwato sun koka game da takin da gwamnatin jihar ta ce za ta raba musu don noman damina cewa bai kai hannunsu ba. Duk da cewa an ƙaddamar da rabon takin kusan mako guda da ya gabata. Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da shirin sayar da takin zamani da magungunan noma a farashi mai rahusa a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa domin bunƙasa harkar noma a daminar 2025. Sama da buhu dubu 105 na NPK da UREA aka sayar a farashi mai rangwame. Hakazalika, an sayi maganin kashe ƙwari da keken noma don raba wa...
    Jami’an Alhazai na shiyya-shiyya sun karrama Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa nasarorin da aka samu a aikin hajjin shekarar 2025.   Shugaban jami’an alhazai na shiyya-shiyya, Alhaji Sale Haruna Kafin Hausa ya tabbatar da hakan a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse Babban Birnin jihar.   Ya ce karrama Ahmed Labbo, na da nasaba da gudunmawar da ya bayar da kuma samun nasarar aikin hajjin bana a gida da kuma kasar Saudi Arabia.   Yace wadannan nasarorin sun sanya hukumar ta samu lambobin yabo da kyautuka da dama a kasa mai tsarki.   Alhaji Sale Haruna Kafin Hausa, yana mai cewar jami’an alhazai na shiyya-shiyya...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke ƙarƙashin tsarin fansho na haɗin gwiwa (Contributory Pension Scheme – CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare  da zai taimaka wa rayuwarsu. A wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma bada umarnin a gaggauta aiwatar da karin fansho da aka dade ana jiran shi, tare da kafa mafi ƙarancin adadin fansho domin kyautatawa tsofaffin ma’aikata mafi rauni a tsarin CPS. Wannan umarni ya biyo bayan bayani da Daraktar Janar ta Hukumar Kula da Fansho...
    Mutum 22 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 20 suka jikkata, bayan wata babbar mota da ta yi lodin mutane da dabbobi ta yi hatsari a kan hanyar Lambata zuwa Lapai da ke Jihar Neja. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin. Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato Motar ta taso daga Kano zuwa Legas ne lokacin da hatarin ya auku da misalin ƙarfe 3 na safe, sakamakon gudun wuce ƙima. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta ce dukkanin fasinjojin da ke cikin motar maza ne. An kai gawarwakin Babban Asibitin Suleja, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati...
    Malaman jami’o’i sama da 100 daga Isra’ila sun bayyana cewar jan kafar da ƙasar Jamus ke yi wajen ɗaukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila na iya bai wa ƙasar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza. Wata wasika da masanan suka rubuta wa ɗaya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar SPD da ke mulki a Jamus, ta ce rashin ɗaukar matakin na iya bada damar gudanar da wasu sabbin laifuffuka a Gaza, tare da watsi da irin tarihin da aka koya a shekarun baya. A ranar 22 ga watan Yuli, biyu daga cikin jiga jigan kawancen jam’iyyun dake jagorancin Jamus, sun bukaci ƙasar da ta shiga cikin ƙasashen duniya da ke ƙawance domin gaggauta kawo ƙarshen yaƙin Gaza...
    A jawabin da Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya yi ta bakin mataimakinsa, Farfesa Sanusi Rafindadi, ya yaba da yadda taron ke taimakawa wajen wayar da kai game da wannan cuta mai hatsari. Ya kuma gode wa Hajiya Fatima bisa amsa gayyatar jagorantar taron. Shugabar Sashen Kula da Mata, Farfesa Rahanatu Lawal, ta jaddada buƙatar haɗin kan kowa da kowa wajen yaƙi da cutar. Ta ce mata ba za su iya wannan yaƙi su kaɗai ba, dole ne maza su ba su goyon baya. Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabi akwai Dakta Aminat Jimoh daga Asibitin Koyarwa na ABU. Ta buƙaci mata da su riƙa duba kansu akai-akai, musamman idan suna da tarihin ciwon a cikin danginsu. Ta...
    Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya taya daliban nan ’yan mata ‘yan asalin jihar Yobe su uku da suka lashe gasar harshen Turanci da aka yi a birnin Landan na Burtaniya. A farkon makon nan ne dai Nafisa Abdullahi Aminu da Rukayya Muhammad Fema da kuma Hadiza Kashim Kalli suka zama zakaru a gasar TeenEagle ta 2025 da aka yi a birnin na Landan. Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 A cikin wata sanarwa daga bakin kakakinsa, Bayo Onanuga, ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce nasarar ’yan matan abin alfahari ce ga Najeriya. Tinubu ya kuma yaba wa makarantun da daliban suke karatu, inda ya ce nasarar daliban wata...
    Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan. Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje da lalacewar gonaki da rijiyoyi da sauran su. Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas Mutanen da lamarin ya shafa sun ce suna bukatar agajin gaggawa na abinci da magani da tsaftataccen ruwan sha. Shugaban karamar hukumar ta Tangaza, Isah Salihu Kalenjeni, ya jagoranci wata tawaga...
    Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurinta na farfado da harkar ilimi ta hanyar gyara makarantun da suka lalace wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata. Da yake jawabi yayin wata ziyarar duba makarantu a Makarantar Sakandare ta Murtala Muhammad da ke ƙaramar hukumar Tarauni, Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Haruna Makoda, ya bayyana halin da wasu makarantu ke ciki a matsayin alamar rushewar tsarin ilimi. Kwamishinan ya nuna damuwa game da yadda ake amfani da harabar makarantu ba bisa ka’ida ba, musamman yadda wasu mazauna yankunan suka mayar da harabar Makarantar Murtala Muhammad wajen zubar da shara. Ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin gaggawa don dakile lalacewar muhalli da kuma tabbatar da amintaccen wuri don karatu. ...
    Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya kawata jami’ai 390 da aka daga matsayinsu zuwa sabon mukami a rundunar. An gudanar da bikin kawata jami’an ne a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Gusau, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sanda, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya taya sabbin jami’an murna tare da bukatar su tabbatar da cancantarsu da mukaman da aka ba su, ta hanyar rubanya kishin aiki, ladabi da kwarewa a  ayyukansu. Ya jaddada bukatar jami’an da su dage wajen yin aiki da jajircewa da kuma bayar da ingantaccen tsaro ga al’ummar Jihar Zamfara da Najeriya gaba ɗaya. Daga cikin waɗanda suka sami...
    Iran ba zata taba amincewa wata hukuma ko wata kungiyar kasa da kasa ta kusanci cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban kwamitin tsaron kasa da kuma al-amuran harkokin waje a majalisar dokokin kasar Iran yana fadar haka a ranar Litinin da ta gabata. Ya kuma musanta zancen da wasu suke yadawa na cewa masu sanya ido a ayyukan makamashin nukliya daga hukumar IAEA sun dawo suna ayyukansu a fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ebrahim Azizi shugaban kwamitin ya kara da cewa an  tsara cewa wata tawaga daga hukumar IAEA zata kawo ziyarar aiki nan Tehran don tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar kan abubuwan da suka shafi sayasar hukumar IAEA...
    Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini yana fadar haka a wani wani taro na tunawa da daya daga cikin shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kallafawa kasar. Ya kara da cewa duniya ta sauya sabada nasarar sannan musamman a fagen diblomasiyya da kuma kafofin yada labarai a duniya, wanda ya bar tasiri mai kyau ga kasar. Labarin ya kara da cewa, akalla kasha 60 % na mutanen duniya...
    Ya ce malamin bai fi Sheikh Ahmad Gumi ba, wanda ya gaza yin zaman sulhu da Turji. Guyawa, wanda ya daɗe yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanai, ya ce ba a taɓa yin sulhu da mutum yayin da yake ci wa jama’a zarafi ba. Ya ce: “Za a iya cewa mutum ya yi sulhu alhali yana ci gaba da karɓar haraji daga hannun manoma da tilasta musu noma? Ko kuma yana kashe mutane da ƙond motar jami’an tsaro?” Guyawa ya ƙara da cewa Turji da sauran ‘yan ta’adda kamar Kachalla Choma da Kachalla Haru suna da makamai da kwamandoji da yawa, kuma babu wani abu da ke nuna sun ajiye makamansu. Ya ce malamin da ya faɗi cewa Turji...
    ‘Yansanda a kasar Iran sun bada labarin cewa suna amfani da jiragen leken asiri da wasu kayakin masu aiki da lantarki na zamani don tabbatar da lafiyar masu tattalin 40 zuwa wurare masu tsarki a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Ahmad Ali Goodarzi  shugaban yansanda a nan kasar Iran ya bayyana cewa, yansandan kasar suna aiki tare da rana wajen kyautata ayyukan tsaro a dukkan kofofi shiga Iraki daga Iran guda 6 saboda tabbatar da tsaron masu zuwa 40 na Imam Hussain (a). Ya ce:  Yansa a kan iyakokin kasar suna sanya kula da musamman a kofofin shiga kasar Iraki, wadanda suke da cinkoson mutane. Tare da amfani da jiragen marasa matuka...
    Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cikakken goyon bayan rundunar ‘yan sanda ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano wajen tabbatar da kiyaye dabi’u da yakar munanan halaye a cikin al’umma. CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar wayar da kai da Sakatare na Hukumar, Abba El-Mustapha, ya kai tare da tawagarsa zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sandan Kano. A yayin ganawar, CP Bakori ya yaba da jagorancin hukumar, musamman kokarin da El-Mustapha ke yi wajen tsara harkokin masana’antar Kannywood da kuma kare tarbiyya ta hanyar sa ido mai tsauri. Ya tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin rundunar da hukumar, musamman wajen dakile cin zarafi da amfani da kafafen sada zumunta...
    Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamad Reza Aref ya bayyana cewa kasar Iran tana goyon bayan dukkan shirin zaman lafiya a yankin musamman tsakanin kasashen Armenia da kuma Azarzaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aref yana fadar haka a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Armenia Vahagn Khashaturyan a kasar Tukeministan ake ake gudanar da taron kasashen wadanda basa kan bakin ruwa a duniya a ranar Litinin. Majalisar dinkin duniya ce ta take shrya wannan taron don ci gaban irin wadannan kasashe a duniya karo na 3TH. Aref yace yana fatan zaman zafiya ta dore a cikin kasashen yankin don amfanin kowa. Daga karshe mataimakin shugaban kasan Iran ya bayyana cewa Iran tana goyon bayan kasar Armenia ta...
    Iran ba zata taba amincewa wata hukuma ko wata kungiyar kasa da kasa ta kusanci cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban kwamitin tsaron kasa da kuma al-amuran harkokin waje a majalisar dokokin kasar Iran yana fadar haka a ranar Litinin da ta gabata. Ya kuma musanta zancen da wasu suke yadawa na cewa masu sanya ido a ayyukan makamashin nukliya daga hukumar IAEA sun dawo suna ayyukansu a fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ebrahim Azizi shugaban kwamitin ya kara da cewa an  tsara cewa wata tawaga daga hukumar IAEA zata kawo ziyarar aiki nan Tehran don tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar kan abubuwan da suka shafi sayasar hukumar IAEA...
    ’Yan bindiga sun sace mutum 150 a mabanbantan hare-haren da suka kai kauyuka daban-daban na jihar Zamfara a cikin kwana hudu. Kakakin Gwamnatin jihar ta Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ne ya tabbatar da hakan ga BBC. Sai dai duk da yake bai bayyana hakikanin adadin mutanen da aka sace ba, amma ya ce gwamnatinsu na iya kokarinta wajen ganin ta ceto su. Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’ Haka na zuwa ne a daidai lokacin da malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunna, ya ce kwamitin zaman lafiyar da yake jagoranta ya sami nasarar kulla yarjejeniyar zaman...
    A dai dai lokacinda ake yaki na kwanaki 12 tsakanin Iran da HKI da Amurka, daga ranar 13-24 na watan Yunin da ya gabata, cibiyoyin yakin yanar gizo na kasar Iran sun gwada karfinsu da kuma kwarewansu a wannan fagen fama. Kanfanin dillancin labarai na Tasnim na kuma kasar Iran ya nakalto sharhin wasu kafafen yada labarai na kasashen yamma dangane da shi. Makarantar Midle East Institute ya dubi wannan al-amarin a cikin wabi bayani da ya fitar. Inda yake cewa cibiyoyin yakin yanar gizo na Iran sun shagaltu a wannan lokacin da kare cibiyoyin kasar Iran, amma ta kuma ya aiki da kare kasar taga makiya musamman masu taimakawa HKI a wannan yakin. Kuma da hakan ta kare wurare...
    Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma ɗaukar nauyin ayyukanta a bainar jama’a. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al’amuran da suka shafi jama’a da kuma halin da ake ciki. Ya ce: “A matsayina na ɗaya daga cikin...
    Babbar Kotun Shari’a ta Minna a Jihar Neja ta bayar da wani umarnin na wucin gadi game da gidan rediyon Badeggi Radio Broadcasting Services Ltd, inda ta hana Gwamnatin Jihar  ɗaukar duk wata matsaya da za ta dakatar da ayyukan gidan rediyon. Mai Shari’a Mohammed Mohammed ne ya yanke hukuncin bisa ƙorafin gaggawa (motion ex-parte) da Badeggi Radio Broadcasting Services Ltd da Daraktan gudanarwarta, Mohammed Shuaibu Badeggi, suka gabatar a kotun da ke Minna. A cikin ƙorafin, lauyoyin masu ƙara sun jingina hujjoji da sassa daban-daban na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara), da kuma Dokar Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC Act). Hukuncin kotun ya hana wadanda ake ƙara, ciki har...
