Za a biya ma’aikata 445 garatitun sama da biliyan ɗaya a Kebbi
Published: 9th, August 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sama da biliyan ɗaya a matsayin kuɗin garatitu ga iyalan ma’aikatan gwamnati 445 da suka rasu.
Wannan biyan zai shafi tsoffin ma’aikatan jihar, ma’aikatan wucin-gadi, ma’aikatan ƙananan hukumomi, da malaman firamare.
Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfaraAna sa ran biyan kuɗin zai fara daga kan watan Disamba 2024 zuwa Maris ɗin 2025.
Gwamna Idri, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da walwalar ma’aikata da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima.
Ya ce biyan haƙƙoƙin ma’aikata ba wasa ba ne, kuma gwamnatinsa za ta yi tsayin daka wajen ganin an biya su a kan lokaci.
Wasu tsoffin ma’aikata sun yaba da wannan mataki, amma sun roƙi gwamnan da ya ci gaba da biyan sauran waɗanda ba su shiga jerin wannan sahun ba.
Sun ce akwai ɗimbin masu jiran haƙƙinsu, kuma idan ana biyan kowa a hankali, cikin lokaci kaɗan za a rage yawan masu jiran kuɗi.
Sun kuma buƙaci gwamnati ta duba tsarin fansho na jihar don inganta shi.
A cewarsu, yawancin masu karɓar fansho a Kebbi na cikin halin ƙunci saboda kuɗin da ake ba su ba ya wadatarwa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Garatitu gwamnati Walwala
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
“Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.
A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.
An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan ƙananan hukumomi, tare da samar da kujeru, littattafai, kayan koyo da horar da malamai domin tabbatar da ingantaccen ilimi ga yaran jihar.
Haka kuma, ana gina sabuwar kasuwa ta zamani a Nasarawa Burkullu, da ake sa ran za ta zama cibiyar bunƙasa sana’o’i da kasuwanci ga mazauna yankin. A bangaren ruwa da wutar lantarki kuwa, ana tono ruwan sha da kuma shimfiɗa sabbin hanyoyin rarraba wuta zuwa asibitoci, makarantun firamare da sakandare, da cibiyoyin gwamnati.
Dantawasa ya ce, an riga an kammala wasu daga ayyukan tare da ƙaddamar da su, yayin da sauran ke kan gaba, abin da ya tabbatar da cewa gwamnatin Lawal “ba ta tsaya kan magana kawai ba, tana aiki tare da sakamako a fili wanda jama’a ke iya gani da idonsu.”
“Wannan gwamnati ta tsayu kan gaskiya, amana, da samar da kyakkyawan sakamako ga al’umma. Ayyukan da ake gani su ne shaida,” inji Kwamishinan.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA