2025-09-20@13:05:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6356
«Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano»:
Gundumar Bakori ta jihar Katsina ta kaddamar da shirin dashen itatuwa domin rage zaizayar kasa a yankin. A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin aikin gona, Cigarin Bakori Alhaji Shehu Ishiye ya fitar, ya bayyana cewa Hakimin Bakori, Makaman Katsina Alhaji Garba Tukur Idris, ya yi kira ga jama’a da su daina sare itatuwa ba...
Sheikh Na’im Kassima wanda ya gabatar da jawabi a jiya juma’a ya kuma kara da cewa; A halin yanzu kungiyar gwagwarmaya tana fuskantar matsanancin yanayi mai hatsari,tare da jaddada cewa; Wanzuwar HKI, manufarsa ita ce a samar da wani yanki na turai da Amurka a cikin wannan yankin domin hana al’ummar yankin ci gaba da...
Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar....
Tsarin ya ƙunshi na “ kwas na ƙwarewa kan lamarin koyarwa na gajeren lokaci wanda akan yi wata uku zuwa shida ne, bayan haka ne waɗanda suka yi kwas ɗin ne za su cancanci yin rajista da hukumar , har su samu Lasin na amincewa da sun cancanta su yi aikin koyarwa.” Tsarin na ma’aikatar...
An tsinci gawar Igbonna Uzoma, kwamandan hukumar da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) a otel da ke birnin Kalaba, Jihar Kuros Riba, a ranar Juma’a. Rahotanni sun ce Uzoma, wanda aka dawo da shi aiki daga wata jiha zuwa Kuros Riba a kwanan nan, bai daɗe da kama aiki a sabon ofishin ba...
Ukraine ta ce Rasha ta kai sabbin hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuka wasu yankuna da dama na kasar cikin dare. A gabashin birnin Dnipro, an kai hari kan wani gini kuma an ji ƙarar fashewar wasu abubuwa a Zaporizhzhia kusa da tungar da ke zaman iyakar dakarun Rasha da na Ukraine...

An Rufe Makarantu 6 Masu Zaman Kansu A Kano Saboda Karin Kudin Makaranta Da Tilasta Iyaye Sayen Littafai
A ci gaba da kokarin da take yi na tsaftace harkar ilimi, wata kotu a Kano ta bayar da umarnin rufe wasu makarantu masu zaman kansu nan da nan, 6 saboda saba ka’idojin jihar da suka hada da kara kudin makaranta da kuma tilasta iyayen yara sayan litattafai na dole da sauran tsarabe-tsarabe da suka...

Miyetti Allah ta roki Gwamntin Kwara da ta sa baki kan rufe Kasuwar Kara da Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi
An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa. Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema...
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauya sunan ma’aikatar harkokin mata, yara da nakasassu a hukumance zuwa “Ma’aikatar harkokin mata, yara da masu bukata ta musamman.” Wannan dabarar yanke shawara, ga kwamishiniyar harkokin mata Ambasada Hajiya Amina Sani Abdullahi, ta nuna irin kwakkwaran kudurin gwamnati na inganta mutunci, hada kai,...
Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Jigawa, ta shirya taron yini daya a birnin tarayya tare da hadin gwiwar ELIP kungiyar farar hula ta musamman, domin tattara kayan aiki na kasafin kudin 2026. A nasa jawabin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Alhaji Ibrahim Babangida Umar Gantsa ya bayyana mahimmancin taron, inda...
Kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya (MƊD) ya ƙasar samu Isra’ila da laifin aikata kisan ƙare dangi kan Falasɗinawa a zirin Gaza. Wani sabon rahoton kwamitin binciken ya ce akwai ƙwararan hujjoji da za a iya cewa Isra’ila ta aikata huɗu daga cikin nau’ika biyar na kisan ƙare dangi a ƙarƙashin dokokin ƙasa da...
