2025-11-05@11:22:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 104

«Guyawa»:

    Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jinjinawa rundunar Sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro bisa gaggawar daukar mataki kan hare-haren ‘yan bindiga da suka faru a wasu sassan jihar. Gwamnan ya yi wannan yabo ne a lokacin da Babban Hafsan Runduna ta 1, wato GOC 1 Division da ke Kaduna, Major Janar Abubakar...
    A Iran dubban ‘yan kasar ne suka taru a Tehran da kuma birane sama da 900 a fadin kasar don tunawa da karbe ofishin jakadancin Amurka a 1979, bikin da ake wa lakabi da ‘’Ranar Yaki da Girman Kai ta Duniya’’ A kasar. Dalibai, matasa, malamai, da iyalai ne suka halarci tarurrukan na yau Talata...
    Sanarwar ta ce, wannan horo mai taken ‘Computer Appreciation Training’ an shirya shi ne ta Hukumar Fasaha da Sadarwa ta Zamfara (ZITDA), a matsayin babban taron ƙarawa juna sani ga manyan jami’an gwamnati.   A jawabinsa yayin buɗe shirin, Gwamna Lawal ya bayyana cewa wannan horo wata muhimmiyar hanya ce wajen cimma burin gwamnatinsa na...
    A Ivory Coast sakamakon wucin gadi na zaben shugaban ya nuna cewa  Shugaba Alassane Ouattara, wanda ke jagorantar kasar tun 2011, na kan lashe zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Oktoba, 2025 da gagarumin rinjaye. Rahotanni sun ce Ouatara ya samu kashi 89.77% na ƙuri’un da aka kaɗa, bisa ga sakamakon wucin gadi da...
    Mahalifinsa, Chief Thomas Osen Ekpemupolo, da mahaifiyarsa, Mrs. Ewe Ekpemupolo, sun rayu cikin al’umma mai arziƙin mai a lokacin da ake tsaka da nema a yi wa yankinsu adalci. Daga cikin wannan rikicewar ya taso mutum wanda daga baya zai zama ɗan gwagwarmayar Niger Delta don neman daraja, adalci, da samun ikon gashin kai. Sojoji...
    Majalisar dokokin jihar Yobe, ta yi kira ga bangaren zartarwa na gwamnatin jihar da ta dauki matakan gaggawa domin magance yawaitar haduran ababen hawa a garuruwan Ngelzarma, Damagum da Dogon Kuka da ke kan hanyar Damaturu zuwa Potiskum. Majalisar ta yi wannan kiran ne bayan gabatar da kudiri da dan majalisa mai wakiltar mazabar Damagum,...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wasu ’yan sandan bogi guda biyar, da ke damfarar jama’a wajen karɓar kuɗi a Kano, Katsina da kuma Kaduna. Waɗanda ake zargin sun haɗa Aliyu Abbas mai shekaru 35, Sani Iliyasu mai shekaru 47, Ashiru Sule mai shekaru 41, Abubakar Yahaya mai shekaru 45 da kuma Adamu Kalilu...
    Majalisar Wakilai ta ƙaddamar da bincike kan ƙaruwar koke-koken ’yan Najeriya kan yawan cire musu kuɗaɗe ba tare da bayani ba daga asusun ajiyarsu da bankunan kasuwanci ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da wani ƙuduri da ɗan majalisa Hon. Tolani Shagaya (APC, Kwara) ya gabatar, inda ya nuna damuwa kan abin da...
    Tsohuwar mai bai wa Basshar Asad na Syria shawara, Busaina Sha’aban ta kore gaskiyar labarin da aka rika watsawa na cewa ta yi wata ganawar sirri da jami’an kasashen Iran, Iraki da Lebanon tare da Basshar Asad. Busaina Sha’aban ta kuma ce ba ta yi managa da tsohon shugaban kasar ta Syria Basshar Asad ba...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025 October 11, 2025 Daga Birnin Sin Tarihin Hassan Usman Katsina (1) October 11, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique October...
    Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati...
    A yau Alhamis, kamfanin sufurin jiragen kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, layin dogo na kasar Sin ya gudanar da balaguron fasinjoji miliyan 23.13 a jiya Laraba, wato ranar farko ta hutun bikin ranar kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin da kuma bikin tsakiyar kaka na tsawon kwanaki 8. A cewar kamfanin sufurin jiragen kasan,...
