Aminiya:
2025-08-10@14:51:25 GMT

An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi

Published: 10th, August 2025 GMT

Wata kotu a N’Djamena, babban birnin Chadi, ta yanke wa tsohon firaminista kuma madugun adawa, Succes Masra, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari.

Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito kotun ta samu tsohon firaministan da laifin kalaman ƙiyayya, nuna wariyar ƙabilanci da kuma tayar da tarzomar da ta rikiɗe zuwa kisan kiyashi.

Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza

Kotun a ranar Asabar ta ce ta sami Mista Masra da laifi kan rawar da ya taka wajen tayar da rikicin ƙabilanci wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 42 a ranar 14 ga Mayu — waɗanda galibi mata da yara ne a yankin Mandakao da ke kudu maso yammacin Chadi.

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata ce, Lauyan gwamnati mai shigar ƙara, ya nemi kotun ta yanke wa Succes hukuncin ɗaurin shekaru 25 a gidan ɗan marina

An dai kama Masra a ranar 16 ga Mayu wanda aka tuhuma da “tayar da tarzoma da fitina, haɗin kai da ƙungiyoyi masu riƙe da makamai, taimakawa wajen kisan kai, ƙona gine-gine da kuma wulaƙanta kaburbura.”

An gurfanar da tsohon firaministan tare da wasu maza kusan 70 da ake zargi sun taka rawa a wannan kisa.

Masra, wanda asalinsa ɗan kudancin Chadi ne ya fito daga ƙabilar Ngambaye, kuma yana da karɓuwa sosai a wajen yawancin Kiristoci da masu bin addinin gargajiya a yankin kudu, waɗanda ke ganin ana nuna musu wariya daga gwamnatin da Musulmai suka fi rinjaye a N’Djamena.

A lokacin shari’ar, lauyoyinsa sun ce babu wata hujja tabbatacciya da aka gabatar a kotu da za ta tabbatar da laifinsa.

A watan Yuni, lauyoyinsa sun ce ya yi yajin cin abinci na kusan wata guda a gidan yari.

Masra ya tsere daga Chadi bayan mummunan matsin lambar da aka riƙa yi wa mabiyansa a 2022, sai dai ya dawo ne a ƙarƙashin afuwar da aka cimma a 2024.

AFP

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Succes Masra

এছাড়াও পড়ুন:

Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr

A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League.

Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi.

MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da Pakistan

Martinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara.

Kafin haka, ya shafe shekaru bakwai yana murza leda a Real Sociedad bayan fitowa daga makarantar horas da kwallon kafarta, sannan ya shafe shekaru shida a Bilbao.

Martinez, wanda ya buga wa kasar Spain wasanni 21 tsakanin 2013 zuwa 2023, ya koma Al-Nassr wadda ta kare a mataki na uku a gasar Saudi Pro League a kakar da ta gabata, wadda Cristiano Ronaldo ya zama dan wasa mafi zura kwallaye da kwallaye 25.

AFP

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr
  • An Maka Gwamnatin Neja Da NBC A Kotu Kan Barazanar Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM
  • Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 
  • Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027
  • Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh
  • Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara 
  • Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu
  • Buƙatar Katange Iyakokin Nijeriya Don Tabbatar Da Tsaro 
  • Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana