Leadership News Hausa:
2025-09-24@11:25:35 GMT

Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu

Published: 9th, August 2025 GMT

Tsohon Shugaban PDP Audu Ogbeh Ya Rasu

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta, yana da shekaru 78 a duniya, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar.

A cikin wata sanarwa, iyalan sun ce: “Ya rasu cikin kwanciyar hankali, ya bar mana gado na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasa da al’umma.

Mun sami kwanciyar hankali daga yadda ya shafi rayuka da kuma yadda ya kafa misali.”

Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa

Iyalan sun bayyana cewa za a sanar da yadda za a gudanar da jana’izarsa a nan gaba, tare da godewa abokai, da abokan aiki. Sun kuma roƙi a basu dama domin yin jimamin rasuwar baban nasu.

Rahoton LEADERSHIP ya nuna cewa Ogbeh, wanda ya shahara a siyasa, rubuce-rubuce da aikin gona, ya shugabanci PDP daga 2001 zuwa 2005 kafin ya zama minista a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025

An ba shi kyautar ne a daren ranar Litinin a Theatre du Chatelet da ke birnin Paris, inda ya doke matashin Barcelona, Lamine Yamal, wanda ya lashe kyautar matashin ɗan wasa mafi ƙwazo.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Kama Tsohon Ɗan Wasan Super Eagles, Victor Ezeji, Kan Zargin Aikata Zambar ₦39.8m
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutum 4,383, Sun Ceto 1,138 Daga Hannun Mahara Cikin Wata 3
  • DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata
  • Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
  • Yadda Aka Bai Wa Ousmane Dembélé Kyautar Ballon d’Or Ta 2025
  • Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau
  • Lokaci Yayi Da Shugabannin Arewa Za Su Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Yankin –  ACI
  • Yadda Wasu Mata Ke Gwada Mazansu Ta Hanyar Magana Da Su Ta Wasu Hanyoyi Don Sanin Ku Suna Kula Mata
  • Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 4, 16 sun jikkata a Yobe
  • Yadda Ƴan Agbero’ Ke Cin Karensu Ba Babbaka A Abuja