    Yau Litinin ofishin ‘yan jarida na kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai don bayyana nasarorin da Sin ta samu a fannin ban ruwa a lokacin “shirin raya kasa na 14 na shekaru biyar” . Minista mai kula da harkokin ban ruwa Li Guoying ya bayyana cewa, tun daga farkon shirin, Sin ta fara...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Amurka ta kawo cikas ga yarjejeniya tsakanin Iran da Turai game da batun yin watsi da dawo da takunkumi kan Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: An cimma yarjejeniya da kasashen turai dangane da yadda za’a yi watsi da batun sake dawo da takunkumi kan Iran,...
    Ko za ka fadawa masu karatu dan takaitaccen tarihinka? An haife ni a unguwar Tudun Nufawa dake Kano Municipal, na yi karatun firamare a jakara ‘Special Pramary School’, na yi sakandare a Gwammmaja 2. Sannan babban Sakandare a ‘GSS Dala’. Na yi karatun ‘Diploma’ a fannin ‘computer’, sannan na yi ‘National Diploma’ akan lafiyar hakori...
    A wajen ɗalibin Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Collins Whitworth, zane ba kawai sha’awa ba ce kaɗai, face hanya ta shiga kundin tarihin duniya. A ranar 1 ga watan Oktoba, 2025, Collins zai shiga sahun tarihin duniya yayin da zai yi ƙoƙarin kafa tarihi har guda biyu na shiga kundin ‘Guinness World Record’ a fannin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta ce jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da DSS sun kashe ’yan ta’addan ƙungiyar IPOB da yawa. Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya ce tawagar ta lalata sansanonin IPOB a yankin Ezioha da ke Ƙaramar Hukumar Mbaitoli, da kuma a Umuele, Ubuakpu, da Amakor a Ƙaramar...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya koka bisa yawan bashin da Najeriya ke ciyowa da kuma yadda gwamnati ke facaka da kuɗaɗen. Sarkin wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ne, ya kuma bayyana cewa cire tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi shi ne mafi alheri, yana  mai cewa da Gwamnatin...
    Wasu cibiyoyin bincike na Pew Research da CIA World Factbook sun tabbatar da cewa Najeriya ce ƙasa ta biyar mafi yawan Musulmai a duniya, inda ƙasar ke da Musulmai kimanin mutane miliyan 124. Ƙididdigar ta waɗannan cibiyoyi ta nuna Musulunci na ci gaba da zama addini na biyu mafi girma a duniya, wanda yawan mabiyansa...
    Alal hakika, akidar mulkin danniya akida ce wadda take tarnaki ga ci gaba da wayewa ta bil Adam, kuma yaduwar wannan akida barazana ce ga daukacin bil Adam. Don haka yaki da wannan akida ta bazu kamar wutar daji tsakanin sama da kasashe 80 daga nahiyoyin Asia, Turai, Afirka da Oceania. An kuwa tafka asarar...
    Shugaban majalisar shugabancin kasar Yemen Mahdi Almashat ya bayyana cewa, yahudawan sahyuniya su dakaci daukar fansa daga al’ummar Yemen kan shahahar kami’ansu da Isra’ila ta kaiwa hari. Ya ce tabbas Faraminista da sauran jami’ai ministoci da sua yi shahada sun yi sadaukarwa ne a kan tafarkin taimakon al’ummar Falastinu, kuma a kan wannan tafarki ne...
    Matsala ta farko na yi mata take da: 1. Sai Bango Ya Tsage….: Gaskiyar diyan Bawo, da yake cewa, ‘Sai bango Ya tsage, kadangare ke samun wurin shiga. Lallai babu yadda za a yi gwamnati da sauran manyan al’umma suna kallon harshen Hausa a matsayin wani harshe wanda nazartarsa koma baya ne ga al’umma kuma...
    Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha. Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi. Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari....
    Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen ɗan majalisar jiha da aka gudanar a mazaɓar Ghari/Tsanyawa. Jam’iyyar ta ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da wasu ’yan siyasa sun yi maguɗi. Jauro Jatau: Al’umma sun roƙi gwamnati ta samar musu da wutar lantarki APC ta lashe zaɓen cike...
    Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi nasara a zaɓen cike gurbi na Ghari/Tsanyawa da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Kano. Da yake sanar da sakamakon da misalin karfe 6:10 na safiyar Lahadin nan, babban jami’in da ya tattara sakamakon zaɓen, Farfesa Muhammad Waziri na Jami’ar Bayero, ya bayyana Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar...
    Da safiyar yau Jumma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton tattalin arzikin kasar na watan Yuli, inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare da inganta dunkulewar manyan kasuwanni cikin sassan kasar, ta yadda aka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin tsari, da kara...
      Tabbas fannonin zamanintar da kai na Sin na iya zama babbar taswira da kasashen Afirka ka iya bi, wajen kaiwa ga bunkasa yankuna, da kyautata zamantakewar al’ummunsu, da samar da isassun damammaki na gudanar da kyakkyawar rayuwa mai cike da walwala ga al’ummun nahiyar.(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Gwamnatin Tarayya ta yanke shawarar dakatar da ƙirƙirar sabbin manyan makarantu har na tsawon shekaru bakwai masu zuwa a duk faɗin Nijeriya. Dakatarwar ta shafi ƙirƙirar sabbin jami’o’i, kwalejojin ilimi da kuma kwalejojin kimiyya da fasaha na tarayya kamar yadda Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta tabbatar. Tinubu zai tafi ziyarar ƙasashe 3 An naɗa...
    Mai magana da yawun ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya bayyana a yau Talata 12 ga wata cewa, bisa dokoki ko ka’idojin da suka shafi saka wasu sassa cikin wadanda aka sanyawa takunkumin sayar musu da kayayyaki, ma’aikatar ta fitar da sanarwa mai lamba 21 da ta 22 a ranar 4 da kuma ranar 9...
    Kashi 3/4 na kasashe mambobi a majalisar dinkin duniya sun amince da samar da kasar Falasdinu, mai zaman kanta tare da kasar Australia a yau Litinin ta bada sanarwan cewa zata shelanta amincewarta da kasar Falasdinu a matsayin mai zaman kanta a taron babban zauren mdd wana za;a gudanar a cikin watan Satumba mai zuwa....
    “Shin an taɓa yin sulhu a na cin zarafin jama’a, an taɓa yin sulhu a na sa manoma noman dole, an taɓa yin sulhu a na karbar harajin dole, an taɓa yin sulhu ba a ajiye makamai ba?” Ya ce Turji da sauran ‘yan bindigansa irin su Kachalla Choma da Kachalla Haru ba za su...
    A dai dai lokacinda ake shirin juya yin 40 na shahadar Imam Hussain (a) jikan manzon All..(s) Iraniyawa fiye da miliyon 1.2 suka shiga kasar Iraki daga Iran don halattar wannan makokin. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana ncewa hotunan bidiyo na jami’ann tsaro sun bayyana cewa a lardin Ilam wacce ta...
    Ya ce malamin bai fi Sheikh Ahmad Gumi ba, wanda ya gaza yin zaman sulhu da Turji. Guyawa, wanda ya daɗe yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanai, ya ce ba a taɓa yin sulhu da mutum yayin da yake ci wa jama’a zarafi ba. Ya ce: “Za a iya cewa mutum ya yi sulhu...
    Bayanin da ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya yi a baya-bayan nan game da hasashe kan tattalin arzikin kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa ya jawo hankalin duniya sosai. Kuma sakamkon binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi a tsakanin masu...
    Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta samu nasarar kama mutane 15 da ake zargi da laifuka daban-daban, ciki har da wani kasurgumin  dan fashi da  makami mai suna Mu’azu Barga, a wani samame da aka lakaba wa suna “Operation Kukan Kura”.   Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana...
    Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ta kasar Sin ta fidda bayani a jiya Talata cewa, cikin rabin farkon shekarar bana, yawan zirga-zirgar jiragen sama ta fasinja ya kai ton-kilomita biliyan 78.35, adadin da ya karu da kaso 11.4 bisa dari, idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara. Kana, yawan zirga-zirgar...
    Wata sabuwar tashin-tashina ta sake kunno kai a yankin kahon Afirka a daidai lokacin da shugaban kasar Eritrea Isaias Afwerki ya yi gargadi kai tsaye ga firaministan Habasha Abiy Ahmed, inda ya yi kashedin sake kaddamar da wani yaki. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Habasha ke kokarin shiga bangaren ruwa...