    Gwamnatin jihar Legas ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar duk wanda yake haka rijiyar burtsatse a unguwar masu hannu da shuni ta Lekki da ke jihar, ruwan masai yake sha. Babban Sakatare a ofishin da ke kula da magudanun ruwa da tsaftar ruwan sha a jihar, Mahmood Adegbite ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan samar da ruwan sha a jihar a kwanakin baya. DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’ Mahmood ya kuma ce gurbataccen ruwan sha a unguwar zai iya haifar da barazanar lafiya matukar ba a bi hanyoyin da suka dace wajen...
    Ta sake kafa tarihi bayan da jaridar National Concord mallakar MKO Abiola ta naɗa ta a matsayin editan jaridar ta farko, inda A shekarar 1986, aka ɗaga darajarta zuwa matsayin Manajan Darakta kuma Babban Edita mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a tarihin jaridun Nijeriya. Ta auri MKO Abiola a shekarar 1981, kuma ta tsaya tsayin daka tare da shi wajen gwagwarmayar siyasarsa da rikicin da ya biyo bayan zaɓen 12 ga watan Yuni, inda ta bayar da gagarumar gudunmawa a fagen jarida, tare da shafe kusan shekaru 30 tana jan ragamar kafafen yaɗa labarai a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan.   Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa suka zabi zama “sojojin baka” ko “karnukan farautar” ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya nada Ali Larijani babban mai baiwa Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara a matsayin sabon babban sakataren kwamitin kolin tsaron kasar. Larijani ya taba rike mukamin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar daga ranar 15 ga watan Agustan shekarar 2005 zuwa ranar 20 ga watan Oktoban shekarar 2007, sannan ya rike mukamin kakakin majalisar dokokin kasar Iran daga shekarar 2008 zuwa 2020. A ranar Lahadin da ta gabata, Iran ta sake gudanar da wasu sabbin canje-canje a kwamitin tsaron kasar, domin yin nazari a  kan tsare-tsaren tsaro da kuma karfafa karfin sojin kasar. Sanarwar da aka fitar a hukumance ta bayyana cewa, shugaba Masoud Pezeshkian ne zai jagoranci kwamitin tsaron, kuma zai hada da...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheik Naim Qassem ya jaddada cewa, ba a samu wani abu na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba daga bangarenmu ba, amma Isra’ila ta keta wannan yarjejeniya sau dubbai. Da yake jawabi a wajen taron cika kwanaki 40 da shahadar Birgediya Janar Mohammad Saeed Izadi (Hajji Ramadan), Sheikh Qasem ya bayyana cewa, Haramtacciyar Kasar Isra’ila tana fatan ganin an kwace makaman Hizbullah, ta yadda hakan zai bata damar cin karenta babu babbaka a kan kasar Lebanon. Ya ci gaba da cewa, “Abin da ya faru a Siriya ya yi tasiri matuka kan matakan da Isra’ila ta dauka, wanda hakan ya sanya ta yi nadama wajen tsara yarjejeniyar. Shugaban na Hizbullah ya jaddada cewa, Amurka ce...
    Majalisar tsarin mulkin kasar Kamaru ta amince da matakin haramta wa babban abokin hamayyar shugaba Paul Biya Maurice Kamto tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 12 ga watan Oktoba. A watan Yulin da ya gabata ne dai hukumar zabe ta fitar da Kamto daga jerin sunayen ‘yan takarar da aka amince da su. Hukumar ta bayyana cewa an hana Kamto tsayawa takara ne saboda ya tsaya takara a karkashin tutar jam’iyyar Manyedem, wadda ita ma ta goyi bayan dan takara na biyu. Kamto ya daukaka kara a cikin kwanaki biyu. Sai dai shugaban majalisar tsarin mulkin kasar, Clement Atangana, ya amince da hukuncin haramta masa tsayawa takarar. Ba a iya samun damar jin ta...
    A wata ganawa da ya yi da manyan jami’an tsaro a wannan  Talata don kammala dabarun yakin Gaza, Firayim Ministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya amince da kwace yankin zirin Gaza baki daya da karfin soji, duk da  hadarin da ke tattare da sauran fursunonin yahudawa da ke tsare a hannun ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa a Gaza. Ofishin Netanyahu ya fitar da wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ke tabbatar da cewa Netanyahu ya gudanar da wani zaman  shawarwarin tsaro na tsawon sa’o’i uku, inda babban kwamnadan rundunar sojojin Isra’ila ya bayyana yuwuwar aiwatar da Shirin mamaye zirin yakin Gaza baki. Sanarwar ta kara da cewa rundnar sojin Isra’ila  ashirye take domin aiwatar da duk wani matakin da majalisar tsaron kasa...
    Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi, ya yi murabus daga muƙaminsa saboda ce-ce-ku-ce da ya biyo bayan karɓar belin wani wanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi da ya yi. Namadi ya yi murabus ne sa’o’i kaɗan bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ya kafa kan lamarin. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Namadi ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne don “amfanin jama’a gaba daya” da kuma kare gwamnatin a “yaƙin da take yi da sayarwa da shan miyagun kwayoyi.” Sai dai ya dage kan cewa ba shi da laifi, amma ya yarda cewa ra’ayin jama’a na da muhimmanci, kuma yana da kyau ya kare kimar gwamnatin. Tuni Gwamna...
    Gwamnan ya kuma jaddada kudirinsa na ci gaba da tabbatar da adalci, ladabtarwa, da yakar laifukan da suka shafi sha da fataucin miyagun kwayoyi da sauran munanan dabi’u da ke addabar matasa da al’umma jihar Kano. Gwamna ya kuma yi gargaɗi ga duk masu rike da mukaman siyasa da su rika yin taka-tsantsan kan al’amuran da suka shafi jama’a, tare da neman izini daga hukuma kafin su shiga irin waɗannan harkoki marasa daɗi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kuma kara da cewa, a Benuwe, sama da mutane 5,000 ne suka rasa rayukansu a gwamnatin baya.   Nuhu ya bayyana cewa, ayyukan da sojoji ke ci gaba da yi a yankin Arewa-maso-Yamma sun kai ga ceto mutane 11,259 da aka yi garkuwa da su a watan Mayun 2025. An kuma kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga da tawagarsu a jihohin Zamfara, Kaduna, da Katsina.   A wajen taron, akwai manyan shugabannin Arewa da suka hada da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna, Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe, Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume, tare da gwamnoni na yanzu da tsofaffi, Ministoci, Hakimai, da masu rike da mukaman siyasa.   Ribadu ya kammala da jaddada kudirin gwamnati na tabbatar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yayin da ya rage kwanaki biyu a yi bikin bude gasar wasanni ta duniya karo na 12, shugaban kungiyar shirya wasanni ta duniya (IWGA) Jose Perurena Lopez, ya bayyana shirye shiryen da aka yi a Chengdu a matsayin wadanda suka zarci tunani, yana cewa abu ne da zai kafa tahiri. Perurena ya shaidawa kamfanin dilancin labarai na Xinhua a yau Talata cewa, cikin shekaru biyu da suka gabata, yana da burika sosai kan gasar, amma yana ganin abun da aka shirya ya zarce tunaninsa. Ya ce suna da tabbacin birnin Chengdu zai gudanar da gasar wasanni mafi kyau a tarihi saboda ingancin wuraren wasa da na masu aikin sa kai da ma na kwamitin shirya gasar, na nuna matukar kwarewa....
    Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun riga mu gidan gaskiya a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda ya janyo ruftawar ginin gidansu a ƙauyen Dankama da ke Karamar Hukumar Kaita a Jihar Katsina. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na dare a ranar Litinin yayin da waɗanda ajalin ya katsewa hanzari ke tsaka da barci. Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri Bayanai sun ce wasu mutum huɗu waɗanda su ma lamarin ya rutsa da su an gaggauta miƙa su asibiti domin samun kulawa. Magidancin da aka yi wa wannan babban rashi, Muhammad Sani Garba, yayin ganawa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kotun tsarin mulkin Kamaru ta haramta wa jagoran adawar ƙasar, Maurice Kamto tsayawa takarar shugaban ƙasa, a babban zaɓe mai zuwa na watan Oktoba, kan abin da ta bayyana rashin cika ka’idojin tsayawa takara. Lauyansa, Hippolyte Meli Tiakouang ne ya tabbatar wa manema labarai hukuncin kotun wanda ba za a iya ƙalubalanta ba, bayan kammala zamanta na wannan Talata. A cewarsa, kotun ta yi watsi da ƙarar da suka shigar kan matakin hukumar zaɓen ƙasar na cire shi daga cikin jerin ’yan takarar da za su fafata a zaɓen ranar 12 ga watan Oktoban bana. Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Mista Kamto...
    Sashen cinikayyar samar da hidimomi na Sin ya ci gaba da bunkasa yadda ya kamata cikin watanni shida na farkon shekarar nan ta 2025, inda ya karu da kaso takwas bisa dari kan mizanin shekara. A cewar ma’aikatar cinikayya ta Sin, darajar hidimomin shige da fice a wannan wa’adi ta kai kudin Sin tiriliyan 3.89, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 544.9. Cikin wannan adadi, alkaluman hidimomin da aka fitar daga kasar Sin ya karu da kaso 15 bisa dari, wato darajar da ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 1.69, yayin da na wadanda aka shigo da su kasar ya karu da kaso 3.2 bisa dari, daidai da kudin Sin tiriliyan 2.2. Sai kuma gibin cinikayya a fannin na bayar da hidimomi...
    Tsohon Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Adamu Maina Waziri, ya caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da cewa gwamnatinsa ta kere ta tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta fuskar muni, wanda a yanzu ƙasar tana cikin mummunan bala’i.  Waziri, wanda jigo ne a jam’iyyar ADC (African Democratic Congress), ya bayyana haka ne a yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Trust TV. ’Yan gida ɗaya sun kitsa garkuwar ƙarya domin karɓar N5m a wurin mahaifinsu Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa “Babu ta inda gwamnatin Tinubu ba ta gaza ba. Ta gaza a dukkan fannoni, kama daga kan tsaro, tattalin arziki, yaƙi da cin hanci saboda komai ya tabarbare. Nijeriya ta koma baya...
    Sadarwar intanet da lantarki da ruwa da sauran abubuwan bukatun jama’a na yau da kullum sun game baki dayan kasar Sin. Ni ganau ce ba jiyau ba, domin na yi tafiye-tafiye da dama, na shiga kauyukan kasar Sin, kuma cikinsu babu inda na ziyarta da ban ga wadannan abubuwa da na ambata ba. Idan muka ajiye batun sadarwar intanet a gefe, majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ita ce majalisar koli mai tsara dokoki a kasar, kuma wakilanta na fitowa ne daga dukkan bangarori da yankunan kasar. Sabanin yadda muka saba gani a kasashenmu inda wakilan jama’a ke tarewa a babban birnin, wakilan jama’a a kasar Sin na komawa ne cikin al’ummominsu, kuma a nan suke tattaro ra’ayoyi da shawarwari da...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa; Haɗin kai tsakanin kafofin watsa labarai, diflomasiyya da fage na tabbatar da ƙarfi da ci gaban ƙasa A jajibirin ranar ‘yan jarida ta kasa, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ziyarci hukumar kula da harkokin yada labarai ta kasa (NBO) inda ya gana da shugaban kungiyar da sauran jami’an kafofin yada labarai na kasar. A yayin taron, shugaban kungiyar ta NBO, Peyman Jebli, ya yi maraba da minista Araqchi, ya kuma yaba da kokarin da hukumomin diflomasiyya ke yi wajen inganta manufofin harkokin waje da kuma kare muradun kasar. Mista Jebli ya bayyana hadin kai da hadin gwiwa tsakanin harkokin diflomasiyya da kafafen yada labarai da cewa yana da matukar muhimmanci wajen...
    Mai ba da shawar ga Jagora ya jaddada cewa: Iran za ta mayar da martani da karfi ga duk wata gwamnati da ke neman yin amfani da hanyar Zangezur ta hanyar da ba ta dace ba Ali Akbar Wulayati, mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran kan harkokin kasa da kasa, ya yi gargadin cewa: “Duk wata gwamnati a yankin ko a wajenta da ke son maimaita gwajin da aka yi a baya game da hanyar Zangezur, za ta fuskanci martani mai karfi daga Iran.” A shafinsa na Twitter, Ali Akbar Welayati ya rubuta cewa: “A nan ma, wasu gwamnatocin da ba su nuna halin ko-in-kula ba, ba ruwansu da muradun kansu da na yankin,...
    Sojojin Yemen sun kaddamar da hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa a haramtacciyar kasar Isra’ila da makami mai linzami Dakarun sojin Yemen sun sanar a yau cewa: Sun kai hari kan filin jirgin saman Lod da ke birnin Jaffa, domin mayar da martani kan laifukan kisan kiyashi da kakaba masifar yunwa da makiya yahudawan sahyoniya suka aikata a kan ‘yan’uwansu a zirin Gaza, da kuma mayar da martani kan gungun yahudawan sahayoniyya da suke kutsawa cikin masallacin Al-Aqsa tare da wulakanta farfajiyar sa mai alfarma. A cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar ta bayyana cewa; Rundunar ta kai wani harin soji mai inganci a kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da...