Da yake magana game da taron, Maiha ya ce sadarwa ita ce jigon ciyar da harkar kiwon dabbobi gaba, “Bayan wannan taron, muna sa ran za ku yi amfani da dabarun ku don ƙara faɗaɗa labarin fannin kiwo. “Muna yaba wa ƴ an jarida bisa aikinku na ƙwarewa da muke sa ran za ku ci...
Dubban ’yan Nijeriya ne ke zaune a ƙasar Saudiyya ba tare da takardun izinin zama ba, musamman a biranen Makkah da Madina. Rayuwarsu cike take da fargaba da rashin tabbas, a yayin da suke yin ayyukan hannu ko ƙananan sana’o’i ba tare da wata kariya ta doka ba. A yayin aiki Hajjin shekarar nan...
A ɓangaren al’umma an samu halartar shugaban ƙaramar hukumar Faskari Hon. Surajo Aliyu Daudawa da Ɗan Majalisa dokokin mai wakiltar ƙaramar hukumar Faskari injiniya Sama’ila Mu’azu Bawa. Sauran sun haɗa da Hakimin Faskari da kuma na Mai Ruwa da wakilan al’umma da masu riƙe da masarautar gargajiya da sauran al’umma. Sai kuma ɓangaren ɓarayin daji...

Jakadan Iran A Majalisar Dinkin Duniya Ya Ce: Kwamitin Sulhu Ya Rasa Damar Tattaunawa Da Fahimtar Juna
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron...
Shugaban kasar Faransa ya jaddada cewa; Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya tabbatar a yammacin jiya Juma’a cewa: Zai amince da kafa kasar Falasdinu a ranar Litinin mai zuwa a birnin New York. Macron ya bayyana cewa: Amincewa da kasar...
Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya. A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli...

Kamfanin Kasar Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Kayayyaki Ga Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Sudan Ta Kudu
Kamfanin man fetur na kasar Sin (CNPC), ya mika wasu kayayyakin agaji ga dubban mutanen da ambaliya ta raba da matsugunansu a jihar Unity mai arzikin man fetur dake arewacin kasar Sudan ta Kudu. Daraktan sashen hulda da jama’a na reshen kamfanin CNPC a Afrika Ren Yongsheng, ya ce gudunmuwar ta kunshi tantuna, da barguna,...
1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani...
Wata matar aure ta shiga hannu kan zargin ƙone fuskar ’yar mijinta, Fatima Talba mai shekara 17 da tafasasshen man girki, a unguwar Jiddari Polo da ke Jihar Borno. Wata majiya ta tabbatar da cewa lamarin ya faru a ranar Asabar da ta gabata, bayan wata taƙaddama da kaure tsakanin Fatima da matar ubanta. Sauya...
Tawagar gwamnatin jihar Jigawa ta shiga sahun sauran kasashe da suka halarci taron kasa da kasa na Halal da ke gudana a Malaysia (MIHAS), domin neman jari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa na tattalin arziki. Tawagar karkashin jagorancin Kwamishinan Harkokin Kiwo, Farfesa Abdurrahman Salim Lawal, ta hada da Dr. Saifullahi Umar, Darakta-Janar na Hukumar Zamanantar...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa a shirye ta ke, ta haɗa kai da APC, idan an shirye karɓar sharuɗansu. Kwankwaso, ya faɗi haka ne a gidansa da ke Miller Road a Kano, lokacin da ya karɓi baƙuncin tsohon jigon APC a jihar, Buhari Bakwana,...
Muhawara game da sanya doka a kan makarantu masu zaman kansu yana ta ci gaba a ciki da wajen jihar Kaduna saboda ƙaruwar makarantun masu zaman kansu a cikin ƴ an shekarun nan musamman a cikin sabbin unguwanni da ke cikin ƙwaryar Kaduna. Abubuwan da jama’a ke magana a kai sun haɗa da tabbatar da...
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona...
Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum shida bisa zargin tono gawar wani mutum a kabari tare da cire sassan jikinta domin yin asiri. Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Kawuji Sarki, mai shekaru 39, ya amsa laifin. Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Janye...
Albarkacin bikin murnar cika shekaru 100 na kafuwar Jam’iyyar Zhigong ta Sin, shugaban kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, JKS, kana shugaban kasar Xi Jinping ya aika wasikar taya murna, kuma a madadin kwamitin tsakiyar JKS, ya taya dukkan ’yan Jam’iyyar Zhigong murna tare da nuna musu gaisuwa. Xi Jinping ya jaddada cewa, a kan...
Ya ce ma’aikatar ta tsaya a kan tabbatar da ladabi da bin doka don haka babu wani shugaban makaranta da za a bari yana sabawa doka ko karbar kudade a hannun dalibai da iyaye ba tare da an hukunta shi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...
Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro. Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi...
Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya dawo bayan shafe tsawon lokaci baya jihar biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Tinubu ya yi. A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci, wadda tsohon Hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ekwe Ibas (rtd), ya jagoranta. ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar...
Gwamnatin jihar Sakkwato ta dakatar da wasu shugabannin makarantun sakandare guda shida kan zargin karbar kudi daga hanun dalibai na bisa ka’ida ba. Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na jihar, Farfesa Ahmad Ladan Ala ne ya amince da dakatarwar. Matasan Nijeriya sun koma yin ci-rani a Nijar da Chadi Akasarin masu kai mana hare-hare daga...
A yau a Nijeriya, kalmar “Japa” ta zama gamagari wajen bayyana yadda matasa da dama ke barin ƙasar domin neman ingantacciyar rayuwa a wasu ƙasashe. Abin da ya bambanta shi yanzu shi ne inda suke nufa: ba kawai Turai da Amurka ba kawai, har ma da ƙasashen Afirka maƙwabta. Yawaitar tsadar rayuwa da ƙarancin ayyukan...
Sai yace “A’a ba haram ba ne, kawai dai mutanena ba su san shi ba ne.” Annabi (SAW) ya taɓa cewa kar a ci tafarnuwa a shigo masallaci, aka tambaye shi: “Ya Rasulallah haram ne?” Sai ya ce “A’a ba na haramta abin da Allah bai haramta ba, kawai dai ni ne ba na son...
Matatar Dangote ta sanar da dakatar da tsarin ɗaukar mai kai tsaye daga matatar, inda ya ce wannan mataki zai fara aiki daga ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sanarwar ta bayyana cewa matakin zai hana masu siye marasa rajista shiga wajen saye kai tsaye tare da ƙarfafa amfani da tsarin kai wa kyau bayan...
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce akalla mutane 1,666 mazauna jihar Legas sun rasa ransu ta hanyoyin da ba su dace ba, ciki har da kashe kansu, tsakanin farkon 2020 zuwa karshen 2024. Wannan bayani ya fito ne daga bakin likitan binciken gawarwaki na rundunar, ACP Samuel Keshinro, yayin gabatar da rahoton bincike kan kisan...
A cewar ma’aikatar, dakatarwar ta na nufin samar da damar ci gaba da tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki da kuma yin cikakkiyar bitar tsarin harajin da tasirinsa na dogon lokaci ga tattalin arziki. A watan Afrilu 2025, Kwaturola Janar na Kwastom, Adeniyi, ya bayyana shirin sake gabatar da harajin kashi 4 bayan tattaunawa...
Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI. Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin...
Matsayar kasar Faransa na amincewa da Falasdinu a matsayin kasa a hukumance a babban taron zauren majalisar dinkin duniya dake zuwa, ya kawo tarnaki sosai a alakar diplomasiya tsakanin ta isara’ila. Shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya sanar tun a watan yuli cewa faransa za ta amince da falasdinu a matsayin kasa, za ta shiga...
Wani rahoto da kwamitin bincike da Gwamna Caleb Mutfwang ya kafa kan kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a Jihar Filato ya ce akasarin masu kai hare-hare suna fitowa ne daga jihohin da ke makwabtaka da Filato. Shugaban kwamitin, Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas, ya bayyana cewa sun gana da kabilu daban-daban da kungiyoyin...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira ga kwamitin tsaro na MDD da ya shiga tsakaninta da kasashen turai guda 3 don tabbatar da cewa sun zabi diblomasiyya da Iran mai makon fito na fito da ita. Tashar talabijan ta Presstv daga nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Alhamis ya...
An sabunta wannan ƙididdiga kusan shekaru shida kamar yadda ya kamata a yi. Abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, ƙididdiga da bayanai su kasance masu sahihanci kuma a yawaita samun su. “An sabunta ƙididdigar, kuma ya nuna mana ainihin halin da muke ciki. Don haka, duk wani ra’ayi na...
Aƙalla mutane 58 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon barkewar cutar Kwalara a ƙananan hukumomi 14 daga cikin 20 da ke jihar Bauchi. Haka kuma, an samu sabbin mutane 258 da suka kamu da cutar a faɗin jihar. Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza An yanke wa Soja hukuncin...
Kazalika, masu sukar na ganin cewa, gwamnatin ta yi watsi da irin halin ƙuncin rayuwa da musamman talakwan ƙasar, ke ci gaba da fuskanta, kamar dai, na ci gaba da hauhawan farashin kayan masarufi da ƙarin kuɗin Man Fetur da ƙarin kuɗin wutar lantarki da ƙarancin albashin da ake biyan ma’aikata, musamman na gwamnati, wanda...
Rundunar Brigade ta 17 na Sojojin Najeriya da ke Katsina ta raba buhunan takin zamani ga manoma a ƙauyuka shida da ke kusa da sansanin Natsinta, cikin Jibia da Katsina. Kwamandan brigade ɗin, Birgediya Janar Babatunde Omopariola, ya ce an yi hakan ne don ƙarfafa dangantakar sojoji da al’umma, tare da taimaka musu wajen noma,...
Ƙasar Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a dakatar da yaki a Gaza nan take kuma ba tare da sharaɗi ba. Daftarin kudurin na majalisar ya kuma buƙaci Isra’ila ta cire duk wani takunkumi kan kai agaji ga yankin na Falasɗinawa. Wani ya sace munduwar...
Benfica ta sanar da naɗa José Mourinho a matsayin sabon kociyanta, domin maye gurbin Bruno Lage, wanda ƙungiyar ta karo bayan da Qarabag ta doke ta a gasar Zakarun Turai ranar Talata. Benfica ta kori Lage duk da cewa wasa ɗaya kawai ya yi rashin nasara a dukkanin gasa a bana. Wata sanarwa da Benfica...
A cewarsa, jihar ta ba da fifiko wajen samar da kudade, kayayyakin more rayuwa, da kuma samun damar koyo tun bayan hawansa kujerar mulki. Gwamnan ya kara da cewa, yadda gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ilimin ’ya’ya mata, bayar da tallafin karatu, da rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta, ya taimaka...
Rahotannin cibiyoyin kididdiga a HKI sun ambaci cewa, ana ci gaba da samun yin hijirar yahudwa zuwa waje wanda shi ne mafi girma a cikin shekaru da dama. Jaridar “Ma’ariv” ta amabto wani makwararre a fagen kididdiga yana cewa; Shekarar 2024 ta fuskanci ficewar mutane masu yawan gaske daga “Isra’ila” saboda yakin da ake yi...
Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita. An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta...
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun shirya horar da aikin ceto yayin ambaliya, a Ƙaramar Hukumar Auyo. Taron horaswar ya haɗa masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban,...
Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama wasu mutane tara da ake zargi da shirin yin garkuwa da kansu tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 7. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce waɗanda ake zargin na da hannu...