An Yi Allah Wadai Da Hana Amfani Da Hijabi A Jami’ar LandMark, Omu-Aran Kwara
Published: 11th, August 2025 GMT
Kungiyar Muslim Media Watch Group ta Najeriya ta yi Allah-wadai da wata sanarwa da ake zargin Bishop David Oyedepo kan amfani da hijabi da daliban Musulman Jami’ar Landmark ta Omu-Aran ta Jihar Kwara suka yi.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun wakilinta na kasa Sheikh Abu Sheriff, kungiyar ta yi Allah wadai da Bishop David Oyedepo da take hakkin dalibai musulmi da ma’aikatan cibiyar da ke da hakkin dan Adam kamar yadda sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar.
A cewarsa a cikin wani faifan bidiyo da aka yada sosai, Oyedepo ya yi kira ga iyaye da masu kula da Musulmai da su janye ‘ya’yansu mata idan suka dage ba za ayi amfani da hijabi ba.
Kungiyar ta bayyana dokar hana amfani da hijabi a jami’ar Landmark Omu-Aran a matsayin ‘wani abin da ba za a lamunta dashi ba’ kuma tauye hakkin addini ne.
Ya yi nuni da cewa ba a daukar musulmi aiki a wannan jami’a, kuma idan aka dauki shi bisa kuskure, to ba za su barshi yin salloli sau 5 ko azumin watan Ramadan ba.
Kungiyar ta ci gaba da cewa haramta wa dalibai musulmi ‘yancin yin amfani da hijabi cin zarafi ne ga ‘yancin yin imani da ibadarsu.
Sanarwar ta bayyana cewa neman iyaye da su janye ‘ya’yansu saboda amfani da Hijabi yana tauye musu hakkinsu na dan Adam.
Kungiyar ta kuma yi kira ga ma’aikatar ilimi ta tarayya, NUC, NBTE da sauran su da su binciki duk masu take hakkin dan adam a cibiyoyin ilimi a fadin kasar nan.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kungiyar ta
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe mutum 24 an sace 144 a mako guda a Zamfara — Rahoto
’Yan ta’adda sun kashe mutum 24 tare da sace wasu akalla 144 a cikin mako guda a sassan Jihar Zamfara.
Kungiyar Al’ummar Zamfara mai suna Zamfara Zamfara Circle Community Initiative ta bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai hare-haren da suka kai kan kauyuka 15 inda suka jikkata mutane 16 a kananan hukumomi daban-daban.
Ta bayyana cewa daga ranar 4 zuwa 10 ga watan nan na Agusta, 2025 ’yan ta’adda suka kai hare haren; kauyukan da aka kai wa farmakin sun hada da Sabe, Tungar Yamma, Sauru, Lambasu, Dogon Madacci, Dankalgo, da Kwanar Kalgo a ƙaramar hukumar Bakura.
A Karamar Hukumar Tsafe, hare-haren sun shafi Chediya, Kucheri, Yankuzo, da Katangar Gabas Bilbils.
A Karamar hukumar Mafara, an samu rahoton hare-hare a Tabkin Rama, Matsafa, da Ruwan Gizo, yayin da Rafin Jema a Gummi da ƙauyukan Adabka da Masu a Bukkuyum suma suka fuskanci hari.
Kungiyar ta jaddada cewa ci gaba da kai hare-hare yana nuna bukatar gaggawa ta ƙarfafa matakan tsaro domin kare al’ummomin karkara daga hannun ‘yan bindiga da ke addabar jihar.