    Dokta Muhammad Tahir da aka yi wa barazanar kisa ya bayyana abin da ya gani na masifa a Gaza Dr. Muhammad Taher ya dauki kashe-kashe da kakaba yunwa da ke faruwa a Gaza a matsayin abin tunawa da abin da ya faru da Imam Husaini (a.s), kuma Gaza ita ce Karbala ta wannan zamani. A jajibirin taron tunawa da Arbaeen na Imam Husaini (a.s) Dr. Muhammad Taher ya halarci taron kiran Al-Aqsa karo na hudu a birnin Karbala mai tsarki. A gefen taron, Dr. Muhammad Taher ya kasance bako a cikin shirin “Tattaunawa da Baki” a tashar talabijin na Al-Alam. Dr. Muhammad Taher wani likitan fida ne dan kasar Iraqi wanda ya sadaukar da kansa wajen kula da mutanen Gaza...
    An samu bullar sabani da rikici a tsakanin ‘yan sahaypniyya game da mamaye Gaza a daidai lokacin da ake ci gaba da kai hare-hare da kuma rage yawan sojojinsu a yankin Yakin kisan kiyashi yana ci gaba da gudana a Gaza ta hanyar ci gaba da kai hare-hare kan mai uwa da wabi, tare da nau’o’i daban-daban na aiwatar da kashe-kashe da kuma kakaba yunwa. Duk da yadda kasashen duniya ke ci gaba da nuna bacin ransu kan irin girman kai da gwamnatin mamayar Isra’ila ke nuna wa, kafafen yada labaran haramtacciyar kasar isra’ila sun rawaito cewa: Majiyar fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ta bayyana cewa ya yanke shawarar mamaye yankin gaba daya da aka killace saboda yana...
    Matar Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Hajiya Hadiza Ahmad Sama’ila Yakawada, ta kaddamar da Makon Shayar da Nono na Duniya na bana, tare da kira ga iyaye mata da mazajensu da su ba wa jarirai nono kacokam na tsawon watanni shida na farko. A yayin kaddamarwar, Hajiya Hadiza ta bayyana cewa shayar da jarirai nono na da muhimmanci matuƙa wajen tabbatar da lafiyar yara da kuma inganta cigaban su tun daga ƙuruciya. Ta kuma bayyana cewa makon yana da nufin wayar da kan jama’a musamman a tsakanin iyalai game da amfani da shayar da nono, tare da ƙarfafa gwiwar ma’aikatan lafiya da su ci gaba da fafutukar wayar da kai a fadin karamar hukumar. A nata jawabin, Sakatariyar Lafiya...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya reshen Abuja ta sanar da cafke wasu mata ’yan gida ɗaya da ake zargi da kitsa garkuwar ƙarya da zummar karɓar kuɗin fansa na naira miliyan biyar a wurin mahaifinsu. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya Ta bayyana cewa sun samu tushen faruwar lamarin ne bayan da wani Mista Innocent, ya kai rahoton ɓacewar ’yarsa mai shekaru 16 a ranar 18 ga Yuli, 2025. Mista Innocent ya shaida wa ’yan sandan cewa ’yar tasa ba ta dawo gida ba tun bayan da ta fita domin...
    Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba wa ɗalibar nan ’yar shekara 17 daga Jihar Yobe da ta lashe Gasar Turanci ta Duniya, Nafisa Abdullah Aminu, kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa ta OON. Ya buƙaci a gayyato Nafisa da malamanta na harshen Turanci musamman zuwa Fadar Shugaban Ƙasa a karrama su saboda yadda suka ɗaga sunan Najeriya a idon duniya a fannin ilimi. “Ina kira da babbar murya cewa a a ba wa Nafisa kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa daga Gwamnatin Tarayya.” A cikin saƙon da ya wallafa a safiyar Talata, Pantami ya ƙara da cewa malaman Nafisa sun cancanci irin kyautar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun sojin Nijeriya sun hallaka aƙalla ’yan ta’adda 17 na ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a wasu hare-haren kwantan bauna da suka kai a jihohin Borno da Adamawa a tsakanin ranakun 23 ga Yuli zuwa 2 ga Agustan 2025. Kyaftin Reuben Kovangiya, Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. Buni ya shirya bikin karrama daliban da suka lashe gasar duniya An soka wa jami’in Sibil Difens wuka har lahira a Jigawa Ya bayyana cewa sojojin ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun kai hare-haren ne a ƙananan hukumomin Bama, Konduga, Gwoza, Magumeri, da Biu a Jihar Borno, da kuma Michika da ke Jihar Adamawa. A cewarsa, an...
    Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya shirya da wani gagarumin biki domin karrama Nafisa Abdullah ’yar shekara 17 da Rukayya Muhammad Fema ’yar shekara 15, wadandan ’yan asalin jihar ne, bayan sun lashe gasar duniya da aka gudanar da kasar Birtaniya. Nafisa ta lashe Gashar Iya Turanci ta Duniya a yayin da Rukayya ta lashe Gasar Muhawar ta duniya, inda suka doke kasashe 69 a Gasar TeenEagle na shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan. Bayan doke dalibai sama da 20,000 da suka fafata a gasar inda suka wakilci Najeriya daga Kwalejin Nigerian Tulip (NTIC) da ke Jihar Yobe. Nafisa da Rukayya dukkansu sun ci gajiyar shirin tallafin karatu na Gwamna Mai Mala Buni wanda ya kunshi cikakken dawainiyar karatun...
    Wasu zauna gari banza sun burma wa wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) wuka har lahira a Kasuwar Shuwarin da ke ci Karamar Hukumar Kyawa a Jihar Jigawa. Kakakin Hukumar NSCDC reshen Jihar Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani, ya bayyana cewa an kai wa jami’in hari ne a lokacin da yake bakin aiki a ranar Linitin a lsashin sayar da shanu na kasuwar (Kara), inda ’yan iskan suka kai wa jami’in hari. Ya ce “Maharan da ake zargin suna xauke da wuqaqe ne suka farma   jami’in, suka yi masa mummunar varna, inda maharan suka far wa jami’in da wukake, kuma abin takaici, ya rasa ransa nan take. Kakakin ya bayyana cewa, “Wanda abin ya shafa mai suna Sufeto Bashir Adamu...
