Aminiya:
2025-11-08@16:57:18 GMT

Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja

Published: 9th, August 2025 GMT

Shugaban Hukumar Yaki da Cin Masu Karya Tattalin Arziki ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa yawancin gidajen da aka yi watsi da su a Babban birnin Tarayya, Abuja, an gina su ne da kuɗin da ma’aikatan gwamnati suka sace.

Olukoyede ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba a wani taron tattaunawa da zauren lauyoyi na Law Corridor ta shirya, mai taken “Muhimman Matsaloli da ke Addabar Harkar Gidaje a Najeriya.

Ya shaida wa mahalarta taron cewa EFCC ta kafa wata tawaga ta musamman da za ta fara binciken irin waɗannan gine-gine.

“Za mu fara bibiyar dukkan gidajen, ba a Abuja kaɗai ba, har da sauran sassan Najeriya. Muna son sanin wa ke da su,” in ji Olukoyede.

Shugaban na EFCC bayyana cewa wasu daga cikin gidajen sun shafe fiye da shekaru goma, ba tare da an kammala su ba.

Ya ce, “Za ka yi mamaki ka ji cewa wasu daga cikin waɗannan gidaje sun shafe shekaru 10 zuwa 20 a ba a kula su. Ana fara gina su, sai a bar su haka. Babu wanda ya san dalili.”

Ya ce binciken EFCC ya nuna cewa yawancin gidajen an gina su ne da kuɗin da ma’aikatan gwamnati suka sace. Bayan sun bar aiki kuma ƙofar satar kuɗaɗen ta toshe, sai su bar aikin ginin. Daga nan sai masu gina su su fara neman masu zuba jari don kammala aikin.

Olukoyede ya ce hukumar ta fara neman ƙwace gidaje kusan 15 a baya-bayan nan, kuma tana samun ƙarin bayanai.

A jawabinsa ga mahalarta taron, shugaban na EFCC ya ce,  “Wasu daga cikin ku da ke zaune a wannan dakin, wataƙila wasu daga cikin waɗannan gidaje naku ne.

“Amma nan ba da daɗewa ba, za mu haɗu da ku a kotu, domin ba za mu iya bunkasa wannan fanni ba idan aka ci gaba da irin wannan hali. Na san wasu daga cikinku kuna da halatattum hanyoyin samun kuɗi.”

Olukoyede ya gargaɗi lauyoyi da masu gine-gine da kada su ’yan barandan masu aikata laifin wanke kuɗi.

A nasa bangaren, Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA), Afam Osigwe, ya buƙaci a samar da tsarin tantance mallakar kadarori a ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma yi gargaɗin cewa soke  mallakar ƙasa ba tare da cikakken bayani ba — musamman saboda rashin biyan harajin ƙasa — na iya hana masu zuba jari daga ƙasashen waje shigowa.

“Dole ne mu tabbatar da gaskiya da daidaito a harkar mallakar fili idan muna son jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje,” in ji Osigwe.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kuɗaɗen sata wasu daga cikin

এছাড়াও পড়ুন:

Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata

Ya yi Allah-wadai da wannan lamari, tare da roƙon Allah Ya tona asirin waɗanda suka aikata laifin kuma Ya kare ƙaramar hukumar Gaya daga irin wannan lamarin.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisa Ta Ɗage Tantance Ministan Tinubu Saboda Rashin Rahoton Tsaro November 6, 2025 Labarai Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140 November 5, 2025 Labarai Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i November 5, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal
  • An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa
  • Ma’aikatan NPA Wasu Ginshikai Ne Na Ciyar Da NPA Gaba —Dantsoho
  • Kamfanin wutar lantarki na Abuja ya salami ma’aikata 800
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT
  • Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan
  • Ɓarayi Sun Shiga Ofishin Shugaban Karama Hukuma A Kano, Sun Tafka Sata
  • Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa
  • Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140