Majalisar Dokokin Kano Ta Karɓi Ƙarin Kasafin Kuɗi Na 2025
Published: 11th, August 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta karɓi ƙarin kasafin kuɗi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tattaunawa da amincewa.
Bisa wasikar da bangaren zartarwa ya aika wa Majalisar, ana neman amincewar ta kan ƙarin kasafin kuɗi na kimanin Naira biliyan 170 domin aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a fadin jihar.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ya bayyana cewa bangaren zartarwa yana neman wannan ƙarin kuɗi ne domin gudanar da ingantattun ayyuka da za su amfani rayuwar al’ummar jihar.
Bayan tattaunawa, ‘yan majalisar sun mika kudirin ga Kwamitin Majalisa kan Kasafin Kuɗi domin yin bincike da shirye-shiryen aiwatar da dokokin da suka dace.
A wani labarin kuma, majalisar ta karɓi wasika daga bangaren zartarwa mai ɗauke da sunan Barrista Saidu Yahaya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC).
Nadin nasa ya biyo bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Barrista Muhyi Magaji Rimin Gado.
An mika sunan sabon shugaban zuwa ga Kwamitin Majalisa kan Ƙorafe-ƙorafe domin ci gaba da tantancewa da gudanar da matakan doka.
Majalisar ta dage zaman ta zuwa washegari Talata 12 ga watan Agustan 2025.
Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: bangaren zartarwa
এছাড়াও পড়ুন:
An Rantsar Da Sabbin Mataimaka Na Musamman A Karamar Hukumar Auyo
An shawarci sabbin mataimaka na musamman da su kasance masu adalci da gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu a ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa.
Shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Alhaji Binyaminu Ahmad Adamu Kafur ne ya bayar da wannan shawara yayin bikin rantsar da sabbin mataimaka na musamman 69 da aka gudanar a Auyo.
Alhaji Binyaminu Kafur ya sake tabbatar da kudirin majalisar wajen yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin samar da kayayyaki more rayuwa, don tabbatar da ganin kowa ya amfana da mulkin dimokuraɗiyya.
Ya yi kira ga jama’a da kada su gaji wajen yin addu’a domin samun nasarar shugabanni wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwarsu.
Shi ma a nasa jawabin, Alhaji Umar Jura ya yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa zabar mutanen da suka dace don yin aiki a lokacin mulkinsa.
Ya yi kira ga waɗanda aka naɗa da su bada haɗin kai tare da yin aiki tukuru don nuna amincewar da aka nuna gare su.
A madadin waɗanda aka naɗa, Malam Yakubu Muhammad Auyo da tsohon shugaban rikon ƙwarya Mika’ila Auyo sun gode wa shugaban ƙaramar hukumar bisa amincewa da su don yin wannan aiki.
Haka kuma sha alwashin haɗin kai domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Usman Muhammad Zaria