    Gwamnan ya bayyana cewa za a gudanar da babban taron girmamawa ga Nafisa a faɗin jihar, sannan ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da gyaran makarantu da ɗaukar malamai domin ganin kowanne yaro a Yobe ya samu ingantaccen ilimi kamar Nafisa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dokki ta Jihar Katsina ta amince da sabuwar Dokar Masarautu ta jihar, bayan ta yi wa daftarin dokar karatu na daya har zuwa na uku. A sabuwar dokar da aka yi wa kwaskwarima, wadda take jiran sa hannun Gwamna Umaru Dikko Radda, gwamnan jihar ne kadai ke da ikon daga darajar sarki. Kazalika ta ba wa gwamnan jihar kadai ikon zabar masu zabar sarki, sa’annan ta kara yawan da masu zaben sarki daga mutane hudu zuwa biyar. Kauran Katsina, Galadiman Katsina, ’Yandakan Katsina da Durbi su ne mutum hudu da aka sani a mastayin masu zabar sarki, amma yanzu dokar ta da Marusan Katsina Hakimin Shargalle, sarautar da aka ba wa tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Hadi Sirika....
    Jiniyoyin gargadi sun tashi a HKI bayan da sojojin Yemen sun cilla sabbin makamai masu linzami kan HK. Kafafen yada labarain na HKI sun bayyana cewa makamai na yemen sun haddasa tashin jiniyoyin ne a tsakiyar kasar da kuma yankunan da kuma yankunan da ke gewaye da birnin Qudus. Majiyar sojojin yemen kuma ta bayyana cewa sun cilla makaman ne don tallafawa falasdinawa a gaza, wadanda HKI take kashewa da yunwa da kuma makamai a ko wace rana. Labarin ya bayyana cewa dubban dubatan yahudawan sun kideme suna kuma neman inda zasu fake daga boma-boman kasar ta yemen. Hukumar kwana, kwana, ta HKI wato ‘Israel’s Magen David Adom (MDA)’ bata bada wani rahon jikata da kuma rushe-ruehen da aka samu sanadiyyar faduwar...
    Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta kafa kwamitin tsaron kasa, wanda zai kula da sabbin matsalolin tsaron kasa, da kuma da kuma karfin sojojin kasar . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne tare da dogaro da duka da 176 da kundin tsarin mulkin kasar. Labarin ya kara da cewa , kafa kwamitin wani mataki ne, na kyautata harkokin tsaron kasar, da kuma samar da mafita ga wasu sabbin matsalolin tsaro wadanda kasar take fuskanta. Da kuma tabbatar da cewa jami’an tsaron kasar a shirye suke su fuskanci duk wata barazanar tsaron da zasu bullowa kasar nan gaba. Banda haka kwamitin shine zai shirye dabarbarin kare kasar tsakanin bangarori daban0daban na sojojin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa kasar Rasha tana shirin kara dankon zumunci da kungiyar Brics saboda fuskantar takunkuman tattalin arziki wadanda kasar Amurka ta daura mata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Maria Zakharova kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha tana fadar haka, ta kuma kara da cewa, kungiyar BRICS kungiya ce wace kasar Rasha ta dogara da ita don magance irin wadannan matsaloli. Sannan kasashen iya magance takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka suke dorawa kasar Rasha. Zakharova, ta kara da cewa kasashen Global south da BRICS sune kawayen Rasha a kan abinda ya mshafi matsalolin takunkuman tattalin arziki da kuma kawayenta a cikin harkokin siyasar duniya. Zakharova ta kara...
    A birnin Paris na kasar Faransa dukkan kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka yi tattaki daga danlin Repuplican zuwa dandalin Bastille saboda nuna rashin amincewar su da kisan kiyashin da HKI take yi a gaza, da kuma hana shiga abinci a yankin wanda ya kai ga mutuwar falasdina ko saboda yunwa ko kuma saboda makaman yahudawan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tun farkon yakin Gaza a cikin watan Octoban shekara ta 2023 munanen kasashen Turai musamman faransa suke nuna rshin amincewarsu da kasashe kashen da HKI take yi a Gaza, amma a lokacin mafi aywan gwamnatocin kasashen yamma sun zuwa HKI su bayyanawa Natanyahu kan cewa suna bayanta don hamas ce ta fara yakin HKI tana...
    Gwamnatin kasar Burtaniya ta bayyana cewa zata fara amfani da wata yarjeniya da ta cimma da kasar Faransa kan maida dukkan yan gudun hijira ko bakin hauren da suke shigo kasar ta kwale-kwale zuwa kasar kasar ta Faransa. Daga yau Talata. Shafin labarai na yanar gizo Arab News ya nakalto cewa gwamnatocin biyu sun amince kan cewa Burtaniya zata maida dukkan wadanda suka iso Burtaniya ta amfani da kananan kwale kwale ta maida su Faransa, a inda ita kuma faransa zata mikawa kasar Burtaniya masu nrman mafaka wadanda suke da iyali a kasar Burtaniya dai dai adadin da ta mayar daga Burtaniya. Firai ministan kasar Burtanita Keir Starmer da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel macron sun amince haka a cikin...
    Hukumar Kula da Dokokin Hanya ta Jihar Legas (LASTMA) ta rufe wani gidan casu mai suna Vaniti Club House da ke kan titin Adeola Odeku a Victoria Island bisa laifin karya dokar harkokin sufuri ta shekarar 2018. A cewar LASTMA, an rufe gidan casun ne saboda ajiye motoci ba bisa ƙa’ida ba a gefen titi da kuma toshe hanyoyi, lamarin da ke haddasa cunkoso da barazana ga lafiyar jama’a. Wannan matakin ya samu jagorancin babban daraktan hukumar, Olalekan Bakare-Oki, tare da sashen ceto da tabbatar da doka. Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos Kwalara Ta Kashe Mutane 5 A Lagos, An Kai 60 Asibiti Ranga-Ranga Hukumar ta ce wannan mataki na ɗaya daga cikin tsarin...
    Gobara ta ƙone gidan Barden Bauchi Hakimin Ƙasar Lere, Alhaji Sulaiman Muhammad da ke unguwar Gwallaga a cikin garin Bauchi. Sa’in Tafawa Balewa Mallam Yunusa Ado ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa “Wannan gobara ta auku ne akamakon kawo wutan lantarki da hantsi ranar Litini 4/8/2025 lokacin Hakimin na Fadarshi dake garin Zwall.” Mallam Yunusa ya ce, “Gidan ya ƙone ƙurmus, an yi asarar dukiya mai tarin yawa amma an yi sa’a  da hatsin ne ya faru, amma ba a samu asarar rai ba, kuma babu wanda ya jikkata. Ya bayyana cewa makwabta da zuwan jami’an sun taimaka an aka fitar da motar da ke  garejin zuwa waje, amma an tafka asara. Sa’in yace “Muna addu’ar Allah Ya Maida...
    Tsohon jami’in harkokin wajen Tarayyar Turai Joesp Borrell, ya yi gargadi game da ci gaba da rashin taka rawar gani daga bangaren kasashen Turai dangane da ayyukan cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi, yana mai cewa irin wannan rashin hankali ya sa kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta zama abokiyar tarayya a cikin laifukan da Isra’ila ke aikatawa. Joesp Borrell ya bayyana hakan ne a cikin wani fashin baki wanda aka buga a cikin jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya. “Wadanda ba su yi aiki ba don dakatar da wannan kisan kiyashi da kuma keta dokokin kasa da kasa, duk da cewa suna da ikon yin wani abu kan hakan, to tabbas suna da hannu a cikin wadannan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza. Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana ga Isra’ila”. “Amincin da kake da shi a wajen Isra’ilawa zai ƙara ba ka damar sanya Firaiminista [Benjamin] Netanyahu da gwamnatinsa a kan hanya daidaitacciya: A kawo ƙarshen yaƙin, a dawo da mutanen da ke tsare a kuma daina gallaza wa Falasɗinawa,” kamar yadda suka rubuta. Roƙon nasu na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa Netanyahu na ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan soji a Gaza...
    Kwalejin Kiwon Lafiya ta Najeriya ta fara taron shekara-shekara karo na 19 na kimiyya da nufin yin amfani da sabbin fasahohi da kirkire-kirkire wajen kawo sauyi a fannin likitanci a kasar.   Da yake yiwa manema labarai jawabi gabanin taron a Sokoto, shugaban kwalejin na kasa, Dokta Peter Ebeigbe ya ce taron zai tattauna hanyoyin da za a bi domin tunkarar manufofi aiwatarwa mai inganci da shigar da kamfanoni masu zaman kansu a fannin ilimin likitanci na gaba da digiri na biyu.   Gidan Rediyon Najeriya dake Sokoto ya ruwaito cewa, ana sa ran taron zai kuma tattauna kan ingancin aikace-aikacen kirkirariyar fasaha ta Artificial Intelligence (AI) da illolinsa na isar da sahihanci mai inganci.   Shugaban na kasa ya...
    Gwamnatin tarayya ta ce tace a shirin ta sauya wuraren dake bushe a sassan arewacin Nijeriyaza a raba naira miliyan  miliyan 3.4 kuma akasarin wadanda zasu amfana da wannan za su kasance mata ta hanyar Shirin ACReSAL.   Da yake jawabi a wajen bude taron kwanaki 10 na masu ruwa da tsaki kan tsarin kula da tsare-tsare (SCMP) na sabbin magudanan ruwa guda 11 a fadin Jihohi bakwai na tarayya a Ilorin, kodinetan ayyukan ACRESAL na kasa, Mista Abdulhamid Umar, ya ce za a gudanar da aikin ne ta hanyar shirin kawo sauyi na dogon lokaci.   Jami’in kula da ayyukan na kasa na ACRESAL Adamu Shettima wanda ya samu wakilcin kwararre a bangaren kula da ayyukan ruwa na gwamnatin...
    Kungiyar masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa reshen jihar Nasarawa ta kalubalanci kungiyar tabbatar da gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari (NS-TA&G), da su tabbatar da zargin nuna son kai wajen sauke nauyin da babban Akanta Janar na jihar, Ahmed Musa Mohammed ke yi.   Ko’odinetan kungiyar na jiha Abimiku Dangana Solomon ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga wani jawabi da Mista Lazarus Salaki, ko’odinetan kungiyar NS-TA&G2 na jihar ya yi a wani taron manema labarai da aka gudanar a garin Lafia babban birnin jihar.   Mista Abimiku Dangana ya ce, hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan bai hana masu rike da mukaman gwamnati da ma’aikatan...
    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba wa sabbin ma’aikatan aikin gona 1,038 da aka dauka aiki takardun su na kama aiki.   Bikin, ya gudana ne a gidan gwamnatin Kano.   Da yake jawabi yayin bikin gwamnan ya gargade su da su guji cin hanci da rashawa, ya kuma bukace su da su yi wa jihar hidima cikin himma da gaskiya.     Ya ce matakin ya nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da jihar ke yi na inganta samar da abinci da kuma habaka arzikin iyali.     Gwamna Yusuf ya bayyana daukar ma’aikata a matsayin cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da kuma wani muhimmin mataki na cimma wadannan manufofin.  ...
    Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle. Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu. Jami’in Sadarwar Zamani na Gwamnatin Jihar Yobe, Yusuf Ali, ya bayyana cewa Rukayya ta samu kafa wannan tarihi ne a dalilin zurfin tunani da kuma kaifin basirarta da kuma fahimtar al’amuran duniya, duk kuwa da ƙarancin shekarunta. Ɗalibar daga Kwalejin Nigerian Tulip International (NTIC), Rukayya, ta ɗauki hankalin alƙalan gasar da sauran jama’a saboda ƙarfin hujjojinta da ta gabatar da kuma iya bayani mai ganawarsa...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fada a ranar Litinin cewa kimanin yara 28 ne ake kashewa a kullum a zirin Gaza sakamakon harin bama-baman Isra’ila da kuma yunwar da ta jefa a l’ummar yankin a ciki. Kungiyar ta yi bayanin a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, yaran Gaza na fuskantar kisa “sakamakon tashin bama-bamai, rashin abinci mai gina jiki, yunwa, da kuma rashin muhimman kayan agaji da ayyukan kiwon lafiya. UNICEF ta jaddada cewa yara a Gaza na bukatar abinci, ruwa, magunguna, da kuma kariya. Mafi mahimmanci kuma shi ne, suna bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa.” A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa, sama da mutane...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk da karin kudin da gwamnatoci a matakin jiha suke samu daga asusun tarayya, ’yan Najeriya da dama suna korafin ba sa gani a kas.   Manazarta dai sun ce ko kafin karin ma ya kamata ya yi a ce ayyukan da gwamnatcin jihohi suke yi sun fi da ake gani Ko mene ne ya sa jihohi “ba sa kashe karin kudaden da suke samu yadda ya kamata”? NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Wannan shi ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai. Domin sauke shirin,...
    Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba wa ɗalibar nan ’yar shekara 17 daga Jihar Yobe da ta lashe Gasar Turanci ta Duniya, Nafisa Abdullah Aminu, kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa ta OON. Ya buƙaci a gayyato Nafisa da malamanta na harshen Turanci musamman zuwa Fadar Shugaban Ƙasa a karrama su saboda yadda suka ɗaga sunan Najeriya a idon duniya a fannin ilimi. “Ina kira da babbar murya cewa a a ba wa Nafisa kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa daga Gwamnatin Tarayya.” A cikin saƙon da ya wallafa a safiyar Talata, Pantami ya ƙara da cewa malaman Nafisa sun cancanci irin kyautar...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yaba da ziyarar kwanaki biyu da shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya kai a Pakistan, wanda a sakamakon an bude wani sabon shafi na karfafa alaka mai karfin gaske tsakanin Iran da Pakistan da suke makwabtaka da juna. “Ziyarar shugaban kasar Pakistan na da matukar muhimmanci,” in ji Esmaeil Baghaei yayin wani taron manema labarai na mako-mako a ranar Litinin a birnin Tehran, yayin da yake magana kan ziyarar Pezeshkian. Baghaei ya ba da misali da matsayar  da kasashen suka dauka na yin ciniki cikin ‘yanci bisa yarjejeniyar da ta dace a matsayin wani muhimmin batu na ziyarar, yana mai cewa wannan lamari mai matukar muhimmanci ga bangarorin biyu. Ya kara da cewa, yayin ziyarar, an...
    Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi. Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen iskar gas na Amurka da kuma zuba jarin dala biliyan 3.3 a masana’antun Amurka a wata yarjejeniya da tawagar shugaban Amurka Donald Trump ta gabatar. Wannan yunƙurin ya ci tura. Jami’an Afirka ta Kudu sun ce, a cewar kamfanin dillancin labaran  Reuters, harajin Amurka zai iya janyo asarar dubunnan ayyuka, musamman a fannin noma da kera motoci. A wani taron manema labarai, ministocin ciniki da...
    Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin  ƙasar Birtaniya. Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a Gasar ‘UK Global Finals’, sakamakon fintinkau da ta yi wa takwarorinta na ƙasashe daban-daban da ke jin harshen Ingilishi a duniya. Wannan nasara ta lashe wannan babbar gasa da Nafisa ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a mahaifarta, Jihar Yobe. Nafisa ta wakilci Najeriya ne daga Kwalejin Tulip International College (NTIC), Jihar Yobe....
    Kungiyar Hamas, ta musanta kalaman da wakilin Amurka Steve Witkoff, inda ya yi ikirarin cewa kungiyar ta bayyana aniyar ta na yin watsi da makamanta. Kungiyar ta tabbatar da cewa, tsayin daka da makamanta hakki ne na kasa kuma na shari’a matukar dai an ci gaba da mamaye Falastinu, kuma dukkanin dokoki na kasa da kasa sun amince da hakan a ka’idojin MDD. Kungiyar ta jaddada cewa, “wadannan makamai ba za a yi watsi da su ba sai ta hanyar dawo mana da cikakken ‘yancinmu na kasa, wato kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, mai cin gashin kanta tare da Kudus a matsayin babban birninta.” A baya can, Hamas ta zargi Witkoff da gudanar da wani shiri a ziyarar da...
    Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi da kuma takin zamani kyauta ga al’ummar mazaɓarsa. Da yake ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobin garin Goɗɗiya da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, Sanata Buba ya ce, “A bana, za mu yi allurar rigakafin dabbobi 85,000 a wannan yankin na Majalisar Dattawa.” Ya ce a baya an yi wa dabbobi kimanin 40,000 allurar rigakafin a fadin yankin. “Na yi imanin cewa wannan abu ɗaya ne daga ayyukan wakilci wa mutanenmu manoma da makiyaya. ’Yan Najeriya ne kamar mu duka, suna zaɓe mu, kuma suna ba da gudummawa sosai ga tattalin arzikin ƙasar nan. “Wannan ba wani abu ba ne na musamman amma na yi imanin cewa wani abu...
    Hukumar Yaki da Hamada da Sauyin Yanayi ta Kasa ta kammala shirye-shiryen dasa itatuwan dabino miliyan hamsin (50,000,000) a jihohi goma sha ɗaya 11 da ke fama da fari a Najeriya. Daraktan Hukumar, Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin dasa itatuwan dabinon da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya ce za a dasa itatuwan dabino guda dubu dari biyar (500,000), tare da wasu nau’o’in itatuwa na gida a faɗin jihar Jigawa. Alhaji Salihu Abubakar ya yi kira ga jama’a da su rungumi al’adar dasawa da kula da itatuwa domin magance matsalolin hamada, zaizauar ƙasa da sauyin yanayi. A cewarsa, Hukumar tana aiki tukuru a jihohin da ke  fama da fari a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata D’Tigress kyautar Dala dubu 100 da gidaje da lambar girmamawa ta OON, a matsayin karramawa bayan lashe kofin gasar ta bana. Shugaban ya kuma ba masu horar da ’yan wasan dala 50,000 kowannensu. Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025 Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ya ’yan wasan ƙwallon ƙafa mata wata Super Falcons makamanciyar wannan kyautar ta dala 100,000 da lambar girma. A wannan Litinin din ce tawagar ’yan wasan ƙwallon kwando ta mata ta Nijeriya ta koma ƙasar bayan lashe gasar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka, wato Afrobasket. Tawagar ta D’Tigress ta...
    Yau Litinin, rokar Long March-12 ta kasar Sin ta harba wasu jerin taurarin dan adam masu samar da hidimar intanet zuwa sararin samaniya. Rokar ta tashi ne da misalin karfe 6:21 na yamma, daga cibiyar harba kumbuna ta kasuwanci dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin. Rokar ta yi nasarar harba jerin taurarin irinsu na 7 masu zagaye a kusa da doron kasa, cikin da’irarsu da aka tsara. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin ‘yan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin yahudawan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. A lokacin da yake halartar taron manema labarai da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya gudanar a yau Litinin, Araqchi ya ce: Na farko dai ya zama wajibi a gare shi ya girmama dukkanin shahidai: shahidan juyin juya halin Musulunci, shahidan tsaro mai alfarma (1980-1988), da dukkanin shahidan da suka sadaukar da rayuwarsu wajenkare kasa, tun farko-farko har zuwa yau, musamman ‘yan jaridu da shahida yakin matsorata masu wuce gona da iri na...
    Mashawarcin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Za su koma shawarwari da Amurka ne yayin da suke dauke da makamai a hannu Mai baiwa ministan harkokin wajen Iran shawara Sa’ed Khatibzadeh, ya jaddada cewa: Iran ba za ta sake amincewa da Amurka kan duk wata tattaunawa da za ta iya yi ba, yana mai cewa makomar yankin ba kamar yadda Amurka da Isra’ila suke zato ba. A ziyararsa ta farko da ya kai kasar China bayan hare-haren da Amurka da yahudawan sahayoniyya suka kai kan kasar Iran a baya-bayan nan, Khatibzadeh ya yi wata fitacciyar hira da gidan talabijin na Phoenix, inda ya tattauna muhimman batutuwa da suka hada da ci gaban Shirin makamashin nukiliyar Iran, dangantakar shiyya da...