    Rahotanni na cewa ’yan fashin daji masu yawan gaske ne aka tabbatar da kashewa a wani kwanton ɓauna da sojoji suka yi musu a ranar Laraba a jihohin Zamfara da Kebbi. Sojojin ƙasa da na sama sun yi amfanin da bayanan sirri wajen buɗe wuta kan ayarin ’yan fashin da ke kan ɗaruruwan babura suna...
    Manjo Janar Hatami: Nasarar da gwamnatin Musulunci ta samu kan makiya yahudawan sahayoniyya wata babbar nasara ce ga al’ummar Iran Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Dakarun tsaron sama na sojojin Iran sun cimma wani gagarumar nasara a yakin da suka yi da makiya yahudawan sahayoniyya. A wata ganawa...
    Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan  sahayoniyya kan kasar Iran Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mai yiwuwa masu sauraro sun san wani bawan Allah wanda kusan a kullum, kuksan a ko yaushe a cikin nema yake, amma Allah bai kawo ba.. Wasu dai na ganin yawan fadi-tashin da mutum yakan yi ba shi ne zai ba shi kudaden da yake bukata ba, yayin...
    Taken laccar ita ce, “Tsarin Tattalin Arziki Kan Kiwon Dabbobi A Nijeriya: Kalubale da Nasarori.” Jega a cikin takardarsa, ya bayyana cewa; “Hasashen da aka yi, ya nuna cewa; nan da shekara ta 2050, al’ummar Nijeriya za ta karu da kusan mutum miliyan 400, wanda hakan zai sanya ta zama kasa ta uku mafi yawan...
    Bayan Plato sai kuma masani Aristotle shi ma ya zo da ta shi fahimtar, a shekara 340 kafin zuwan Annabi Isah (AS). A tunani irin Aristotle, yawaitar al’umma ba ta da wani alfanu, don haka hakki ne da ya rataya kan gwamnati ta kayyade yawan iyalin da mutum zai iya haifa. Idan matar mutum ta...
    Misali, a lokutan hare-haren, an kone gidaje da dama, inda wasu ahali ma, wanda yawansu ya kai, har zuwa 15, aka shafe su, daga doron kasa, a lokacin da suke kan bacci, a gidansu. Wasu daga cikin wadanda suka tsallake Rijiya da baya daga hare-haren na ‘yan ta’addar, sun bayyna yadda ‘yan ta’addar, suka cinnawa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar amosanin jini wacce aka fi sani da cutar sikila na cigaba da barazana ga rayukan masu dauke da ita. Wannan cuta na saka masu ita da ‘yan uwan su cikin halin ha’ula’i, a wasu lokutan ma tana haifar da rasa rayukan wasu dake dauke da ita. Rahotannin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi  Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar...
    Rundunar ’Yan Sanda ta jihar Kano ta ce ta gurfanar da mutum 29 da ta kama bisa zarginsu da hannu a kashe DPO na garin Rano da ke jihar, CSP Baba Ali da sauran laifuffuka. Kakakin rundunar a jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, inda ya...
    Hakika abin da suke yi shi ne kokarin cika alkawarin da gwamnatin kasar Sin ta sanya, na taimakon yankunan karkara na kasashen Afirka wajen samun hakikanin ci gaba, inda za a kyautata muhallin rayuwar mutane, da fitar da su daga kangin talauci, maimakon samar da karuwar adadin tattalin arziki kawai. Kana a bayan manufar ta...
    Yau Talata, kungiyar masu jigilar kayayyaki da sayayya ta kasar Sin ta gabatar da alkaluman watanni 4 na farko na bana, wadanda suka nuna cewa, a watan Afrilu, sha’anin jigilar kayayyaki ya bayyana inganci da boyayyen karfi, kuma duk da kalubaloli da matsin lamba daga ketare da aka fuskanta, ya tafi yadda ya kamata tare...
    Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na MDD ta bukaci kasashen duniya su takurawa HKI ta kawo karshen kissan kiyashin da take yi a gaza bayan hare-haren da ta kai a kan wata makaranta a unguwar Fahmi Aljarjawi a cikin birnin Gaza wanda ya kashe falasdinawa akalla 36. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta...